← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 100

Sashe 16

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Sun shiga bayan mota ita da Yara, nace su matsa na zauna tace wajen ba zai ishemu ba, nace to Nana ta koma gaba sai na zauna ni a bayan. Tace yaranta baza su shiga gaban mota ba sai dai ni na shiga, ni kuma naga da aurena, ina matarka kuma na shiga gaban mota da direbanka ai ba daraja. Shine tace ya kaisu ya dawo ya kaini, ni kuma kafin ma ya dawo na hau tasi na tafi.’

‘Ni ba haka aka gaya min ba, kuma bana jin Zahra zatayi haka tunda yaran ko makaranta Sule zai kaisu suna shiga gaba. Kuma a dawowa me yasa baki biyosu ba tunda a lokacin Anisa tace Yusra gaba ta zauna.’

Ta riga ta fuskanci inda zancen ya dosa don haka cikin halin ko in kula tace

‘Saboda ban san irin shirin da suke dashi ba a dawowar shi yasa kawai na dawo ta hanyar da na tafi.’

Suka yi shiru na dan lokaci, sannan daga baya yace

‘Aisha! Bana son fitna irin wannan, saboda na raba muku gida ba zai yiwu kice ba zaki hada mu’amala da Zahra da yarana ba. Shekaru wajen sha bakwai nake zaune da ita ban taba samun matsala da ita ba, gaskiya ba zan dauki irin wannan ba.’

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makoro tace

‘Ai baka taba yi mata kishiya ba sai yanzu ku…'

Ya katseta

‘Ni dai na gaya miki gaskiya ba zan dau wannan ba, yanzu Hajiya sai fada takeyi saboda abun da kuka yi.’

‘To ai na gaya maka ba laifina bane, ka bincika kafin ka yanke hukunci.’

‘Mtsewww! Ni dai na gaya miki don kin sa na raba miki gida da iyalina ba wai yana nufin ba zakiyi mu’amala da su ba, kuma kece karama dole kiyi hakuri ki bita idan wata sabga ta hadaku. Wannan din ma kuma zan bincika kuma zan dauki matakin a kan mai laifi.’

Ya mike ya shige daki ya barta a nan.

Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, har ya shige ya turo kofa.
Wannan shine a doke ka a hanaka kuka; ita aka yiwa wulakanci amma ita ake zargi tayi laifi. Ai kuwa ko me zai yi sai da yayi amma bazata taba daukan laifin da ba nata ba.

Ta riga ta gama shirin kwanciya bacci domin kayan bacci ne ma a jikinta, don haka itama ta mike ta kashe wutar falon ta wuce dakinta ta kwanta.

Ba zata iya binsa dakinsa ba don bata son zama da mutum idan yana jin haushinta; ko waye shi, kuma bata ga laifin da ta yi masa ba balle ta bashi hakuri. Ta kashe fitila ta kwanta bayan tayi adduointa.

Sai da ta kwanta sannan hawaye ya kwace mata; fadan da yazo yana yi mata ya fi bata mata rai a kan abinda Zahra tayi mata don ita za a iya cewa kishi ne. Amma shi ya zo yana gaya mata dole ta kula iyalansa; kenan ma har yanzu ita bata zama iyalinsa ba kenan? A haka har bacci ya kwasheta.

Tana jinsa ya fita masallaci da asuba, itama ta tashi tayi sallah ta sake komawa, sai wajen karfe bakwai sannan ta fito ta shiga kicin. Nan da nan ta soya doya da kwai ta zuba ta dora a dining table ta koma daki ta yiwo wanka ta shirya, har ta fito bai fito ba.
Don haka ta zuba nata abincin ta zauna ta kunna TV tana ci tana kallo.

Ta kusan cinyewa ta ji motsinsa, yana shigowa falon ta gaisheshi ya amsa ba yabo babu fallasa. Kan table kawai ya wuce ya zauna zai fara cin abinci, ta tashi ta hada masa shayi ta zuba masa abincin kamar yanda ta saba sannan ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta.

Yana gama cin abincin ya tashi ya fice ba tare da yace mata wani abu ba, duk da dai ta san gidansa ya tafi.

Yana zuwa bakin gate din gidan Malam Sule yana sauka daga acaba, ya karasa da sauri ya kwashi gaisuwa.

Abban ya matsa gefe ya ce

‘Yauwa Malam Sale, dama Ina nemanka. Ni jiya wai ya akayi kuka tafi gidan Hajiya ba tare da Aisha ba?’

Ya shafa kai

‘Ranka ya dade ai mata sai hakuri, rashin fahimta ce aka samu ni kuma na rasa yanda zanyi da su ranka ya dade. A dai bata hakuri.’

‘So nake ka gaya min tsakanin da Allah Malam Sule don Allah kada ka boye min, me ya faru? Ya akayi baku tafi da Aisha ba?’

A hanakli malam Sule ya koro bayani, yayi masa bayanin abinda ya faru har zuwa lokacin da suka dawo. Ya dora da

‘To kaga yallabai babu yanda zanyi, kuma ai bai kyautu Ina tuki ace ta zauna a gaban mota ba, ai ko Yusra ta girma kamar haka ai ta shiga baya na tuka ta balle matarka ta aure ranka ya dade. Amma a dai yi maslaha yallabai lamari ne na kishi.’

Ya jijjiga kai kawai yace

‘Nagode Sule, nagode.’

Ya juya ya bude gate din suka shiga.

Kansa ya kulle gaba daya; yanzu ya za ayi Zahra tayi haka, kuma sannan jiya ta zauna ta tsara masa zance yaje yanata yiwa Aisha fada. Ya tuno yanda take kallonsa lokacin da ya hakikance yana fada.

A zatonsa ya san Zahra shi yasa ya kama zancenta don bai zata zata yi masa karya ba, ashe ma bai santa ba. Ranshi yayi matukar baci; babban damuwarsa yanda ta dora Hajiya a kan karya har take jin haushin Aishan, ya san kawo yanzu kaf danginsa sun ji zancen nan.
Ya karasa cikin gidan ya shiga da sallama.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

11

Ranar asabar ce don haka yana shiga ya samesu a falo ita da Yusra, Nana da Ummi domin ragowar basu tashi ba. Da gudu Ummin ta rungumeshi tana masa oyoyo, gaba daya suka gaisheshi. Itama Mommy tayi masa sannu da zuwa ya amsa ba yabo babu fallasa, ta san dai akwai matsala daga yanayin yanda ya amsa ba tare da bata lokaci ba ya haye sama. Nan take ta tashi ta haye tabi bayansa.

A zaune ta sameshi a dakinsa a kan kujera, ta wuce ta zauna a gefen gado tace

‘Ya kwanan amarya?’

‘Alhamdulillah.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace

‘Zahra, me yasa kika yi min karya?’

Taji wani banbarakwai, mamaki ya kamata

‘Uhm, karya kuma?’

‘Eh, kika ce min Zahra kin binku tayi ku tafi gidan Hajiya bayan cewa kikayi ta shiga gaban mota?’

Tayi tsuru-tsuru, ta sunkuyar da kai zuciyarta cike da takaicin kiranta makaryaciyar da yayi

‘To motar ta cika, gaban motar ne kawai da waje aka ce ta zauna kuma taki.’

‘Amma kin san gaban mota ba wajen zamanta bane tana matar aure, don me Yusra ko Nana bazasu shiga gaban motar ba?’

Ta sha kunu ta kauda kai, sukayi shiru na dan lokaci yana kallonta yana sauraron amsarta. Tace

‘To yanzu kafi kishin matar da ka auro kwanannan a kan yaranka, naga dai suma sun balaga ko?’

Mamakinsa ya karu

‘Oh! Da baki san sun balaga ba kike barinsu suna shiga gaban motar idan zaku fita ko kuma idan za a kaisu makaranta? Ko kuwa sai jiyan suka balaga?’

Ta murgude baki ta kawar da kai

‘Gaskiya bana so, kada ki sake yi min irin wannan. Ba zan dauka ba, yara su shiga gaban mota ku ku shiga baya idan ba haka ba wallahi zan dau mataki a kai kuma matakin ba zai yi miki dadi ba.’

‘Uhm, yanzu dai zugo ka tayi dani da Hajiya kazo kace mu makaryata ne kenan.’

Yayi yake cike da takaici

‘Karyar dai da kika biyawa Hajiya, ai Hajiya bata san me ya faru ba sai abinda kika gaya mata. Kada ki sake yi min irin wannan na gaya miki.’

Kafin tace wani abu ya fice daga dakin yana saukowa ya fice daga gidan ya nufi gidan Aisha.

……..

Yana shiga ya sameta a kicin tana wanke-wanke, yanda bai yi mata sallama ba bata sa rai zai ce mata ya dawo ba. Ga mamakinta sai ya karaso kichin din yace

‘Na dawo.’

Ta juyo tana rike da kwanon da take wankewa tace

‘Sannu da zuwa.’

Ya amsa yayinda ta juya ta cigaba da wanke-wankenta shi kuma ya shige ciki.

Har yayi wanka ya fito tana kicin din, tana hada kayan abincin rana saboda idan ranar tayi sai kawai ta dora. Ya leko kicin din tana tsaye tana yanka kabeji, yace

‘Har yanzu ba a gama ba?

Ta juyo tace

‘Um, aikin ne da yawa.’

‘To sannu da aiki.’

Ya koma falo ya zauna ya kunna TV, yana kallo amma hankalinsa baya wajen, yana ta tunanin yanda zai yi da Aisha don ya kula fushi takeyi da shi. Yana sane da cewa jiya bata kwana a dakinsa ba amma shima a jiyan fushi yayi saboda abinda aka ce masa tayi, saida ya ji daga bakin Malam Sule da kuma yanda Zahran tayi masa da yayi mata magana sannan ya san bai kyautawa Aisha ba.

Yana nan zaune ta zo ta wuce daki, yayi zaton zataje ta dauko wani abun ne yaji shiru bata fito ba har wajen minti talatin. Don haka ya tashi ya bi bayanta; dakinsa ya fara dubawa bata ciki sai dai kawai ta gyara dakin don haka ya wuce dakinta.

Tana zaune a kan gadonta ta mike kafa da novel a hannunta tana karantawa, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ta gyara zama ta dan matsa don ya sami wajen zama sosai.

Yayi gyaran murya yana ta wani murmushi da yake bata mamaki tunda a saninta fushi yake da ita don ko da zai fita bai ko kalleta ba.

Yace

‘Um, ya kika zauna a nan? Yau ba kallon Zee World don ne?’

Ba tare da ta kalleshi ba tace

‘Um, karatu nakeyi.’

Suka yi shiru na dan lokaci yana kallonta, yaga dai bazata kulashi ba, ya kirawo sunanta

‘Aisha’

‘Na’am.’
Chapter 16 · 0% Book details