← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 100

Sashe 35

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dai kau da kai ne ga abun saboda bata so aure ya rabata da yaranta; yanzun ma kuma bazata bari aure ya shiga tsakaninta da su ba.
Jimawa kadan ta gama hada musu kayansu ta janyo karamin akwatin ta fito falo yaran suna biye da ita. Ta ajiye akwatin a bakin kofa ta wuce kicin ta sami roba ta juyo kazar da ta soya musu tazo ta ajiye a kusa da akwatin. Ta shige dakin Abban tana rike da mukullin mota ta tsaya bayan ya amsa sallamarta tace

‘Zan je na mayar da su Abdallah gida.’

Ya tashi daga kashingiden da yayi ya dubeta da mamaki

‘Daga dan wannan abun da ya faru, ki barsu su gama kwankinsu ranar Lahadi sa tafi. Yusra nayi mata fada ba zata sake dukan kowa ba.’

‘Babu komai, sun fi so su tafi. Zan mayar dasu din ai yanzu zan dawo.’

Bai ga alamar zata fasa ba kuma baya son rigima da ita don haka yace

‘Allah ya tsare, sai kiyi sauri kafin dare yayi sosai. Bari na taso na fice sai ki rufe gidan tunda ba nan zan kwana ba.’

Kusan tare suka fito falon, ta dubi Rukayya tace

‘Ki bi Abbanki Rukayya, idan na dawo zan masa waya sai ki dawo.’

Sai da ya rufe mata gate sannan ya kama hannun Rukayya suka nufi gida. Yana mamakin irin wannan fushin na Aisha, ita idan akayi abu ko magana bata fiya son yi ba sai dai kawai ta yi shiru tayi ta faman fushi. Yanzu ya san sai ya kai sati yana lallabata kafin ta bari su dawo yanda suka saba.

Suna dab da shiga gidan ya cewa Rukayyan

‘Wai da gaskene Farha ta cewa Yayarki Mai siffar karuwa?’

Da sauri ta bude bakinta ta rufe da tafin hannunta tana zaro ido, ta ajiye hannun tace

‘Tab, wallahi Abba babu wanda yayi zagi a falon nan. Tana taka ta ma tace sorry, kafin ta gama magana ta mare ta, gaskiya bata zageta ba. Farha ma ai bana jin ta iya zagi wallahi.’

Shiru kawai yayi saboda takaici; to ya akayi Yusra ta iya karya haka, gashi har Mommy tana goya mata baya?

Zuciyarsa a jagule ya shiga gidan, suka rabu da Rukayya a falo ya haye sama.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

21

Babu kowa a falon saman don haka ya wuce ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku ya zuba tagumi. Wannan abun da ya faru yayi masa ciwo, yanzu Yusra har ta san ta kirawo kanta mai siffar karuwa saboda tana so tayi wa Farha mugunta? To me ya hadata da Farhan da har ta mare ta haka; don tabbas shi kansa yaga yanda yatsun Yusra suka kwanta a kan fuskar Farhan. To Mommy ce ta tsara musu wannan karyar ko sune suka tsara mata?

Ya tuno fuskar Aisha lokacin da yake ce mata ta dinga yi musu fada; tabbas bai kyauta ba. Yanda Aisha tayi ya san taji zafin abun amma ya zata son zuciya ne kawai saboda yanda take son yaranta.

Sai a lokacin ma yaga rashin kyautawarsa da bai je ya kaita gidan ba; take ya fara nadamar barinta ta fita gashi baya son fitar dare.

Sallamar Mommy ce ta katse shi, bayan ya amsa sallamar ta wuce ta zauna a kusa da shi. Bayan tayi masa sannu da zuwa tace

‘Na gama abinci fa, ko sai kayi Sallah.’

‘Eh, bari nayi sallar a daki don masallaci ma kafin na kai sun idar.’

Ya tashi ya shige daki ya barta.

Sai da yayi Sallah ya fito yaci abinci ya gama, ya dawo tsakiyar falon ya zauna yana kallon labarai a Aljazeera. Mommy tana zaune a kusa da shi tana rike da Sumayya ya dubeta yace

‘Kirawo min Yusra.’

Ta tashi ta fice ta tsaya a kafar bene ta kwalawa Yusra kira,nan da nan ta hawo saman. Abban ya dubeta yace

‘Kirawo Nana ku zo tare.’

Ta juya jimawa kadan suka dawo tare da Nanan.

Nan suka zauna a gaban Abban, saida ya dan dauki lokaci sannan ya dubi Yusra yace

‘Kika ce Farha ta ce miki mai siffar karuwai ko?’

Cike da tabbas ta ce

‘Eh Abba.’

‘Me yasa kuka yi min karya?’

Yusra ta zaro ido tana kallonshi

‘Abba ba fa karya bane wallahi haka aka yi.’

Yayi gajeriyar dariyar takaici da mamakin yanda Yusra ta kware da karya haka. Yace

‘Akwai CCTV camera a falon, da na duba ba haka na gani ba. Ta fito daga kicin ta takaki kuma kamar ma tace miki sorry shine kika mareta kamar kina marin sa’arki shi kuma Abdallah yana tasowa kafin ya karaso kusa dake ma kikayi fatali da shi kuma kika zage su. Ko na gaya miki zagin da kika yi musu?’

Cikin sanyin jiki ta sunkuyar da kai yayinda Nana ta fara kokarin buya a bayanta itama tana sunkuyar da kai.

Ya nuna Yusra yana fadin

‘Kika sa naje ina yiwa yara fada ashe kece makaryaciya kuma kece me yin zagin sannan kika zo kika kirawo kanki mai siffar karuwa, ke kin san meye karuwa kuwa? Ki rasa abinda zaki siffanta kanki da shi sai karuwa?’

Sukayi tsamo-tsamo babu wanda ya iya magana. Yayi shiru yana sauraronsu, Mommy tace

‘Au yanzu dama ba haka aka yi ba Yusra kuka zo kuka tsarawa mutane karya?’

Nana tace

‘Mommy wallahi Yaya Yusra ce.’

Ya kalli Mommy kallo na takaici, ta dauke kanta.
Ya dubi Yusra yace

‘Allah ya shiryeka, amma dai ki sani wannan abun da kika yi karya ce da annamimanci kuma kin kai shekarun da komai kikayi Allah zai tambayeki a kai. Duk hakkin wanda kika dauka kuma idan bai yafe ba sai kin biya.’

Ya mayarda dubansa ga Mommy; wadda itama jikinta yayi sanyi saboda bata taba zata karyane abunda suka gaya mata ba, domin suna shigowa suka gaya mata haka itakuma tacewa Yusran tayi dai-dai; yace

‘Wannan shine abinda ya kamata ki mayar da hankali a kai ba shirme da sa idonki a inda bai kamata ba, Allah ya shirya.’

Ya tashi ya wuce daki ya barsu a nan itada yaran.
Cikin fushi tace

‘Yusra me ya sa kuka fadi karya kuka sa nima na hau kai?

Ta zumbura baki tana kawar da kai tace

‘Mommy yarinyar ce wallahi take bani haushi, bana sonta.’

‘Kada ki sake yi min irin wannan, sai ki gaya min ainahin abinda ya faru in ya so sai na san yanda za ayi. Ku tashi ku bani waje.’

Suka fice suka barta a nan cikin damuwa.
…………..

Wajen karfe tara na dare saura kwata suka shiga gidan Umma. Waya tayiwa Umma don haka tana danna horn Anti Uwani ta bude kofa, bata shigar da motar ba tayi parking a nan bakin gate.
Ta dauki Farha wadda ta fara bacci shi kuma Abdallah yabi bayanta, suna shiga farfajiyar gidan Anti Uwani ta karbi Farha tana fadin

‘Allah ya sa dai lafiya, me ya sami Farhan? Ko bacci ne?’

‘Eh bacci ta fara.’

Suka karasa ciki.

Umma tana zaune a falo don haka suka zauna nan. Bayan sun gaggaisa da yake da wuta Anti Uwani sai ta kunna musu cartoon, suka zauna har Farha wadda ta tashi daga baccin suka fara kallo.

Aisha ta tashi ta shige dakin Hajiya, tana shiga ta zauna a gefen gado ta zuba fuskarta a tafukan hannunta tana ajiyar zuciya. Jimawa kadan Anti Uwani ta shigo dakin, takarasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi tana fadin

‘Ikon Allah, wai lafiya kike Aisha naga dazu kika tafi da yaran nan kuma Lahadi kika ce zaku dawo wai me ya faru ne?’

Ta sauke hannuwanta ta bude baki zatayi magana sai hawaye, Anti Uwani ta mike ta leka falo ta kirawo Umma. Suka saka Aisha a gaba suna tamabayarta tana share hawaye, saida ta gama share hawayen sannan ta basu labarin abinda ya faru.

Umma tace

‘To ai wannan ba abun kuka bane, suma su Farhan ai da gatanasu ba gashi kin dawo da su ba. Kuma kin san halin yaran yanzu tunda dama ke da kanki kince yarinyar nan uwarta take tayawa kishi ai kuwa kinga zatayi abinda yafi haka ma.’

Ta sake share kwalla sannan tace

‘Nima abinda tayi bai bani haushi ba, abinda ubanta yayi ne ya fi bata min rai. Ai dama ba tun yau ba na gaya miki baya son su Abdallah suje don idan suna nan yayi ta muzurai kenan yana faman saka ni aiki. Da zarar na mike zanyi hidimarsu sai ya san abinda yace nayi masa, har gara ma idan ba kwanana bane sai mu sake ni da su. Yanzun kuma yana kallon shatin yatsun Yusra a kan fuskar Farha amma bai wani damu ba, bayan yaje sun tsaro masa karya da gaskiya ya dawo yace min wai Farha ta cewa Yusra mai siffar karuwa. Don Allah Umma yaushe Farha ta san karuwa, ai ko kalmar siffa ma bana jin Farha ta san ma’anarta; shekarunta hudu fa kacal.’

Anti Uwani tace

‘Ai ce masa zasuyi ke kika gaya mata shi yasa zai hau kai ya zauna, idan dai son kai ne ai kika sami namiji kin kure.’

Umma ta harari Anti Uwani sannan ta dubi Aisha tace

‘Duk wannan ba wani abu bane, wannan ya wuce ai sai ki tashi ki koma dare yana yi.’

Aishan ta kalli Anti Uwani tace

‘Shi da kansa yake yaba tarbiyyata amma yanzu da yake yaso son zuciya ce min yake yaransa basu iya zagi ba nawa ne suka iya.’

Tayi kwafa.

Anti Uwani ta dawo kusa da ita ta dafa kafadarta tace

‘Yi hakuri kin ji Shatu, sai dai su gani a kansu ba dai mu ba.’

Haka suka sakata a gaba sunata bata baki, zuwa tara da rabi ta taso ta fito ta kamo hanya.

Bayan ta fita Umma ta dubi Anti Uwani tace

‘Uwani ki daina taya yarinyar nan rigima fa, kin santa da taurin kai ga fushi.’

‘Yaya wallahi dole na tayata, duk taurin kanta da ake gani amma tana da hakuri. Ba karamin kureta akeyi ba kafin ta fara fushin da taurin kai, Allah ne kawai ya san abubuwan da take hadiyewa a wannan gidan don haka duk abinda ta fada ai dole na tayata Yaya.’
Chapter 35 · 0% Book details