← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 100

Sashe 90

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

'Bari naje nayi sallah, ko magriba ban yi ba ga shi nan har an fara kiran isha'i.’

Ba tare da ta saurari abinda zasu fada ba ta bar wajen da sauri ta shige dakin da yaran suka shiga da kayanta.

Hajiya ta dubi Anti Uwani tace

'Kin ga yarinya don Allah, guduwa fa ta yi. Tabbas wannan zuwan nata akwai dalili.’

Anti Uwani tace

'Barni da ita, bari ta idar da sallar na ji abinda ya kawota.’

Har aka ci abinci akayi sallar isha'i tana daki, babu wanda ya nemeta. Sai dai Anti Uwani ta zuba abinci ta bawa Farha ta kai mata daki. Da yake tana tattare da yunwa ta dan taba tuwo, ta mayar ta rufe kwanukan ta wanke hannunta a bandakin da yake cikin dakin sannan ta dawo ta kashingide a gafen gadon Anti Uwani.

Bata dade da zama ba Anti Uwani ta turo kofa ta shigo dakin, bayan Aishan ta amsa sallamarta ta wuce ta zauna a gefen gadon yayinda Aishan ta gyara zama ta janye kafafunta. Bayan Anti Uwanin ta zauna ta dubi Aishan, suna hada ido ta sunkuyar da kanta yayinda Anti Uwani tayi murmushi. Tace

‘Kya ji kunya mana Shatu! To ya aka yi? Don dai wannan zuwan na san ba na lafiya bane.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tana sauraronta ita kuma tana kallon hannunta tana tunanin ta inda zata fara. Jimawa kadan ta gaji da yanda Anti Uwanin ke kallo da sauraronta ta bude baki da kyar tace

'Cewa yayi idan na zauna a gidan zaman kaina nakeyi, shine na taho.’

Mamakin Anti Uwani ya karu, ta gyara zama tace

'Ban fahimceki ba fa, Yusufan ne yace zaman kan ki kikeyi ko kuwa? Kiyi min bayani yanda zan gane.’

Ta dan muskuta ta fara yiwa Anti bayanin abinda ya faru a kan umarnin da ya bata ta koma gidan yaransa har zuwa inda yace idan bata koma ba zaman kanta takeyi ba zamansa ba. Ta kara da

'Shine na taho.’

Mamakin Anti Uwani ya sake karuwa, domin duk wannan bayanin da Aishan ta dauki lokaci tana yi kara kulle mata kai kawai tayi; ta kasa gane dalilin da ya sa ita Aishan ba zata koma wajen yaran nasa ba. Tace

‘A’a! To ai dole yace zaman kanki kikeyi Aisha, matar nan ta mutu fa me ya sa ba zaki bi umarninsa ki koma gidan ki kular masa da yaran ba? Wannan ai kowa ma ya san haka ce zata kasance.’

Nan ta fayyacewa Anti Uwani dalilan da suka saka ba zata rike masa Yusra da Nana ba, ta bata misalan wasu daga cikin abubuwan da Yusran ta yi mata.

Suka yi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tace
'Kina da gaskiya Aisha, to amma fa gaskiya bana jin akwai wanda zai saurareki. Kowa cewa zai yi yarinya ce in an tsawatar mata zata daina; amma ni na fahimceki sosai. Rayuwa ce mutum zai yi ta yi rigima daga wannan sai wannan, kuma tsakaninki da miji kullum sai fitna.’

'To ai shine. Kuma ni Allah bai dora min zama da yaransa ba, ya kai su dangi uwarsu ko kuma ya auro wata ta rike masa su amma ba ni ba. Kinga ni uwarsu musamman take koya musu tsanata don haka zai yi wahala a sami wanda zai saukesu daga kan koyarwar uwarsu, amma kinga idan wata ya aura watakila su bata dama ta zauna da su.’

‘Hakane Shatu. Amma fa gaskiya duk bayanin nan naki babu wanda zai fahimceki fa don ina jin ko Hajiya ba zata saurareki ba. Ina ga gara kiyi hakuri ki koma in ya so a zauna da Yusufan ya tsawatarwa yarinyar watakila ki ga abun ya zo da sauki.’

Ta share kwalla sannan tace

'Wallahi Anti Uwani ba zai tsawatar mata ba, kuma ko ya tsawatar mata babu abinda zata fasa tunda yaran sun saba ba sa jin magabarsa. Ba zan iya rayuwa da wannan yarinyar ba wallahi don idan ta kasheni nawa marayun yaran ta cuta shi ubanta wata zai auro su cigaba da rayuwarsu. Idan kuma bata kasheni ba to in ta kureni nace zan dauki mataki a kanta wallahi kowa ba zai ji dadi ba tunda ai duk muguntarsu nima na iya Allah ne yake katangeni.’

Sukayi shiru na dan lokaci. Abun ya sha kan Anti Uwani sai dai ta san babu wanda zai fahimcesu. Ita ta san irin wadannan yaran don ta zauna da su, don daya har bayan an yi mata aure ma haka ta dinga zuwa cikin gidan tana haddasa fitna a karshe sai da ubanta ya saki Anti Uwani a kan laifin da ba nata ba. Ta muskuta tace

'Hmm! To yanzu ya za ayi Aisha?’

'Su Baffa suyi masa magana, idan ya dauke Yusra da Nana bani da matsala da sauran yaransa, ko dan shege ya bani kuma zan rike masa da amana. Amma idan dai aka ce sai na zauna da Yusra to gaskiya na hakura da aurensa.’

'A'a abun ma ba zai kai haka ba in sha Allah. Amma dai ina kokonton yiwuwar abinda kike so domin su fa maza gani suke kamar tunda suka aureki to ko me suka rakito dole ki zauna da shi. Iyayenku ma kuma goya masa baya zasuyi. Kuma daga baya idan ta kashe miki auren a cigaba da zaginki.’

'Duk ma abinda zasuyi sai dai suyi don wallahi Anti Uwani idan aka ce sai na zauna da yarinyar nan zaku nemeni ku rasa ba zaku sake gani na ba.’

Ta bata rai tana harara Aishan tace

'Bana son rashin hankali, kada na sake jin wannan zancen kin ji na gaya miki. Ki ci gaba da addu'a in sha Allah za a sami maslaha.'

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Anti Uwani ta tashi ta fice ta koma dakin Hajiya; inda ta tarar Farha har tayi bacci yayinda Hajiyan take zaune a kan dadduma inda ta idar da shafa'i da witri.

Nan ta zauna ta bawa Hajiya labarin abinda Aishan ta gaya mata. Cike ta mamaki da takaici Hajiya tace

'Kin ji ko Uwani, na gaya miki yarinyar nan fa bata da hankali har yanzu. Ya za ayi kina matsayin matar mutum kuma kice yaransa marayu sai kin zabi wadanda zaki rike masa?’

'To Yaya ai tayi mutunci ma tunda ita nata marayun ko daya bai zaba ba balle ya taya ta rikonsu.’

Ta harareta

'Kinga Uwani ki daina tunzura yarinyar nan fa. Ke da baki taba haihuwar nan ba ba kin zauna da ‘yayan kishiyoyin ba kala-kala, me ya kasheki? Duk sharrinsu ba haka suka hakura suka barki ba?’

Ta kawar da kai

'Na hakura na barsu dai Yaya bayan sun sa ubansu ya kore ni. Kuma zama da su din ai rayuwa ce wadda na cikin gidan yari ya fi ka ‘yanci kuma ko makiyi na bana yiwa fatan irin wannan rayuwar Yaya.'

Suka yi shiru na dan lokaci. Hajiya bata so ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar ba don ta san tabbasa ta sha wahala a hannun yaran kishiyoyi domin ita din Allah bai taba bata haihuwa ba. Kuma haka Allah ya hada ta da mijin da ya dinga auren mata suna haifa masa yara yana sakinsu, kusan duka yaran ita ta rikesu. Duk wata fitnarsu haka zai muttsike ido yace itace bata san ciwon yara ba don bata haifa ba, haka tayi wannan rayuwar kuma daga karshe ya saketa a kan laifin da ba nata ba.
Sai daga baya kafin rasuwarsa ya dinga kokarin mayar da aurenta ita kuma a lokacin ko sauraronsa bata yi ba.

Anti Uwani tace

'Idan gari ya waye zan gayawa Abubakar ya sanar da Baffansu; ai tayi mutunci ma tunda ba duka yaran tace ba zata rike ba. Tunda na bude ido nake zuwa islamiyya har yau ban daina zuwa ba kuma ban taba ji a cikin karatu an karanta aya ko hadisin da yace dole idan kina auren mutum ki rike masa yaran da baki haifa ba, hasali ma har aka gama bayanin masu riko babu matar uba a ciki to na me za ace sai ta yi? Idan yana so ta rike masa su kuma ai matarsa ce sai yayi amfani da dabara ya lallabata ba wai ya nuna mata isa ba. Kuma idan sun sabauta Aishan ai yaranta suka cuta da mu da muka haifeta, tunda shi ubansu aure zai kara ya cigaba da rayuwarsa.’

Cikin sanyin jiki Hajiya ta dafa hannun Anti Uwani tace

'Hakane. Bari dai gari ya waye Baffa yazo, idan aka bi abun a hankali za a sami mafita in sha Allah.'

Jimawa kadan Anti Uwani tayi mata sai da safe ta tashi ta koma daki; dukansu zuciyoyinsu babu dadi. Ita Hajiya ba da son ranta ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar auren ba wadda take cike da jarrabawa kala-kala ga rashin haihuwa, ita kuma Anti Uwani abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata tana tunani babu yanda za ayi ta bari Aisha ta shiga irin rayuwar da ita tayi.

Haka suka kwanta bacci kowa da abinda yake ransa.
Chapter 90 · 0% Book details