← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 100

Sashe 14

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da aka yi wajen minti talatin sannan taji motsin saukowarsu, yana tafe Zahra tana biye da shi rike da jakarsa ta computer da litattafansa. Sai wani faman murmushi take suka jero suka shigo falon, ta dubi Aisha da fara’a tace

‘A’a, ina ‘yayan naki sukayi Anti Aisha shine suka barki ke kadai?’

Murmushi tayi tace

‘Yanzun nan suka fice ai.’

‘Kuma sai ki kashe TV, da kin canza channel din kawai.’

‘Uhm.’

Abban Sadik yace

‘To mu tafi ko?’

Ta mike ta dubi Zahra tace

‘To sai an jima, na gode.’

Ta mika mata 'yar karamar leda dauke da turaren wuta da wata karamar burner tace

‘To ga wannan amarya, sai mun shigo ni da yara.’

Sukayi mata sallama suka fice.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

10

Saida amarya ta kwana biyu sannan su Yaya Zuwaira suka kawo mata ziyara tare da Abdallah da Farha. Nan suka wuni ana ta hira, sai bayan la’asar sannan suka tafi, suka barta da kewarsu.

Haka Yusuf ya cigaba da kwantar mata da hankali har ta samu ta dan kara sakewa.

Ranar Talata ne ya kama kwana uku, don haka ranar ne zai koma kwanan Zahra. Ya riga yayi musu bayani da daddare zai dinga canza waje kwana don haka wadda zai kwana a wajenta ita zatayi masa abincin dare.

Bayan ya dawo daga sallar magriba ya sameta a falo tana kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya zauna a kusa da ita suna fuskantar juna, yace

‘Yanzu zan wuce wajen yayarki, amma gaskiya bana son barinki ke kadai. Kinga da a can kike da bani da wata damuwa.’

Tayi dariya ta dan kwanta a jikinsa

‘To ai ni ban ce maka ina jin tsoro ba, tunda idan ma wani abun ya taso zan iya kiranka ko na kirawo Mommy ko?’

‘Hakane, amma dai bari naje gidan sai na kawo miki Yusra ta zo ta taya ki kwana.’

‘To duk yanda kace.’

Sai da yayi da gaske sannan ya Kanye jikinsa ya tashi yayi mata sallama ya fice a kan yanzu zai dawo ya kawo mata Yusra.


A falo ya samesu gaba daya banda Sadik, bayan Mommy ta amsa sallamarsa duka sukayi masa sannu da zuwa. Ya karasa ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Mommy, ya dubeta yace

‘Wa zaki bawa kanwarki aro ne a tayata kwana?’

Ta dan tsuke fuska

‘To ai kaga dalilin da yasa nace a hademu kace tace bata so, ai na zata zata iya kwana ita kadai.’

Ya kalleta alamar tuhuma, ta kau da kai sannan tace

‘To ai gasu nan duk wanda ka daukar mata, sai dai Yusra itace take tayani kula da kannenta idan suna bacci.’

Nana da take zaune tana yin homework tace

‘Ni dai don Allah ba ni ba Abba nafi so na kwana a nan.’

Kafin ya amsa Rukayya tace

‘Abba bari na shirya muje, amma fa ban yi homework dina ba, ga hadda ma ina so Yaya Yusra ta biya min.’

Cikin fara’a yace

‘Kada ki damu itama Antin zata biya miki, kwaso kayanki kafin na sauko daga sama sai na raka ki.’

Ya wuce saman ya barsu a zaune.

Yana kulewa Mommy ta harareta

‘Ke wai wacce irin yarinya ce Rukayya, kin ji kowa ya ce ba zai je ba sai ke uwar sakarci ko? Idan ya kuma zuwa yace wa zai je kika amsa sai na ci mutuncinki wallahi, kin ji na gaya miki.’

Tayi tsuru-tsuru tana mamakin yanda kawai don tace zata kwana gidan amarya abun ya bata ran Mommy haka. Yusra ta harareta tace

‘Sai ki tashi kije ki hado komatsanki kafin ya sauko kuma.’

Ta tashi jikinta babu kwari ta nufi sama inda dakinsu yake.

Tare suka sauko ita da Abban tayiwa Mommy sai da safe suka wuce, yana kula da yanda yanayinta ya canza don haka ya tabbatar fada Mommy tayi mata.

Bayan ya rakata ya tabbatar Aisha ta kulle kofa sannan yayi musu sallama ya dawo.

Dakin baki Aisha ta nuna mata ta ajiye kayanta, sai a hankali Rukayya ta sake sukayi homework din kuma ta biya mata haddarta, suka dan taba hira suna kallo sannan wajen karfe goma na dare aka dauke wuta.
Aisha ta shiryo suka kwanta tare da Rukayya a dakin baki.
……

Saida ya gama duk abinda yakeyi, ya zauna a falon sama yana kallon TV. Bayan yara sun kwanta itama ta zo ta zauna a kusa da shi, jimawa kadan ya dubeta yace

‘Zahra.’

Da murmushi ta dubeshi ta amsa

‘Yallabai.’

Ya gyara zama ya fuskanceta sosai

‘Ban ji dadin abinda kikayi ba, don Allah ki bar yaran nan su yiwa Aisha duk abinda take so wanda bai sabawa addini ba. Ina laifi idan yara sun tayata kwana, amma nayi magana kince ai ita ta zabi haka. Kuma Rukayyan ma saida kikayi mata fada saboda kawai na sakata aiki tayi.’

Ta bata rai tace

‘To ni me nace, shikenan ba zan fadi ra’ayi na ba saboda matarka. Yara kuma ai naka ne, ni babu wanda na hana idan ma Rukayya ce ta gaya maka nayi mata fada to karya takeyi.’
‘Ni dai don Allah kiyi min alfarma ki bari a zauna lafiya, don Allah.’

‘Uhm.’

Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya kuma ta tashi ta wuce dakinsa ta kwanta tana matse kwalla. Wato daga ya dana dadin amarya kwana uku kacal har ya fara nema yayi mata fada a kan matarsa, lallai zata gyara musu zama. Haka ta kwana zuciyarta babu dadi.

Daga wannan lokacin ya zama kullum idan zai kwana gidan Zahra to Rukayya ce take taya Aisha kwana, tun tana dagewa har ta hakura. Kuma sai ya zama jininsu ya hadu da na Aishan suka zama kamar wasu kawaye duk da dai Rukayyan tana shan gori a wajen Mommy da Yusra.
-----

Ranar Alhamis da magriba bayan ya gama shirinsa zai koma wajen Aisha Mommy take gaya masa ita da yara zasu je wajen Hajiya gobe Juma’a don sun kwana biyu basu je ba. Har ya fita ya dawo yace mata zai gayawa Aisha don haka idan sun shirya suyi mata magana sai su tafi gaba daya tunda driver ne zai kaisu. Yayi mata sallama ya wuce.
----

Itama Aishan yana shiga ya sanar da ita gobe da yamma zasu je gidan Hajiya da su Zahra, don haka da gari ya waye yana fita office ta kama hidimarta don tayi sauri ta gama. Ya riga ya gaya mata sai bayan masallaci amma duk da haka tana gama aikinta wajen sha biyu ta sa hijabi ta nufi gidan Zahran.

Babu kowa a gidan sai ita kadai da Jummai wadda take share tsakar gida, tun a nan suka gaisa da Jummai ta wuce ciki.

Tana zaune a falo tana ta faman latsa waya tayi sallama ta shiga bayan ta amsa mata. Da fara’arta ta karasa ciki ta zauna a kujerar mutum daya.

‘Ina kwana Mommy.’

Sai da ta kalleta ta gatsine fuska sannan ta amsa da kyar

‘Lafiya kalau.’

Sukayi shiru na dan lokaci, ita Zahra ta cigaba da duba wayarta kamar babu mutum a wajen yayinda ita kuma Aisha take mamakin wannan tsare gidan da muzuran da ake mata. Ta yi dan gyaran murya tace

‘Uhm, Abban Sadik yace zamuje gidan Hajiya da yamma shine na leko mu gaisa. Idan kun shirya ko yara suyi min magana sai mu tafi.’

‘To.’

Ta mike tsaye tayi mata sallama ta fice, ita kuma tabi bayanta da harara harda kwafa saboda kishi.

Ta tsani ganin matar nan, gashi dai an ce bazawara ce amma kamar budurwa. Kuma ta zata Malam Sule direbanta ne ita kadai amma za ace su wani hada fita.

Ta ja tsaki ta cigaba da abinda takeyi.
……

Sai wajen karfe hudu saura sannan Zahra ta shirya, ita da yaranta gaba daya banda Sadik, domin shi yace ba zai je ba. Suka fito gaba daya suka shiga mota, har Yusra zata shiga gaban mota Mommy tace ta dawo baya. Don haka suka shiga bayan motar gaba daya, ita da Yusra, Rukayya, Nana da kuma Ummi duk da wajen zaman Ummi bai kai na mutum daya ba.

Yusra ce tacewa Malam Sule

‘Malam Sule ka tsaya a kofar gidan matar Abba da ita zamu tafi.’

Suna fitowa yayi parking a gate din Aisha ya latsa honk, ya juyo yacewa Yusra

‘Ko kirawo mana ita zakiyi.’

Mommy tace

‘Kayi mata honk din zata fito ko kuma ka buga mata gate.’

Yanayin da tayi maganar ya sa babu damar musu don haka kawai sai ya fita ya buga gate din, bugu daya ta bude. Cikin girmamawa ta gaisheshi tace

‘Bari na dauko jakata a shirye nake.’

Ta koma cikin gidan shi kuma ya koma mota ya zauna.

Jimawa kadan ta fito ta mayar da gate din ta rufe ta karaso jikin motar ta bude ta gefen da Yusra take zaune tare da sallama tana fadin

‘Yaya Yusra dan matsa na zauna, ko Nana ce zata koma gaba sai mu zauna a bayan.’

Dukansu suka kara babbakewa Yusra ta banka mata harara yayinda Rukayya ta sunkuyar da kanta, Mommy tace

‘Basa shiga gaban mota.’

Ta kallesu da mamaki sannan tace

‘Umm, to ku dan gyara sai na shigo mu zauna nan duka.’

Mommy tace

‘Gurin ba zai isa ba ai baki gani bane, ki zauna a gaban mana ke.’

Mamakin Aisha ya karu, kafin tayi magana Malam Sule yace

‘Ina ga ai ko Ummin Abban aka miko nan ai wajen zai isa Hajiya.’

‘Malam Sule, ka san dai Yallabai baya barin yara zaman gaban mota ko? Ta shiga gaban kawai muje in ba haka ba ka kaimu sai ka dawo ka kaita.’
A tunzure tayi maganar don haka Malam Sule yayi shiru.

Aisha ta dan ja baya, nan da nan Yusra ta ja kofar motar ta rufe yayinda Mommy tace

‘Mu tafi.’

Ya tada motar ya leko ta taga yacewa Aisha

‘Ranki ya dade yanzu zan dawo in Sha Allah.’

Yaja motar suka barta a nan tsaye tana mamaki.
Chapter 14 · 0% Book details