← Book details Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 100

Sashe 88

Uwar Sadiku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta share hawaye ta bi bayansa da kallo; ta riga ta san daman ba zai fahimceta ba saboda yanzu abu daya yake so a kular masa da yaran ya koma harkokinsa. Itama zata so ace ta kular masa dasu amma bata shirya fada da Yusra ba don bata hango abun zai yi kyau ba.

Sai da ta gaji da share hawaye sannan ta tashi ta rufe gidan ta wuce daki inda tayi alwala ta kabbara Sallah domin ta san Allah ne kawai ya san halin da zuciyarta take ciki a yanzun.

UWAR SADDIKU

Written by

Sakina Yazid
(Innar su Amal)

42

Tana sane da cewa Goggo Binta zata tafi don haka gari yana wayewa bayan ta gama shirin tafiya aiki ta zubo sandwich din da ta yiwa yara a roba ta dauko abinda zata bawa Goggo ta nufi gidan.

A falon kasa ta samesu duka suna karyawa. Da gudu Sumayya tayi mata oyoyo ta fara surutu, Saddiku da yake zaune a dining table ya juyo ya gaisheta. Ta karasa ta zauna a kusa da Goggo a dai-dai lokacin da Yusra ta mike ta shige kichin. Cikin girmamawa suka gaisa da Goggo da sauran yaran, ta mikawa Rukayya robar sandwich din tana fadin

'Ga abincin break dinku Rukayya.'

Ta mikawa Goggo daya robar. Rukayya ta dauki robar ta shige kicin. A daidai lokacin Goggo ta dubeta tace

'To nifa yau bako zai yi halinsa, sai dai nace Allah yaji kan wannan yarinyar. Wadannan yaran kuma dama tare na ganku sai dai nace Allah ya zaunar daku lafiya.’

Tace

'Amin Goggo, mun gode.’

'Abban yace min yau zaki dawo dakinki ko?’

Cikin sanyin murya tace

'Eh, sai na dawo daga aiki.’

'To a dawo lafiya. Ni dai nan da awa daya ma na tafi in sha Allah.'

‘'To Goggo mun gode, Allah ya kara lafiya.’

Ta kawo kudi naira dubu goma ta ajiyewa Goggo tana fadin

'Kya yi tsaraba a hanya Goggo, a gaida mutanen gidan.

Nan da nan Goggo ta fara godiya tana saka mata albarka. Ta mike ta nufi kofa bayan tayiwa yaran sallama tana tuna musu gara su fito kada su makara.

Ta kofar kicin Yusra ta fita tsakar gida don haka babu wanda ya san tana waje. Dai-dai lokacin da Aishan ta kusa karasawa bakin kofar dai-dai lokacin Yusra ta shigo falon. Iya karfinta ta bangaji Aisha da kafada har saida Aishan ta danyi baya. Ta kalleta sama da kasa ta wuce. Cikin sanyin jiki itama ta fice daga falon, ta tsaya a bakin gata ta hadiye malolon bakin cikin da ya tokare mata makogoro ta share kwallar takaicin da ta gangaro daga idonta; ya ma za ayi ta zauna da Yusra?

Babu wanda ya ga abinda ya faru sai Saddiku wanda yake kan dining table. Ya jijjiga kai ya cigaba da cin abincinsa, yana mamakin yanda Yusra ta zama marar kunya domin shi kansa ba kyale shi tayi ba tun lokacin da ya dawo daga makaranta.

Kafin Aishan ta fice daga gate din Abba ya sauko daga sama ya yiwa yaran magana su fita a kai su makaranta. Bayan sun fice ya gaisa da Goggo yana tambayarta ita da wa ya jiyo hirarsu. Tace

'Ni da diyata ne Aisha, ka ga abun arzikin ma da ta kawo min.’

Ta nuna masa kudin da Aishan ta bata sannan ta cigaba

'Tace idan ta dawo daga aiki ai zata dawo dakinta. Sai ayi ta hakuri, Allah ya ji kan mahaifiyarsu kuma Allah ya baku hakurin rashi gaba daya.’

Ya amsa sannan ya mike ya koma sama.

Wannan maganar da Goggo ta sanar da shi ta kara masa nutsuwa, duk da daman ya san Aisha ba zata ki bin umarninsa ba. Sai da ya jira Goggo ta shiga mota Malam Ali ya ja su ita da Saddiku sannan shima yayiwa Jummai sallama bayan ya sanar da ita ta sake share dakin da aka gyarawa Aisha sannan ya fice.

—------

Haka Aisha ta wuni a wajen aiki zuciyarta babu dadi, duk wanda ya kalleta sai ya tambaya ko bata da lafiya. Abu daya take jaddadawa kanta shine ba zata zauna da Yusra ba, idan Abba ya matsa mata tabbas zata iya hakura da aurensa.

Ana tashi daga aikin ta kama hanya ta koma gidanta, bata da niyyar barin gidan don haka ta cigaba da harkokinta kamar yanda ta saba.

Wajen karfe uku lokacin da su Rukayya zasu tafi islamiyya ta ja Ummi da Sumayya suka shiga gidan Aishan. A take Nana ta koma gida ta gayawa Yusra wadda tayi alkawarin idan suka dawo sai ta koyawa Rukayya hankali don ba zata barta ta dinga karya dokar Mommy ba ko da bayan ran Mommy din ne.

Suna shiga bayan sun gaisheta Rukayya tace

'Anti Abba yace yau zaki dawo gidanmu fa ko an fasa ne?’

Ta kalleta tana murmushi, bata san amsar da zata bata ba don haka tace

'Ba'a fasa ba amma zan dan fita tukunna sai dai kafin ku dawo na dawo.’

'To Anti.'

Ta aika Rukayya kicin ta dauko musu biskit ta bawa Ummi da Sumayya suka yi mata sallama a kan idan sun dawo zasu sameta a gidansu suka fice.
Ta bi bayansu da kallo cike tsananin damuwa; da ace su ukun nan ne kadai yaran Abba tabbas da tuni wani zancen ake ba wannan ba musamman yanda ta kula shima Saddiku tunda ya dawo daga makaranta cikin girmamawa yake mu'amala da ita.

Suna fita ta kirawo Zahida ta sanar da ita yanda sukayi da Abban. Zahida tace

‘'To yanzu ya za ayi? Kinga fa ko Hajiya ba a gayawa halin da ake ciki ba.’

'Hmn! Da na gaya mata da yanzu ta tursasa ni na koma gidan ni kuma wallahi ba zan yi wannan rayuwar ba. In ya dawo kawai ya daga min hankalin gidan zan tafi sai ayi ta ta kare don ba zan zauna da wannan yarinyar ba. Ko yau ma baki ga wulakancin da tayi min ba da na shiga gidan, Ina kuma ga a ce kullum ina tare da ita.’

Cikin damuwa Zahidan tace

'Allah ya sauwake amma dai akwai kura, ba kadan ba.’

Sukayi sallama suka ajiye waya.

……….

Wajen karfe biyar Abba ya dawo daga aiki, gaba daya ya sakankance cewa zai tarar da Aisha a gidan. Yana shiga falon bayan ya amsa sannu da zuwan Yusra wadda ya tarar a falon kasan tana kallon TV ya karasa ya bude kofar dakin da aka gyarawa Aishan. Ga mamakinsa babu komai a dakin, ya janyo kofar ya juyo ya cewa Yusra

'Antinki bata dawo bane?’

'Eh, babu wanda ya zo.’

Bai amsa ba ya haye saman zuciyarsa tana dugunzuma. Me yasa Aisha take son ta saba umarninsa? Me take nufi da hakan? Idan bata rike masa yaran ba meye amfanin ta a rayuwarsa a daidai wannan lokacin? Bai taba zaton zai dawo ya tarar bata gidan ba amma gashi saboda raini bata dawo ba.

Jakarsa kawai ya ajiye a dakin ya fito ya wuce gidan Aishan.

Tana zaune a falo a kan kujerar zaman mutum daya tana ta faman dube-dube a waya. Bata ji alamar ya yi sallama ba don haka bata amsa ba, ta mike tsaye ta ajiye wayar ta nufo shi tana yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya tsaya daga bayan kujerar yana mata wani kallo na takaici, ta karasa ta tsaya daga kusa da shi tana fadin

'Ga ab…’

Muryarshi ce ta katseta

'Aisha me nace miki? Me kike a gidan nan bayan ga inda nace ki koma kafin na dawo zaki bar min yara su kadai, zaman kansu zasu yi kenan saboda mahaifiyarsu ta rasu ko me?’

Ta sunkuyar da kai ta share kwalla a hankali tace

'Kayi hakuri ai na gaya maka ba zan iya komawa ba.’

A fusace ya nuna ta

'Idan dai zamana kike to yanzu ba tare da bata lokaci ba ki fito ki koma can gidan idan ba haka ba kuma to zaman kanki kike yi. Mun gama magana da maigidan nan next week zasu karbi mukullinsu idan kuma zaki kama hayar sai kiyi magana da su ki kama hayar tunda kin fi karfina.’

Ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita yana mata kallo mai cike da takaici, ya fice ya mako mata kofar.

Yana fita ta zagaya ta zauna a kan kujerar ta sa kuka. Ita kanta bata san kukan me takeyi ba tunda dama ta sa ran hakan zata faru. Sai da tayi mai isarta sannan ta share hawayenta, ta dubi agogon bangon da yake dakin taga karfe shida saura minti biyar. To zaman me takeyi a gidan mutane tunda ya gaya mata gida ya fita daga hannunsa kuma idan ta zauna zaman kanta takeyi. Ta mike a hankali ta shige dakinta.

Kafin magriba ta tattara kayanta na bukata da kuma duk wasu kaya masu mahimmanci wadanda motarta zata iya dauka. Ta fito ta zuba a motarta, ana kiran Magriba ta rufe gidan ta ja motarta ta nufi gidan Hajiya.

—-------

Abba yana fitowa daga gidan Aisha ya koma gida, kai tsaye dakinsa ya shige ya rufo kofa. Ya zauna a gefen gadonsa kamar wanda aka tunkuda, ya hada tafukan hannunsa guda biyun ya zuba fuskarsa a ciki yana fitar da wani huci na takaici; bai taba tsammanin taurin kan Aisha ya kai haka ba. To me Yusra tayi mata da zata ce ba zata zauna da ita ba? Ita Yusran ya zai yi da ita kenan? Babu yanda za ayi ace a rayuwarsa yanzu ya kara aure don wannan ba zai ma yiwu ba. Iya tsawon rayuwarsa abinda ya sani shine idan aka saki mace ko ta rasu to idan dai tana da abokiyar zama yaran wajen abokiyar zaman suke komawa ba tare ma da anyi wata magana ba.
Ita Aishan me yasa take jin cewa tana da zabi? Me Yusra tayi mata da har take jin a cikin yaran zata rike wasu wasu kuma ba zata zauna da su ba? Tabbas ya san da sa hannun Zahra a lokacin da ya manta da Aisha na wani lokaci to amma menene laifin Yusra a ciki?
Chapter 88 · 0% Book details