← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 100

Sashe 2

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka bata zabi ko zata tafi da su Abdallah ko kuma a barsu wajen Yaya Sani, tace zata tafi da su.

Baffa ya sake yi musu nasiha suka yiwa Mustafa addu’a suka yi mata sallama suka tafi suka barsu ita da Hajiya da Zahida kanwarta da kuma da kuma Anti Uwani.

A ranar suka fara hada mata kayanta ita da yaran, gari yana wayewa suka tattara suka koma gidan Hajiya gaba daya.
Gidajen guda biyu da suka fado kasonta ita da yara ta sa Yayanta Abubakar ya sa mata ‘yan haya, ta ware kudi kuma ta bayar a samu wani waje da suke wahalar ruwa a Bichi a yi musu borehole Allah ya kaiwa Mustafa ladan. Musamman Baffa ya kirawota yayi mata godiya yayi ta saka mata albarka da Abba ya kai masa wannan labarin, haka itama Umma har gidansu ta zo tayi mata godiya kuma ta duba su Abdallah.

Haka suka cigaba da rayuwa a gidan Hajiya; kullum da safe Baba Abba zai zo ya daukesu ya kaisu makaranta idan an tashi kuma ya dawo da su.
……….

Yau satinsu biyu da komowa gidan Hajiya, bayan yara sun tafi makaranta Hajiya ta sami Aisha a dakinta wanda aka gyara mata bayan sun dawo. A kwance take a gefen gado bayan ta amsa sallamar Hajiya ta tashi ta zauna, Hajiya ta karasa ta zauna a gefen gado ta dubeta cike da kulawa tace

‘Aisha.’

Ta dago suka hada ido sannan ta sunkuyar da kai.

‘Yaushe zaki koma aiki? Kinga dai sati biyu kenan da fitarki daga takaba, ai ya kamata ki koma ko?’

Ta kawar da kai cike da damuwa

‘Hm! Wallahi Hajiya nima ban sani ba, aikin ma duk ya fice min daga rai wallahi.’

Ta share kwalla.

Hajiya ta gyara zama ta kama hannun Aishan tana kallon fuskarta

‘Zaki koma aiki gobe in sha Allah Aisha.’

Ta kalli Hajiya da mamakin jin maganarta ta zare hannunta daga na Hajiyan ta share kwalla, kafin tayi magana Hajiya ta cigaba

‘Tabbas mutuwar miji tana da ciwo tunda kafin naki mijin ya mutu nawa ya jima da mutuwa ya barni daku gamu Allah ya raya mu. Ki godewa Allah Aisha, domin dama Allah bai yi wa kowa alkawarin dauwama ba, mu din ma da muke raye lokaci muke jira. Ki cire komai daga ranki ki cigaba da rayuwarki; ko babu komai yaranki suna bukatar ki kuma walwalarki ce zata basu kwarin gwiwar cigaba da tasu rayuwar. Ki hakurkurtar da zuciyarki ki cigaba da rayuwarki Allah zai kawo miki mafita in sha Allah, ki cigaba da yiwa Mustafa addu’a Allah ya hadaku a Aljanna.’

Ta share hawaye tayi ajiyar zuciya, ta dubi Hajiya tace

‘Na kasa daina damuwa Hajiya, ki dinga yi min addu’a.’

‘Ina nan ina yi, kema kuma sai ki dage ki bawa kanki hakuri.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aisha tace
‘In sha Allah gobe zan koma aikin Hajiya, shima yana son nayi aikin shi yasa ya samo min.’

Hajiya tayi murmushi ta dan kara bata hakuri sannan ta fita daga dakin ta barta tana tuno lokacin da ya samo mata aikin lokacin saura baifi wata hudu ba ya rasu ma ashe:

A kwance ya sameta a falo tana kallo, yaran duk sunyi bacci don har taran dare ta gota. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya wuce daki ita kuma ta tashi ta jera masa abincin darensa a dining table. Ta bishi dakin suka fito tare, har ya zauna ya mike ya koma dakin ya dauko takardar ya fito ya sameta a zaune ya mika mata takardar sannan ya zauna ya fara cin abincin da ta zuba masa.

Karanta takardar takeyi tana murmushi, ta riga ta gaya masa bata son aiki amma shi ya dage tunda ta karanci education to ya kamata a samar mata koyarwa; ko babu komai ta sami abinda zata kula da kanta da shi. Ya kalleta bayan ya cinye lomar bakinsa yace

‘Sai ki bani tukwici Malama Aishatu ga offer nan kin zama malamar gwamnati.’

Ta kalleshi tana dariya tace

‘Gashi nan na baka tuwo harda nama. Allah dai ya bani ikon yin aikin nan don ka san ni da son jiki.’

‘Dagewa zakiyi fa, ki rike aikin nan kinga ko bayan raina kina da abinda zaki kula da kanki da yara kuma ko ina rayen ma bamu san abinda gaba zata haifar ba don haka aikin nan security ne a gare mu. Ki dage kawai Malama Shatun Musty.’

Wannan maganar tasa kwakwalwarta ta dinga maimaita mata tana share hawaye; gaban da yake nufi kenan ashe. Ai dole ma ta koma aikin nan, kuma in sha Allah goben zata koma.
UWAR SADIKU

WRITTEN BY
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

2
A hankali rayuwar Aisha ta fara dawowa dai-dai, sai dai kawai tana nan da tabon rashin Mustafa a zuciyarta. Ga yaranta suna walwalarsu amma duk lokacin da ta kallesu sai tayi kewar ubansu, musamman Abdallah da yake matukar kama da shi.

Gashi yanzu har an shekara da rasuwar Mustafa; duk abinda uba zai yiwa da ‘yan uwan Mustafa basu taba fasawa ba, kuma suna yawan zuwa duba su ko kuma su zo su kwashesu su yi musu kwana biyu.

Tuni an canza musu makaranta sun dawo kusa da gidan Hajiya amma Umma ta saka dole kullum sai Abba ya zo ya kaisu, in ya so sai Aisha ta dauko su.
………..

Suna zaune a falon Hajiya ita da su Abdallah da kuma Afnan ‘yar wajen Zuwaira sunata wasa, Afnan ce take bawa su Abdallah labari

‘Ni kullum Abbana ya dawo sai ya siyo min ayaba wataran ma harda apple.’

Farha tace

‘To muma dai kullum sai Mommy ta siyo mana duk abinda muke so, kuma Baba Abba yace mu Abbanmu ya tafi can yana Aljannah don ya gina mana gida kafin muje.’

Tace

‘Iyye, ‘yan gidan Aljannah.’

Abdallah ne ya tashi ya koma kusa da Aisha ya ya zauna a jikinta yace

‘Mama.'

Ta kalleshi cike da kulawa

‘Abdallan Mama.’

‘Da ma Abba ya jiramu ko? Ai da sai mu tafi aljannar tare, amma shi yayi wani sauri ya tafi.’

Tayi murmushi ta danne kwallar da ta taru a idonta

‘Watarana muma zamu je in sha Allah.’

Ya kwanta a jikinta yayi shiru, itama tayi shiru tana shafa kansa tana kuma kallon Farha wadda take wasa da Afnan.

Yaro ne ya shigo falon da sallamarsa, bayan ya gaida Aisha yace

‘Wani mutum ne yace na kirawoki Mama.’

Da mamaki ta kalleshi tace

‘Ni kaina Sule?’

‘E haka yace min.’

Ta bude baki zata sallameshi Hajiya ta fito daga daki inda take jiyosu tace

‘Tafi kace tana zuwa Sule.’

Nan da nan ya juya kamar wanda daman ya gaji da tsayuwar.

Hajiya ta karaso ta zauna a kan kujera kusa da Aisha, kafin ta zauna Aisha tace

‘Hajiya nifa ban ce kowa yazo ba kawai ki barshi yayi tafiyarsa.’

‘Ba zai yi tafiyar tasa ba, tashi zakiyi kije. Babu wanda zai yi miki auren dole ai sai an jira yardarki, idan kin saurari mutum ba shine yake nufin zaki aureshi ba. Ki godewa Allah a hakan ma, kuma ki tashi kije ki ga mai kiran naki.’

Kallon da Hajiyan takeyi mata ya tabbatar mata ba zata saurareta ba don haka ta mike ta shiga dakin ta sako hijabi ta zo ta wuce.

Hajiya ta bi bayanta da kallo tana jijjiga kai cike da tausayi; ta san dai Aisha so take tace ba zata sake aure ba, ita kuwa bata yi mata wannan fatan. Har yanzu da kuruciyarta domin shekarunta ashirin da biyar kachal, ba zai yiwu ba kuwa ace a barta babu aure. Addu’ar Hajiya daya Allah ya bata miji nagari wanda ma zai so ta fiye da yanda Mustafa yake sonta.
……..

Motar da ta gani a bakin gate din gidansu ta sakata mamaki.

‘Principal?’

Ta tambayi kanta.

Ta dan saita fuskarta daga murtukewar da tayi, ta nufi motar tana tafiya a hankali tana tunani kala-kala; Allah ya sa dai ba wata matsala aka samu a wajen aikin ba da principal zai taso da kansa har gidansu.
Tana tsayawa a kusa da motar ya bude kofar motar ya fito yana ta faman murmushi kamar wanda yaga wata sabuwar amarya, dariya murmushin nasa ya bata amma sai ta waske da murmushi tana fadin

‘Yallabai sannu da zuwa. Kai da kanka? Ai da kirawo nima kayi yallabai da ba sai ka taso ba.’

Ya kara fadada murmushinsa

‘Haba Malama Aisha, ai zancen mai mahimmancine shi yasa gara na taso dai na zo.’

Suka gaisa tana ta mamakin wannan zance da ya kawo shi. Suka yi shiru tana sauraronsa, yayi dan gyaran murya yace

‘Um ai gara mu sami wajen zama ko? Ko nan cikin motar ma sai mu zauna kya fi fahimtar abinda na zo da shi.’

‘Uhm, hakane. Shigo daga ciki sai mu zauna a nan.’

Ta wuce gaba ya bita a baya suka shiga cikin gida; suna shigowa akwai gareji wajen ajiye mota daya wanda motar mahaifinsu ake ajiyewa a da amma tunda ya rasu sai wajen ya zama babu motar. Ta zaro kujerun roba guda biyu daga cikin kujerun da suke ajiye a garejin ta gyara musu zama ta nuna masa daya tace
‘Bismillah.’

Ya zauna itama ta zauna a dayar. Suka sake yin shiru na dan lokaci, principal yayi gyaran murya

‘Uhmm! Wato Malama Aisha na san dai kin yi mamakin ganina to amma kamar yanda na gaya miki maganar mai mahimmanci ce sosai.’

Ya dan numfasa sannan ya cigaba da yaji bata ce komai ba.

‘Wato ina so ne ki bani dama na shiga cikin manemanki, tunda shi aure nufi ne na Allah. Kuma na san dai duk wani bayani da zaki so ki ji a kaina kin riga kin san shi, sai dai ina fatan ki yiwa zancen nawa kyakkyawar fahimta.’

Tuni murmushin fuskarta ya gushe, sai dai bata daure fuskar sosai ba. Ta kalleshi suka hada ido ta kawar da nata idon yayinda shi kuma yake ta kara fadada murmushin da yake fuskarsa. Ta gyara zama kadan tayi gyaran murya

‘Hmmm! Uhhm! Ban ki zancenka ba, amma dai ina bukatar karin lokaci don a yanzu bana ma jin sha’awar sake wani auren. Don haka ina ga mu bar wannan maganar kawai yallabai.’
Chapter 2 · 0% Book details