← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 73

Sashe 9

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Driven da aka kirawo da Joseph cikin ruɗe wa da tsawar da ogan shi yayi mishi yace cikin rawar murya "sorr.........sorry boss fitsari ne ya matseni na kasa rik'e shi sauran Kad'an ya xubo"

Wani wawan tsaki yaja wanda ya kad'a hanjin cikin Joseph sosai har jikin shi ya d'auki rawa Kafin ya tashi xaune yasa hannu ya murɗe kunnen Joseph da k'arfin wata er k'ara ya saki na axaba Kafin yace

"ahhhhh boss I'm so sorry fitsarin sauran Kad'an ya xubo na rantse boss"

Sakin kunnen shi yayi Joseph ya saki wata ajiyar xuciya har yanxu kafarshi tana matse saboda yana kwakwkwaran motsi xai xubo sai da ya gama jan ajin shi Kafin yace "get out na baka 30seconds sauran ka tsaya shirmen ka"

Ae Kafin ya rufe bakin shi tuni Joseph ya fice daga motar da gudu ya K'arasa gefen titi cikin wasu ciyayo ya fara fitsarin yana sauri don kada ya shige time d'in da Oga ya bashi

Ajiyar xuciya ya sauke ta jin dad'i saboda gama fitsarin da yayi don ya matse shi sosai tun basu dad'e da baro Abuja ba yake jin shi tsoro ya hana shi tsaya wa sai yanxu da yaga baxai iya jira har su je kano ba......

Idon shi yake kusa da kafar shi sai yaga wani bak'in abu wuluk dashi ai baisan lokacin da xuba ihu ba kamar ba soja ba yana cewa "ohhh my god Shikenan xan mutu Oga help me please!!! "

*Aishat A muh'd {Aunty }*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*NA*

*Aishat A muh'd {Aunty }*😘

*~pg 15~*

K'arar da Joseph yayi tasa Abduljabbar fito wa daga cikin motar sai tsaki yake ja dai2 inda yaji ihun Joseph ya nufa cikin tsawa yace "ihun mai kake duk ka cikawa mutane kunne taimakon uban mai xan maka?"

Cikin Joseph na makyarkyata ya nuna mishi bakin abun da yake kusa da kafar shi kallo d'aya Abduljabbar ya fahimci komai ne wani wawan tsaki ya sake ja Kafin yace a fusace

"lalle na yarda kai mahaukaci ne Joseph sake kallon abun ka gani "

Cike da tsoro ya sake kallon wajen sai yaga ashe wata black d'in jaka ce amman duk da hka bai sake ba coz yana tunanin ko wani abun ne aciki

"d'auko min bag d'in nan ka bud'e cikin ta"

Ae da ace kunga yanda Joseph ya koma da idan kuka fara dariya sai cikin ku yayi ciwo don ko shi Abduljabbar d'in sai da ya dariya ta kusa ta kufce mishi amman ya dake don bai d'auko jakar ba sai da ya daɗa mai2 ta mishi maganar Joseph a firgice yace

"I beg you boss ina tsoro kada bom ne a ciki"

Zaro ido abduljabbar yayi kafin kuma ya sake d'aure fuska yace "ai komai ne sai ka dauko min na gani idan bom d'in ne sai ya tashi da mu daman aikin mu ai na taimakon al'umma ne"

Jin abin da boss yace yasa Joseph sake rikice wa don yasan kaifi ɗaya don hka jikin na ɓari yake hannu xae ɗauka amman tuni har abduljabbar yasa hannun shi ya dauko jakar tare da bugawa Joseph jakar a bayan shi a tsorace yayi wani irin wawan tsalle ya kwasa da gudu bai ja birki a ko'ina ba sai cikin mota ya xauna yana faman sauke numfashi shi kuwa abduljabbar tsaya wa yayi yana kallon shi don yayi bala'in bashi dariya ba kaɗan ba don sai da ya murmusa kafin ya buɗe jakar don ganin abin da yake ci

Da laptop yaci Karo sai wasu takardu tsaf ya duba bai ga wani abin tashin hankali ba mybe wani ne ya yar dashi abin da xuciyar shi ta sanar dashi taɓe baki yayi Kafin ya mayar da komai har xai ajiye jakar ɗin sai kawai yaji yana sha'awar tafiya da ita don hka ɗaukar ta yayi ya dawo inda suka yi parking ya buɗe mota ya shiga sannan ya Kalli joseph yace

"matsoraci oya sai mu tafi "

Baice komai ba yayi wa motar key suka ɗauki hanyar kano.....
...

Sun shigo cikin garin kano dare yayi sosai gidan shi dake nassarawa GRA Joseph ya danna hon mai gadi sai da ya buɗe wata K'aramar kofa ya duba ya tabbatar maigidan ne sannan ya bud'e get saboda tsaro Joseph ya shigo da motar sannan ya mayar da get ya rufe ya K'arasa inda Joseph yayi parking yana yiwa abduljabbar sannu da xuwa ya amsa Kafin yayi cikin gida

Wow masha Allah lokacin da na tsaya kallon gida a gasky gidan ya had'u ba kaɗan ba xubin gidan irin xubin gidajen k'asar los angles ta k'asar american sai da ya tsaya ya danna door bell tukunna yakai tsayin 15seconds Kafin er aikin gidan taxo ta bud'e Sannu da xuwa tayi mishi kafin dakyar ya iya buɗe baki ya amsa da yawwa ya shige xuwa main falon wow sakin baki nayi ina kallon k'ayataccen falon wanda colour d'in shi ash da yellow ne bakaramin had'u wa yayi ba

Upstairs na gani ya hau wanda yake a tsakiyar falon sai da ya shige falo 2 kowanne da irin haduwar shi kafin ya isa ainahin bedroom d'in madam d'in shi tana kwance a katafaren gadon ta k'irar italyn bed tana faman bacci hankalin ta kwance

Wani wawan tsaki yaja cike da jin haushin jiddah bcoz ya sanar da ita komai dare xai shigo kano kada tayi bacci saboda a buk'ace yake da ita a nutse ya isa gadon ya d'ora kafar shi d'aya akan gadon d'ayar tana k'asa kafin yasa hannu yana bubbuga pillown da kanta yake cikin ɓacin rai ta bud'e idon ta xaune ta tashi ba Sannu da xuwa ba irin tattalin mijin nan bakomai kawai cewa tayi

"sai yanxu kuka dawo maimakon ka kyale ni nayi bacci na gobe ma had'u da safe sai ka fara tashi na cikin tsohon daren nan"

Harara ya watsa mata kafin yace "na baki 10mint ki haɗo min coffee yanxu ki kawo min"

Yana gama fad'in hka ya fice daga bedroom d'in nata ya nufi nashi ai sai naga d'akin duk haduwar shi sai naga bakomai bane idan aka had'a shi da haduwar d'akin abduljabbar kayan jikin shi ya fara cirewa kafin ya d'aura towel Ya nufi toilet d'in shi dake manne a jikin bedroom d'in

Ita kuwa jiddah haushi ne ya isheta Shikenan mutum baxai huta ba da xarar ya dawo sai aiki shi komai dare gani yake kamar rana ce mtssss taja tsaki tare da hararar kofar da fita kamar shine a wajen yanxu xai ishi mutum da jaraba sai da ta dau tsayin 5mint kafin dakyar ta tashi ta fito falo da yake akwai kitchen a saman nan ta shiga ta haɗo mishi coffee a wani k'aramin tray d'akin shi ta nufa ko sallama babu ta tura kai ta shiga a dai2 lokacin ya fito daga toilet agogo ya duba a kalla sai da ta Kara wajen 6mint akan time din da ya bata ko kulata bai yi ba ya K'arasa gaban dressing mirror ya gyara jikin shi tare da fesa body spray a jikin shi Kafin ya xauna a bakin bed ya d'ago kai tare da watsowa jiddah wani kallo wanda har sai da ta d'an tsorata ganin idon shi yayi ja table d'in da ta ɗora coffee d'in ta tura mishi gaban shi bai mata magana ba da kanshi ya xuba saboda sam jiddah bata iya kula da miji ba kawai abin da ta iya daga chatting a waya sai kallon tsiya da shegen son jikin jaraba k'wata2 kula da miji bata iya ba tana tsaye a gaban shi har ya gama shan coffee d'in sai faman hamma take na barci

Da karfi yasa hannun shi ya fisgo ta jikin shi wanda har sai da ta d'an yi er k'ara saboda ta tsorata hannu yasa yayi switch off din hasken dakin nan ya shiga sarrafa ta cikin gwanan ta tun tana k'in sakin jikin ta har ta bada kai bori ya hau don Abduljabbar ba baya bane wajen sarrafa mace da saka ta cikin nishadi don namiji shi cikakken ma kuwa don duk lokacin da jiddah taxo hannun shi sai tayi kuka da idon ta saboda ba k'aramin wahala take sha ba tun da sai ta ga dama take bashi hakk'in shi, shi yasa duk lokacin da taxo hannu yana sani yake bata wahala........

Wannan daren k'wata2 bai bar jiddah ta runtsa ba tayi kukan tayi magiyar amman duk a banxa bai rabu da ita ba sai da aka kirawo sallahr asuba tukunna ya fad'a toilet yayi wanka tare da d'aura alwala sannan ya fito sai da yayi raka'atul fijir sannan ya nufi masallacin dake jikin gidan shi wanda had'e yake da gidan shi don shi ya gina shi

Jiddah kuwa kasa tashi tayi don wani shegen wahalalen bacci ne yayi awon gaba da ita, sai 6 na safe abduljabbar ya dawo gidan ya tarar tana bacci don baiga alamun ko sallah tayi ba don hka ruwan sanyin dake hannun ya d'an xubo a hannun shi ya yarfa mata a fuska da sauri ta tashi xumbur a tsorace tana sakin ajiyar xuciya don ruwan da sanyi ai baisan sanda ya tuntsire da dariyar mugunta ba haushi ya kama jiddah sosai harara ta watsa mishi kafin hawaye ya biyo baya tace

"wannan ai mugunta ce don Allah ka gama wahalar dani sannan kaxo ka watsa min ruwan sanyi kana min dariya "

Gimtse dariya shi yayi Kafin ya kamo ta yana rarrashin ta da hka ya lalla6a ta ta shige toilet ....

*Aishat A muh'd {Aunty }*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*Na*

*Aishat A muh'd {Aunty }*😘

*~pg 16~*

*WANE CAPTAIN ABDULJABBAR*

Captain abduljabbar d'an gidan Alhj ibraheem ɗanbatta ne don mahaifin shi d'an asalin garin d'anbatta ne dake garin kano su 3 awajen mahaifan su ibraheem shine babba sai mace khadijah da k'aramin su Abdulkareem shine sa'an abduljabbar sun bawa ya'yan su ilimin addini dana xamani,ibraheem bayan ya kammala makaranta shi ya samu aiki a makarantar BUK anan yake lecturing d'an boko ne na k'in k'arawa
Chapter 9 · 0% Book details