← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 100

Sashe 10

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Kan bala’i! Har ya kama hayar gida amma sai jiya kika sani. Lallai abun babba ne Mommy.’

A daidai nan Sadik ya turo kofar ya shigo, ya tsaya a bayan kofar yana sauraron karshen zancen Yusra. Ya dubi Mommy yace

‘Menen babban abun kuma?’

Kafin mommy tace wani abu Yusra tace

‘Abba ne zai yaure next week ma za a daura auren.’

Shima ya zaro ido, ya karasa ya zauna kusa da Yusra yana fadin

‘Lallai, amma ko labari.’

Yusra tace

‘To Mommyn ma sai jiya ya gaya mata ai.’

Yayi 'yar gajeriyar dariya yace

‘Lallai, ashe akwai biki kenan.’

Yusra ta balla masa harara, ya dubi Mommy yace

‘Kin san fa irin auren nasa, wancan karon haka ya tashi mutane a tsaye kuma ya zo ya fasa. Ki sa masa ido kawai kiga gudun ruwansa.’

Mommy tace

‘Hmmm!’

Sukayi shiru na dan lokaci, Sadik ya karya shirun yace

‘Mommy jiya fa kince zaki bani dari biyar na saka data, ita na zo tuni.’

‘Ga jakata can ka dauka.’

Ta fada tana nuna masa jakarta wadda take kan mudubi.

Nan da nan ya mike ya dauki kudin ya fice. Ya bar su Mommy tana ta kara gayawa Yusra maganganun da zasu sa taga kamar Abba wulakanci yake so yayi mata shi ya sa zai kara aure.

Shi kuwa Sadik ficewa yayi yana mamaki, duk da ya san auren ba wani tasiri zai yi ba. Duk da haka yanzu kam ya san shi dai babu wata matar da zata zo tace zata bata masa rai ko tayiwa Mommy ba daidai ba; tabbas zai saita yarinya komai girmanta. Musamman da yake shi din dogo ne kuma yana da zati kamar mahaifinsa, don haka yake jin kansa komai ma zai iya.
……

Haka ta wuni ranar ba tare da walwala ba, shi kansa Abban Sadik din ya gane halin da take ciki. Sai dai da yake ya riga ya san tana da kishi kuma ya san yayi mata laifi sai ya kau da kansa yana fatan nan da wani dan lokaci zata huce.

Wajen karfe uku na yamma yara suka tafi islamiyya, ana yin sallar la’asar kuma Abbansu ya shirya zai fita don haka itama ta shirya tace ya sauketa a gidan kanwarta Suwaiba.

Saida ta ci kukanta ta koshi Suwaiba na bata hakuri sannan ta zaro katin daga jakarta ta mikawa Suwaiban tace
‘Tsabar wulakanci sai jiya na sani kuma bayan da fari ce min yayi basu ma gama daidaitawa ba.’

Ta dauki katin tana dubawa tana tabe baki, tace

‘Hmm! Maza ai sai hakuri lamarinsu, ga munfuncin tsiya.’

‘Wallahi zan yi maganinsu da shi da ita bazawarar tasa, zan ga shegiyar da zata zo gidana tace zata zauna da mijina lafiya.’

Haka suka dauki lokaci Suwaiba tana bata hakuri har ta dan sami natsuwa, ba jimawa kuma ta mike tana fadin

‘Bari kiga na tafi kafin ya shanya ni har yara su dawo daga islamiyya, na san yanzu haka wajenta ya tafi.’

Suwaiba ta mike tana murmushi

‘Ah! Yaya Zahra, shikenan kuma babu inda zai je sai wajenta.’

Tayi kwafa kawai ta nufo kofa, Suwaiban tayi mata rakiya sukayi sallama ta kamo hanyar gida. Sai da ta iso gida sannan ta kirawo shi tace masa ta koma gida ba sai yaje daukanta ba.

Babu kowa a gidan sai Jummai da take karasa wanke wanke, ta bata abinda zata dora mata na abincin dare ta haye sama.

Tana zama a daki ko mayafi bata cire ba ta kirawo Mallam ta sanar da shi aure ma saura kwana bakwai, tayi masa bayanin uzurin da Yusuf din ya bata. Bayan ya gama sauraronta yace

‘Ikon Allah, tabbas akwai wata a kasa don babu mamaki ba haka suka barshi ba. Yanzu haka akwai aikin da suka yi masa don ayi gaggawar daura auren. Amman kada ki damu, da kaina zan fara aikinki wanda mukayi magana yau din nan. Sannan kuma idan ban samu na gama ba to akwai abinda zan baki ki daga carpet ki saka ta daidai inda zata tsallaka idan an kawo miki ita, in dai ta tsallaka to da izinin Allah rana tana fitowa zasu fito tare ta bar gidan kenan har abada.’

Sai da tayi ajiyar zuciya tana murmushi saboda jin dadin wannan bayanin na Malam Hatimu mai almajirai, tace

‘Malam ka san fa da mutane za su zo,dole wasu ma zasu tsallaka ta wajen da ta bi.’

‘Kada ki damu ai lakanin da nasaba zai zo, ita kadai zai yi aiki a kanta. Ke dai ki turo min sunanta da na mahaifinta, idan da hali ma harda na kakanta kafin ranar Alhamis an gama aiki. In ya so sai ki aiko ko kizo ranar Juma’a ki karba. Ai tunda sun zo da fitna sai an tashi tsaye.’

‘Hakane Malam, in sha Allah zuwa gobe ma zan turo maka sunan nata. Sai kuma maganar abun sadaka ko?’

‘Ai kwarai kuwa, Zaki turo kamar naira dubu sittin don sai an sayi rago ma an yanka anyi sadaka da naman, idan aiki yayi sai ki cika dubu hamsin.’

Sukayi sallama tana ta yiwa Mallam godiya.

Tana ajiyewa ta kirawo Hajiya Amina ta bata labarin halin da ake ciki, ta sanar da ita akwai kudin da Abban yace zai bata idan ya bata zata rakata sayayya kuma ranar Juma’a zata rakata Gaya wajen Malam Hatimu. Sukayi sallama suka ajiye wayar.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

8

A zaune suke a garejin gidan Hajiya inda dama nan suka saba zama in ya zo zance, hirarsu suke cikin walwala. Ya dubeta sukayiwa juna murmushi, yace

‘Ni na ishi abokai da zancen zanyi aure amma ke ko ‘yar rawar kan nan da amare sukeyi ba kya yi.’

Ta kyalkyale da dariya

‘Kuma rawar kan me zanyi sai kace wata karamar yarinya?’

Ya kama haba

‘Wai ke ina zaki kai son girma ne? Har yanzu fa ashirin da ake kirga shekarunki.’

‘Kuma dai ni ba yariya bace ai.’

Yayi dariya

‘To yanzu dai me kika shirya a bikin, me kike bukata?’

‘Babu komai, duk na gama wani shiri.’

‘Kinyi shirin zama amaryar Yusuf?’

Tayi dariya, suka hada ido.

Tayi sauri ta sunkuyar da kai saboda yanda yake kallonta. Suka yi shiru ba tare da ta amsa ba, ya katse shirun

‘Sai fa kin bani amsa in ba haka ba sai dai muyi ta zama a nan.’

Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai, don haka shima yayi shiru ya zuba mata idanu. Ta dago suka hada ido ta kawar da kanta tana murmushi tana ta juya wayarta wadda take hannunta.

‘Aisha.’

Ya kirawo sunanta a hankali.

Ta dago ta kalleshi ba tare da ta amsa ba, yace

‘Kina so na kuwa Aisha.’

Ya sake zuba mata ido har tana jin motsin kwayar idonsa a kan fuskarta, kallon da yake mata ya sa ta tabbatar sai ta amsa tambayar. Ta bude baki a hankali tana murmushi tace

‘Um.’

Yayi dariya yace

‘Ban ji ba.’

Ta dago ido itama tana murmushi tace

‘Saboda tsokana ko?’

‘To kin shirya zama amaryar Yusuf?’

‘Na shirya.’

Yayi murmushin da yake nuna har cikin ransa ya ji dadin kalamanta.

Suka cigaba da hirar tasu duk da yawanci shiru sukeyi shi yayi ta kallonta ita kuma tayi ta satar kallonsa suna yiwa juna murmushi.

Shi Yusuf ba mutum ne mai yawan hayaniya ba ita ma kuma Aisha bata da surutu kuma ga miskilanci, don haka sai suyita kallon kallo suna musayar murmushi.
Jimawa kadan ya mike yace

‘Bari na tafi kada yayarki ta rufe min kofa.’

Tayi dare tace

‘Ashe dai ana tsoronmu.’

‘Ai dole ne, ku din hukuma ne sai lallashi.’

Ya fara tafiya suka jera zuwa waje don tayi masa rakiya, suna cikin tafiya ya bude wayarsa ya dubeta yace

‘Gaya min lambar account dinki mana na saka miki ko naira dari haka kya sayi goggoro.’

Tayi dariya, ta karanta masa account number din da sunan bankin.

Suna karasowa bakin motarsa taji wayarta tayi kara, tana dubawa ta bude baki tana kallonsa saboda sakon da ta gani. Ya gyara zamansa a mota yayinda tace

‘Yallabai kudin nan ai yayi yawa sai kace goggoron gwal zan siya?’

‘To ki saya harda janbaki.’

Tayi dariya

‘Nagode Allah ya kara arziki.’

‘Amin amaryar Yusuf.’

‘Ka bari dai a daura.’

Sukayi sallama ya kama hanya, yana tuki yana murmushi.

Kafin ya tambayeta maganar abinda take bukata wajen biki ya riga ya ya ke ko nawa ta nema iya dubu dari zai bata, amma sai ta ma ki yarda ayi zance. Shiyasa ya tura mata da dubu dari biyu, ko babu komai ta cancanci hakan don yana sonta sosai.

Dabi’unta suna burgeshi gata da kunya, shi kuma a rayuwarsa yana son mace mai kunya.

Yana tuki yana ta tunani har saida ya kusa zuwa gidan Suwaiba sannan ya tuna Zahra tayi masa message cewa ta koma gida, yayi murmushi ya karkata kan motar ya dau hanyar gida.
------

Haka aka cigaba da shirye shiryen biki; duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya ‘yan uwanta sun tsaya a kanta anyi. Duk da yaron cikin da Zahida take dauke da shi haka ta dinga rakata wajen gyaran jiki, suka je saloon aka rangada mata kitso a dogon gashinta. Duk lokacin da tayi kamar zata shiga damuwa sai su taru suyita lallabarta.

Su kuwa Abdallah da Farha murna ma sukeyi za ayi wa Mamansu biki, Abdallah ne kawai ya kan dan nuna damuwa idan yaji ana Mamansa wani gidan zata koma. Shima a hankali Hajiya ta dinga kwantar masa da hankali don haka kowa shirin biki kawai yakeyi a gidan.
Zuwa ranar Alhamis amarya ta dau kyalli, ranar Alhamis din da safe kannen Hajiya tare da matar Baffa suka hadu da su Zainab suka tafi kafi. Tsaf suka gyare gidan amarya suka kunna turaren wuta, gida ya dumame da kamshi. Ko ina yayi fes, dakuna uku da falo ga kitchen sannan kuma da fili inda za a iya ajiye mota daya.

Ba a ce dasu su shiga gidan Uwargida ba don haka ma da suka ji yunwa sai Zainab ta fita ta siyo musu abinci, suka ci suka karasa aikinsu suka koma gida.
……..
Chapter 10 · 0% Book details