← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 100

Sashe 53

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jijjiga kai tace

‘Hmmm! Don ma baki zauna da ita ba, ai micijin sari ka noke ce lamba daya.’

Kafin ta bata amsa Abban ya dawo don haka sukayi shiru.

Jimawa kadan Abban yace Malam Ali ya mayar da su gida, ya bashi kajin yace ya kai gida ya bawa Jummai. Sukayi musu sallama suna sake jajantawa suka fice.
_

Satin Sadik biyu a asibitin lafiya ta fara samuwa domin har likita ya sa masa ranar sallama. Yana iya rataye hannunsa ya yita yawo a cikin asibitin sannan kuma yawancin ciwukan jikinsa duk sun warke, sai karayar wadda dama zata dauki lokaci.

A zaune suke ita da Amina a farfajiyar asibitin, inda suke babu nisa da dakin Saddikun don suna hango kofar dakin.

Zahra ta dubi Amina tace

‘Ina jin ma zuwa gobe zasu sallameshi don kin ga yana yawonsa ko ina.’
‘Ma sha Allah ai haka ake so, zakaran da Allah ya nufa da cara kenan.’

‘In Sha Allah.’

Sukayi shiru na dan lokaci jimawa kadan Zahra tace

‘Ina jin gobe zan fito miki da takardun filin nan tunda kin ce akwai mai saye a hannu. Mun gama magana da Yaron Malam yace an daure min bakinsa duk abinda zan yi na yi ba zai iya magana ba don haka a siyar kawai ki turo min kudin account dina.’

‘Ko ke fa kawata, ai gara da kika motsa.’

‘Na gaji ne kawata da cin kashin da mutumin nan yake min, don a kan accident din nan ina jin da ya sami dama zai iya kai min duka.’

‘Ai kece kike abu da tsoro uwar Sadiku, da kin biye min da tuni an sa miki shi a kwalba wallahi idan kika ce ya zauna ko uwar da ta haifeshi bata isa tace ya tashi ba sai in ke kika so.’

Ta jijjiga kai tace

‘Hmmm! Ai kuma yanzu dole ayi hakan kawata tunda yana so ya nuna min taurin kai. Wannan wulakanci da yake min ba zan dauka ba don na ga kamar ya manta lokacin da muke hannu baka hannu kwarya na hakura da komai na zauna da shi yanzu ya sami kudi ya auro matar so zai yi min tijara. Wajen wancan Malamin naki zamu fara zuwa daga baya sai muje wajen yaron Malam, na san kudin filin nan zai isheni.’

‘Zai isa sosai ma, magana ake fa ta wajen miliyan uku da rabi zuwa hudu kinga kuwa ko Aisha kike son siya ai kin saya kin gama.’
Sukayi dariya suka tafa.
Suka karasa hirarrakinsu, daga baya Amina tayi mata sallama ta tafi.

……….

An sallami Saddiku ya dawo gida inda zai karasa jinya, dakinshi na cikin gida aka gyara masa ba don yana so baya koma. Tun daga asibitin Rahama tayi musu sallama ta wuce gida akan idan ta huta gobe zata samesu a gidan.

Ranar da aka sallameshi washegari Amina ta gama cefanar da filin da Mommy ta bata takardunsa. Ko da aka gama ciniki akwai takarda da ake bukatar saka hannun mai fili don haka ta kawowa Mommy takardar har gida. Sadikun ta sa a gaba ya sa hannu a takardar ba tare da ta bari ya karanta ba balle ya gane ta mecece, burinta tunda dai sunansa ne a kan takardar filin kuma ya balaga ko daga baya idan zancen ya tashi to shi ya sayar da filinsa.

Naira miliyan hudu da dubu dari biyu aka sayi filin; a hakan ma ance don karami ne. Amma duk da haka naira miliyan uku da rabi Amina ta kawowa Zahran ta haye kan sauran, bayan ta gama godiya kuma ta tura mata dubu dari da hamsin tace ga tukuici da alkawarin idan an gama aikin ma zata kara mata idan an yi canji. Ta kirga kudinta dubu dari takwas da hamsin ta tafi tana murnar wannan kazamar ribar da ta samu.

Sai daga baya da Sadikun ya kara samun lafiya sannan Amina ta yiwa Zahra bayani shi malamin nata a can wani kauye yake a karamar hukumar Doguwa, Doguwan ma a cikin daji. Don haka ita Amina tana da amintaccen yaronta wanda shi yake kaita saboda nisa kuma ga hadari, nan suka saka rana a kan nan da sati mai zuwa idan an yiwa motar Amina service zasu je in ya so idan suka dawo suka huta sai suje wajen yaron Malam.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

29

Lokacin da aka kwantar da Saddiku a asibiti a dai-dai lokacin ne ake jarrabawar SSCE; wadda har an gama yiwa Saddiku rijista don ya gyara tashi wadda ya fadi English. Sai ranar da ya kwanta a asibiti ranar aka fara jarrabawar, don haka gaba daya Saddiku bai sami zana jarrabawa ko daya ba.

Tun a lokacin Mommy ta sami Abban a kan yayi magana da malaman makarantarsu Sadiku din za a samu mai yi masa amma yace sam bai yadda wani yayiwa Saddiku jarrabawar ba. Gaba daya ma kin saurarta yayi, domin daga baya ma da yaga tana neman ta zagaya ta bayan gida ayi masa jarrabawar ce mata yayi in dai shine zai biyawa Saddiku kudin jamia to ya san baiyi wata jarrabawa a wannan shekarar ba kuma ba zai karbi wani certificate mai dauke da kwanan watan wannan shekarar don nema masa admission ba.

Duk wanda take jin zasu goya mata baya idan tayi magana sai suce ta bari Sadikun ya sami lafiya tukunna. Don haka dole suna ji suna gani aka gama jarrabawa babu Saddiku. Ya tabbata sai ya sake bata shekara guda a gida, daidai lokacin ‘yan ajinsu sun gama level 1 sannan zai sami damar gyara jarrabawarsa lokacin zai kama tare da Yusra kenan wadda a halin yanzu za ta shiga SS 3.
__

Tun bayan da ya biyawa Zahra Umra kamar yanda ta zaba yake tanadin biyawa kansa Hajjin bana; sai dai a yanda ya shirya tare da Aisha yake so su tafi.

Saura abinda bai fi shekaru goma yayi retire ba don haka yana da niyyar idan sun gama aikin Hajji sai ya sako Aisha a jirgi ta dawo gida shi kuma ya wuce Dubai; yana so ya fara shigo da kayan electronics yana sayarwa a Nigeria zuwa lokacin da zaiyi retire ya zama babban dealer. Da fari yana jiran sai ya bude shago amma abokinsa wanda yake masa jagoranci a harkar yace ya shigo dasu haka sai a kama hayar waje a ajiye ana siyarwa a kan sari, yayi na’am da shawarar don haka ya gama lissafin zarcewa Dubai daga Saudiyya.

Ita kanta Aishan bata san zai biya mata aikin Hajji ba don bai gaya mata ba, ya bari sai ya gama komai ya gaya mata; duk da dai yana sane da cewa ta taba yin aikin Hajji.
__

Satin da aka gama service din motar Amina sun gama tsara tafiya Doguwa sai kuma Amina ta kwanta zazzabi. Abu kamar wasa sai da ya kai ta kwanciya a asibiti kwana biyu; aka tabbatar da cewa zazzabi ne na malariya ya kamata da yawa. Wannan ya sa dole suka dakata da tafiyar.

Bayan an sallameta daga asibiti kuma akwai ‘yarta ta fari Asiya wadda take aure a Abuja, shekara kenan da yin aurenta sai a lokacin tazo ganin gida hadi da dubiya ga tsohon ciki; don haka dole suka kara daga tafiyar har Aminan ta kara samun lafiya kuma ta sami mai zama da Asiya. Tunda wannan tafiyar idan sun tafi da sassafe to da isa gari da samun ganin bokan zuwa dawowarsu gida wuni guda ne, don wata ran sai anyi isha’i take dawowa gidan.
__

A zaune yake a kan gado ya mike kafa ya dora computer a kan cinyarsa yana aiki yayinda ita kuma take kwance a rub da ciki a gefenshi. Kanta yana daidai wajen kafafunsa tana karanta littafi a waya kuma a lokaci guda tana wasa da yatsun kafarsa.

Ba tare da ya daina kallon computer ba ya kirawo sunanta

‘Aeesh.’

Itama bata dauke idonta daga kan wayar ba ta amsa

‘Yes My love.’

‘Na biya mana aikin Hajji fa, ni da ke zamu tafi nan da kwana goma. Gobe da safe ki shirya mu fita don takardunki ba a gama hada su ba da passport dinki kuma a goben nake son mu gama tunda kinga lokaci ya dan kure.’

Da hanzari ta mike ta dawo dai-dai fuskarsa, suna hada ido ta kyalkyale da dariyar da ta sashi dariya. Tace

‘Allah Habibi? Kai amma nagode. Allah ya kara arziki.’

‘Amin.’

Mamakin murnar da takeyi yake, musamman da yake ya san ta taba zuwa aikin Hajji bai zata abun zai rudata haka ba. Yanda kuma yaga tana murnar sai shima ya kara jin dadi, ya dinga binta da kallo yana murmushi.
Ta lalubi wayarta a inda ta yar da ita tana fadin

‘Bari na gayawa Hajiya.’

Har ta dauko wayar sai kuma ta sake jefar da wayar, ta dauke computer daga kan cinyarsa ta ajiye a gefe sannan ta rungumeshi. Suka dan dauki lokaci a haka sannan ta sakeshi ta kalli fuskarshi tace

‘Nagode sosai Yallabai, ba zaka gane yanda na ji dadi ba. Zan je na yiwa Abbana dawafi nayi masa addu’a.’

Ta sake kallonshi suka hada ido tace

‘Mijina ma zan yi masa addu’a Allah ya sa kada yayi min kishiya.’

Ya kyalkyale da dariya yace

‘Uhm! Wato gwano baya jin warin jikinsa.’

Ta wurkila ido tace
‘Dama shi gwano baya wari mutane ne da jiye-jiye.’

Ta dauki wayar ta mike tsaye ta barshi yana dariya.

Shima ya mika hannu ya dauki kwamfutarsa wadda ta ajiye masa a gefe ya cigaba da aikinsa.

Gaban mudubi ta koma ta tsaya, sai dai madadin ta kirawo Hajiya kamar yanda ta fada sai kawai ta kirawo Zahida. Tana dauka tace

‘Hida guess what?’

‘Ki fada min kawai sarkin jan rai.’

‘An biya min Hajjin bana da ni za a je.’

‘Aaaah!’

Suka fasa ihu a lokaci guda sannan suka kyalkyale da dariya.

Suka karasa magana suna ta murna.

Tana ajiye wayar yace

‘Wai ke da Zahida ba zaku daina yiwa mutane ihu ba?’

Ta sa hannu ta rufe bakinta tana dariya

‘Mantawa mukayi fa.’

Ta dawo gefen gadon ta zauna ta cigaba da waya tana gayawa ‘yanuwanta abun alkhairi.
Chapter 53 · 0% Book details