← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 100

Sashe 45

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Abba suna barin wajen Baabaa ya tsuguna ya budewa liman abinda yake cikin bakin yadin. Ya tsuguna yana dubawa bayan ya toshe hancinsa.

Ya karewa abun kallo yana fadin

‘Subhanallah.’

Ya saka tsinke ya gama jujjuya kan jabar ya kare masa kallo tas, ya sa waya ya dauki hoton abun sannan ya fara karanta addu’oi yana tofawa abun. Ya tofa kul a’uzai, kulhuwallahu, ayatul kirsiyyi sannan ya tofa la haula.

Yana cikin tofawa da yake zuwa lokacin kan ya dan yiwa Abba sauki commissioner ya taso ya zo ya sami Malam liman, ya tsuguna a kusa da shi da hancinsa a rike da hannunsa yana kallon ikon Allah. Bayan liman ya gama tofin commissioner yace

‘Malam liman wannan fa?’

‘Alhaji wannan da ka gani tsafi ne, ka ga wannan bakin kwadon da wannan allurar da aka soka a goshin kan nan Allah ne kadai ya san fitnar da suke haddasawa wanda akayi wannan ta’asar domin a cuce shi.’

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’

Ya dubi su Masta da suke tsaye a gefe yace

‘Kuma a gidan Yusuf din kuka sameshi.’

‘Eh wallahi, don ma mun dan haka ramin bishiyar da zurfi ne da ba zamu sameshi ba don an binneshi da zurfi.’

Liman ya dubi Baabaa yace

‘Balle min kwadon nan ka zare wannan allurar, yanzu sai a kunna wuta a kona shi. Shikenan ba zai sake tasiri ba da izinin Allah.’

Nan ya fara cukucukun balle kwadon yayinda Abba ya dubi Baabaa yace

‘Koma cikin gidan ka karbo ashana a wajen matar gidan.’

Kafin ya kawo ashanar Masta ya balle kwadon ya zare allurar, nan take liman ya matsa gefe daya ya hada ‘yan karare ya jefe abun ya kunna wuta. Suka dan matsa gefe shi da commissioner suna kallon abun yana ci da wuta, yayinda ya umarci su Masta da su shiga su shuka bishiyar amma su dan matsar da ita kadan daga inda suka cire abun.

Suna nan tsaye abun yana ci da wuta Abba ya dan ji ciwon kan ya sauka har ya fara samun nutsuwa, don haka ya taso ya zo ya samesu.
‘Malam liman me ya faru ne, menene yake wannan azabar warin don Allah.’

Ya nuna masa yace

‘Gashi nan an sa masa wuta.’

‘Ikon Allah, to meye wannan din Malam Liman? Kuma a cikin gidan suka samo shi?’

‘Eh, a ciki suka samo shi mana. Amma gashi an koneshi, kaji warin ma ai ya ragu sosai kuma da zarar ya gama konewa zai bi iska shikenan. Idan muka hadu a masallaci bayan tarawih in sha Allahu zaka ji bayani; don ka ga yanzu zan karasa gida ne kafin na sake fitowa masallaci.’

‘Hakane, to babu laifi.’
Sukayi sallama gaba daya, Malam liman da commissioner suka tsallaka.

Kafin Abban ya bar wajen su Masta suka fito suka ce masa sun gama. Ya tambayesu ko a nan zasu sha ruwa suka amsa da eh, don haka yace maigadinsa zai miko musu abinci gidan commissioner din su kara.

Har zai shiga gidan kuma sai ya fasa ya kama hanyar gidan Zahra. Wannan warin da ya shaka yau ya kusa sumar da shi gashi azumin yau ya wahalar da shi, baya son ya shiga gidan ya shan wahala.
…………

Suna hanya su biyu commissioner yace

‘Wai meye wannan din Malam liman, nifa ban gane ba?’

Saida ya jinjina kai sannan yace

‘Ai wato ranka ya dade wannan abun fa tsafi ne. Gaskiya asiri ne aka yi watakila don a raba shi da matarsa da take wannan gidan ko wani abu mai kama da haka.’

Ya dan zaro ido

‘Allah Malam liman?’

‘Ai kwarai kuwa. Kaga wannan kwadon da yake bakin abun nan to duk wanda aka yiwa wannan tsafin ba zai iya bawa wani labarin abubuwan da yake ji yake gani ba balle ma a taimaka masa da wani abu na magani. Wannan allurar kuwa da aka caka ina tabbatar maka itace musabbabin wannan ciwon kan da yayi da yaji wari. Yallabai ka kalli fuskarshi kuwa lokacin da ya shaqi warin nan? Baki fa fuskarshi tayi, don ni gani nayi ma kamar shirin zurawa da gudu yakeyi sai naga ka dafe shi.'

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Malam Liman kaji wata fitna, kai da iyalinka a shiga tsakaninki.’

‘To mutane basu tsoron Allah.’

Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa, jimawa kadan commissioner yace

‘Ai kuwa sai ka san yanda zaka bashi labarin nan don kada yaje ya fara zargin mutane fa, kaga bamu da wani tabbas. Musamman ita daya matar tasa. Tab! Allah abun tsoro dan Adam abun tsoro.’

‘Ai in sha Allah ba zan masa bayani sosai ba, tunda kaga ko a danginsa ma ko nata ita matar wanda ke jin haushinsu zai iya yi, ko kuma manemanta wadanda ya kasa ya aurota ko ma a kawayenta; komai zai iya faruwa. Shi yasa nace ya bari sai an jima don kafin nan na tsara abinda zan ce masa.’

Suka karasa maganganunsu kowa ya wuce gidansa.
--------

Haka kawai yake jin kansa cikin walwala, duk da azumin yayi wahala kuma gashi da la’asar da ya shaki warin nan ya galabaita; amma yanzu har ji yake kamar ma ya rage nauyi ko kuma an dauke wani abu mai nauyi da aka dade da dora masa a ka.

Cikin walwala ya sha ruwansa tare da yara, su kansu yaran har suna mamaki. Domin Yusra ita a tunaninta ma murna yake saboda saura kwana biyar Mommy ta dawo.

Tunda ta tafi yau ne kadai ya sha ruwa a falon kasa. Rahma da Jummai sai daki suka wuce bayan sun ajiye musu abincin suka barsu shi da yaransa.

Ana gama shan ruwa Mommy ta kirawo wayarsa kamar yanda ta sabarwa kanta; yana dauka ya fara yi mata korafin da kusan kullum sai yayi mata shi amma bata fasa ba.

‘Madam. Yanzu fa a nan Saudiya tarawih akeyi kuma yau daren ashirin da bakwai ai ya kamata ace kin manta damu kina can kina ibada fa, kar a ga daren lailatul kadari kina waya.’

Tace

‘Toh idan na jiku ai shine zan fi samun natsuwar ibadar ko? Ina masallacin ma fitowa nayi, da na gaisa da yara zan koma.’

Suka gaisa yana mamakin dalilin da ya sa kullum sai ta kirawosu kuma a dai-dai wannan lokacin. Ita kuwa dalilinta shine a lokacin ne kawai zata samesu gaba daya a tare kuma sannan Yusra zata karbi wayar ta shige daki tayi ta yi mata tambayoyi.
Gaba daya yaran sai da ta gaisa da su sannan daga karshe Yusra ta karbi wayar ta haye sama ta shiga dakinsu sannan suka fara magana da mommy.

Bayan ta gama bawa Mommy labarin abubuwan da suka faru a gidan tace

‘Shima Abban yau na ga sai wani jin dadi yake ko don kin kusa dawowa ne oho.’

‘Allah? Me kika ga yayi.’

‘Wallahi Mommy sai wani jin dadi yake, kinganshi can ma fa a kasa ya sha ruwa sai hira yake da kowa.’

‘Um, yanzu haka dadi kawai yake ji. Idan kin ga wani abu dai mayi magana gobe.’

Sukayi sallama ta dawo ta bawa Abban wayarsa.

Tun da suka gama waya da Yusran kuma sai ta shiga wasi-wasin dalilin da ya sa Abban yake walwala. Bata alakanta hakan da dawowarta ba ta fi dai tunanin ko yanayinsa ne haka a ranar, ta dai san ko menene babu Aisha a ciki tunda Yusra ta tabbatar mata baya shiga gidan Aishan. Haka ta cigaba da ibada tana tunanin abinda ya sa shi walwalar, don ji take kamar tayi tsuntsuwa taje ta gani.
--------

Wajen karfe tara da kwata bayan an idar da sallar tarawih Abba ya riko hannun Liman suka fito daga masallaci, suka dan matsa daga cikin mutane. Bayan sun gaisa Abba yace

‘Malam kace za muyi magana.’

‘Kwarai kuwa Alhaji Yusuf.’

Suka dan kara gyara tsayuwa, Malam liman yace

‘Wato Alhaji Yusuf wannan abun gaskiya irin suddabarun nan ne, tana iya yiwuwa anyi ne don a rabaka da ita amaryar kuma tana iya yiwuwa ma mutanen da suka zauna a gidan kafin ka zo sune suka binne. Amma yanda mukayi masa haka aka konashi to ko ma wa aka yiwa ba zai sake tasiri ba in sha Allah.’

Da tsananin mamaki a fuskarsa yace

‘Ikon Allah! Wato Malam Liman biri yayi kama da mutum.’

‘Allah ko Alhaji?’

‘Kasan an dauki lokaci bana iya shiga gidan nan duk yanda zan yi, ikon Allah. To yanzu wa zai yi min haka? Kai!’

Liman ya dafa kafadar Abba yace

‘Ai ba za a iya cewa ga wanda yayi ba Alhaji, irin wannan abune wanda ake hadawa da shaidanu. Su kuma shaidanu ka san zantukansu duk karya ne. Kowa ma zai iya yi; ko a kawayen ita matar gidan idan akwai wadda take jin haushinta zata iya yi ko wani cikin manemanta wadanda ka kasa. Abun dai sai addu’a, ko a hakan ma za a iya cewa addu’a ce ta kawo dalilin da yasa aka tono abun yanzu haka da ba za a ganshi ba.’

Ya jijjiga kai

‘Hakane kam, Allah ya sauwake.’

Suka dan taba hira, daga baya Abban yayi masa sallama ya kama hanyar gida.

Yana tafe yana tunani kala-kala; wa zai yi masa wannan muguntar. Yanzu dama wannan wahalar da yake sha idan ya shiga gidan Aisha dama da hannun wani? To waye zai masa haka? Zahra? Kai ya za ayi Zahra tayi irin wannan aika-aikar? To idan ba ita ba waye zai yi haka? To ko dai a kawayen Zahran ne kamar yanda ya fada ko kuma ‘yanuwanta wadanda suke jin haushinta?

Har ya je gida bai samo amsar ba, yana kara tambayar kansa abun yana neman ya sa masa ciwon kai. Ya hakura ya bude gate ya shiga.

Babu kowa a falon kasan duk sun kwanta don haka kai tsaye ya haye sama.
A falo ya zauna ya jefa wayar a kan kujera kusa da shi.

Babu abinda yake so yanzu kamar yaje ya ga Aisha. Ya mike kamar wanda aka tsikara ya nufi dining table, ya bude kwanukan ya duba. Salad ne da kuma madarar waken suya a jug wanda Yusra ta ajiye masa. Ya zauna ya ci salad din ya sha madara sannan ya mike ya shiga daki, mintuna kadan ya fito a shirye ya kulle dakin.
Chapter 45 · 0% Book details