← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 100

Sashe 95

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Yana nan, aiki mukeyi a dakin Mommy. Malam Liman ne yake jiransa a waje yace na shigo da shi, bari na kirawoshi sai nazo na kirawo Abban.'

Yaya Bello ya karasa shigewa falon yayinda Saddikun ya fice da sauri.

Jummai ta fito daga kicin da taji motsin Yaya Bellon, bayan ta gaisheshi tace

'Suna sama ma shi da su Hajiya Murja ne, bari na kawo maka ruwa.’

Kafin ya amsa ta koma kicin din.

Tana shigewa Saddiku suka shigo tare Malam Liman, bayan sun gaisa da Yaya Bellon Saddiku yace

'Cewa yayi ka hawo saman.’

'To bismillah.'

Ya bi bayansa.

Sadik din ya juya yacewa Yaya Bello

'Baba kazo muje saman Abban yana can.’

Ya mike gabobinsa babu kwari don ya zata wata lalura ce ta sami Abban wadda tasa ba zai iya saukowa ba zai ce a zo da mutum.

Suka bi bayan Saddiku suka haye saman.

Cirko-cirko suka tarar da su Abban a daki babu mai magana, yana ganin yayansa yace

'A'a! Yaya a ina ya samoka?’

'To na kasa nutsuwa ni din ma, sai waya nake maka baka dauka ba sai na zata wata matsalar ce a gidan.’

'Ta ba za a ce babu matsalar ba, ku karaso.’

Suka karasa ciki suka gaggaisa a tsattsaye. Abban ya nunawa Malam Liman robar wadda take ajiye a kasa da kuma kwan a kan murfin yayi masa bayani sannan kuma ya mika masa kwalbar fiya-fiya da ya jefe a aljihu. Suka tsuguna gaba daya Abban yana sake yi musu bayanin hayakin da ya fita daga cikin robar Liman yana dubawa.

Jimawa kadan yace

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’

Ya bi mutane dake dakin da kallo gaba daya sannan ya cewa Abban

'To ka san idan mutum ya mutu duk wata tashin-tashina barinta ake yi. Yanzu a nan waye bare wanda ba dan uwan ita marigayiya ba? Don ka ga idan da wanda ba zai rike mata sirri ba sai ya fita.’

Ya nuna su Yusra yace

'Wadannan dai yaranta ne ka san su, wannan yayana ne shi kadai gareni dan uwa, wadannan kuma yayarta ce da kanwarta uwa daya uba daya.’

Yaya Bello yace

'Bari na jiraku daga falo nan.’

Liman yace

'Ai ba ma sai ka fita ba ina ga duk nan amintattune, sai dai kawai zan bamu shawara duk abinda muka ji muka gani mu barshi a nan mu cigaba da yi mata addu'a.’

Duka suka amsa sannan yace

'Gaskiya wadannan abubuwan guda biyu da ka bani tsafi ne ko sihiri, hayakin da kuka ga ya fita ba zan yi mamaki ba idan aka ce aljani ne to amma ba zan sani ba tunda ban gani ba. Ko ma menene ya fitan bana jin zai tsaya nan kusa tunda kamar ya sami ‘yanci ne.’

Ya mikawa Abban karamin kyallen da ya zaro daga cikin kwalbar ya cigaba

'Ka ga wannan gutsure na na rigar wanda aka yiwa sihirin gashi nan. Sai a tattara wadannan tarkacen a kona sannan a binnesu tare da zancen, wadanda suka rigamu gidan gaskiya Allah ya yafe musu.’

Sukayi dif kamar ruwa ya cinyesu kowa da abinda yake tunani. Sai da Malam Liman ya gaji da shirun yace

'Kai Saddiku sai ka kwashi wannan ka kona ka binne shike nan a cigaba da addu'a.’

Abba yace

'Malam babu wata matsala idan an one din.’

'Babu wata matsala. Ai na riga na tofesu da ayoyin Allah kuma tunda me shi ta rasu ba zai yi tasiri ba. In ya so dai yara su karanta suratul bakara a gidan don a sami natsuwa gaba daya.’

Yayi musu sallama Abba da Yaya Bello suka bi bayansa don yi masa rakiya.

Suna fita Murja ta kalli Suwaiba tace

'Uhm! Ina ga sai mu tafi, ragowar kayan ma dawo. Ko kuma bari Abban ya dawo sai na tsaya mu kona wannan tarkace.’

Suwaiba tace

‘Allah ya kyauta.’
Suka fara hada kayansu don tafiya; gaba dayansu kowa zuciyarsa a jagule har Yusra wadda ta kasa magana. Nan falon saman suka zauna suna jiran Abban. Tunani kala-kala ne yake yawo a ran Yaya Murja; to yaushe Zahra ta fara tsafi? Ga shi ta mutu? Kuma ga dukkan alamu Abban take yiwa wanda gashi yanzu ya gani.

Haka suka zauna har Abban ya dawo saman suka yi masa sallama cike da jin nauyin abinda ‘yar uwarsu ta aikata suka fice cike da tsananin damuwa da mamaki. Godiya daya suke yiwa Allah da Liman yace kada a fita da zancen don haka ma suka fice ba tare da sun cewa Abban komai ba a kan zance.

Suna tafiya Abban ya koma dakin ya rufo kofa yayin da Yusra da Saddiku suka shige dakinsu.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

45

Su Yaya Murja suna fita daga gidan suka wuce gidanta don dama a nan zasu ajiye kayan da suka kwaso kafin su san abinda zasuyi da su. A dakinta suka zube a gajiye cike da damuwa. Kowa ya kasa magana saboda damuwa.

Jimawa kadan Suwaiba ta dubi Murja ta kirawo sunanta, sai dai kafin ta fadi abinda take son fada hawayen da take tarewa ya kwace. Itama Murjan ta kama share kwalla, sai da sukayi mai isarsu sannan Suwaiban ta goge fuska tace

'Yaya kin ga yanzu dole mu bar maganar Abban Saddiku ya auri Rahma, tunda na san mu kanmu kallonmu kawai yake yi. Wannan abun da Yaya Zahra tayi ai dole ya zata duka haka danginmu suke. Aishan kuma da muke kokarin mu kare yara daga fitnarta kinga ashe ba itace mai fitnar ba.’

Cikin tsananin damuwa tace

'Hmm! Suwaiba ai dole a bar wannan maganar tunda jiyan nan dama na yiwa Rahman maganar itama ta sakawa idonta toka tace ba zata aureshi ba kada ma mu soma maganar. Watakila ko ita ta san da wadannan abubuwan da Zahran take yi shi yasa taki shiga gidan.’

'Babu mamaki, amma dai ina mamakin yanda akayi Zahra ta zama haka. Kullum fa nusar da ita nakeyi yanzu dubi abubuwan da muka gani, da wanne ido zaka fuskanci ubangiji ka yi wannan aika-aikar?’

Nan suka dauki lokaci suna jimami da jajantawa, sai da aka fara kiran azahar sannan Suwaiba tayiwa Murja sallama ta tafi.

……..

Tunda Abba ya shiga dakin ya rufo kofa ya zauna a gefen gado ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa cikin damuwa. Tunani sun yiwa kwakwalwarsa yawa don haka bai ma san me yake tunani ba.

'Zahra.'

Ya kirawo sunanta a karo na babu iyaka cike da matsanancin mamaki.

To shi kuwa me yayi wa Zahra zata cutar da shi da Aisha? Me yayi zafi har ta barar da imaninta? To tun yaushe take wadannan abubuwan?

'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!’

Ya fada a fili yana goge fuska. So yake ma ya fitar da hawaye ko zai ji sanyi a ransa amma ko digon hawaye idonsa ya kasa fitarwa.

Lallai wadannan sune abubuwan da Aisha ta san ana yi mata har take jin ba zata zauna da Yusra ba. Yanzu haka Yusran ake turawa tana binne mata irin wadannan abubuwan shi ya sa tace ba zata zauna da ita ba; kuma bai ga laifinta ba a yanzu. Domin ko shine ya san halin Zahra to da tuni ya dade da rabuwa da ita.

Ya daga hannu sama kamar mai addu'a yace

'Allah ka hana yarana bin wannan hanyar da uwarsu ta bi, Allah ka shiryesu ka hana su shirka.’

Kwalla ta gangaro kan fuskarsa, ya sa hannunsa ya share.

Sai a lokacin ya samu ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro.

Yanzu wannan dabi'ar Zahra ta dora Yusra a kai? Lallai yana da aiki.
Zahra bata yi masa adalci ba, ta cutar da shi.

A take nadama ta rufe shi, bai taba nadamar auren Zahra ba kamar yanda yakeyi yanzu.

Yanzu ya zai yi da wannan matsalar?

Haka ya wuni a dakin yana ta tufka da warwara shi kadai, don ko masallaci bai fito ya je ba balle ya nemi abinci.

Yanda ya wuni cikin damuwa haka shima Saddikun ya wuni.

Itama Yusra haka ta wuni, sai dai ita damuwarta ba me yawa bace. A iya tsawon rayuwarta ta san kullum Mommy tana tsaye a kan nema musu kariya, wannan abubuwan da aka samu a dakin Mommy din ta san suna cikin wannan kariyar wanda Mommy din ta sanar da ita duk addu'oi ne don haka ita bata ma ga wani abun tashin hankali a ciki ba. Fatan ta daya Allah ya sa kada wata cutarwar ta samesu saboda wadannan abubuwan da aka kona.

—-----
Yana dakin har bayan karfe uku, sai wajen la'asar yunwa ta dameshi. Yana fitowa ya hango abincinsa a kan dining table don haka ya zauna ya ci. Yanda yaji gidan shiru ya san yaran sun tafi makaranta don haka yana gamawa ya sauko ya sami Jummai a tsakar gida ya tambayeta in Saddiku, ta sanar da shi Saddikun yace mata ya fita amma kafin magriba zai dawo. Yayi mata sallama ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.

Ya san sai dare ya kamata suje gidan su Aisha, to amma zaman dakin ya isheshi. Gara ya bi Yayan gidan su tattauna ko ya samu zuciyarsa tayi sanyi.

Tun a farkon layin ya hangi Yaya Bello yana tsaye da ‘yan unguwa, yana wucewa shima Yayan yayi musu sallama yabi bayansa.
Yana yin parking Yayan ya karaso suka hadu, bayan sun gaisa suka wuce cikin gidan. Yaran da Ummansu duka basa nan sun tafi biki sai Muhammad kadai, bayan ya kawowa Abban ruwa ya koma dakinsa.

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Abban ya ajiye kofin ruwan da yake hannunsa yace

'Na kasa nutsuwa Yaya, ace ina zaune da mace shekaru masu yawa kowa yana kyautata mata zato ashe matsafiya ce ban sani ba?’

Yayi gyaran murya

'Gaskiya dai nima har yanzu ina mamaki; don ka ga da ace a lokacin tana raye an ce ka zabi daya ko ita ko Aisha to tabbas na san da mu da duk wani danginka zamu ce ka rabu da Aisha ka dauki Zahra, ashe itace bara-gurbin.’

Ya jijjiga kai
Chapter 95 · 0% Book details