← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 73

Sashe 66

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah ka daina xubar da hawayen ka please "
"baxan dai na Idan har baki hak'ura ba"
Ya fad'i hkan yana sake rik'o hannun ta gam a cikin hannun shi a hankali ta fara cewa
"na hak'ura Yah abduljabbar daman ae d'an ajixine, ni tun tuni na yafe maka amman ina son gaba kada dunga bincike Kafin ka yanke hukunci "

Cikin tsananin farinciki yace "nauwara da gaske kin hak'ura? "
Cikin jin tausayin yanda duk yabi ya rud'e cikin tabbatar wa tace "da gaske nake Allah ya yafe mana gaba d'aya "
Da sauri ya rungume ta tsam a jikin shi tare da cewa "Ameeen thank u habibty nah, kuma Insha Allah xan kiyaye gaba "
Ya cigaba da cewa "i luv u baby nah i really miss u "
Duk gaba d'aya ya rikice mata da godiya a hankali ta lumshe idon ta hawaye suna xuba a idon ta wanda bata san name ne ba na farinciki ne ko akasin hka, had'a fuskar shi da ta ta xai yi yaga hawaye a fuskar ta a rikice yace "baby nah bakya so na rabu da ke? " shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa shi cikata tare mik'e tsaye cikin sanyin jiki ya juya xai fita daga d'akin ganin hka yasa ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta rungume shi ta baya tare da fashe wa da kuka runtse idon shi baya son kukan ta ko Kad'an a hankali ya juya tare da rik'e mata kafad'un ta yace
"calm down nauwara what wrong with u? "
Kasa magana tayi don kuka yaci k'arfin ta hankalin shi gaba d'aya ya tashi xauna wa yayi kan sofa tare da xaunar da ita kan kafafun shi nan ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru sai ajiyar xuciya da take saki akai akai duk fuskar ta tayi ja idanun ta sun kumbura ita kanta batasan dalilin kukan nata ba ganin tayi shiru yasa shi cewa

"what happened to u nauwara, me yasa ki kuka haka? "
"ni kawai haka naji kukan yaxo min "
"ohhh my god nasan Akwai wani abun fad'a min kinji my dear "

Cikin sanyin murya tace "da gaske nake yi fah"
D'an xaro ido yayi Kad'an ya kama kumatun ta duk biyun yace "shine kika d'aga min hankali, are you sure babu wani abin ?"

Jijjiga kai tayi ba tai magana ba d'an siririn murmishi ya saki tare da cewa "thank u once again i luv u baby nah Allah yayi miki albarka "

A hankali ta bud'e d'an k'aramin bakin ta tace "Ameeen "
Bata peck yayi a kumatu da goshi sannan kan lips d'in ta sannan ya bar d'akin, xuciyar shi wasai cike da farin ciki sai faman murmishi yake bai damu da tattare war da shaddar jikin shi yayi ba sai dariya ake mishi wasu na tsokanar shi sai dai ya shafa gashin kanshi tare da Murmishi ko uhm bai ce ba har ya fice daga part d'in umma ya nufi nashi.

Ita kuwa nauwara kwanciya tayi akan sofa tare da rungume pillow a kirjin ta wani sabon son abduljabbar ne yake dad'a shiga xuciyar ta yanxu wasai take jin xuciyar ta.

Da yammaci aka gabatar da Mother's Day bayan sallahr mangariba kuma aka mik'a kowacce gidan mijin ta banda nauwara daga FA'iza sai jiddah sun sha kuka sosai tsakanin FA'iza da nauwara xasu yi kewar junan su don ba k'aramin shakuwa suka yi ba hka twins sun sha kuka su ma,

Dakyar fa'iza ta cika nauwara suka tafi gida jikin nauwara a sanyaye, suna k'arasa wa gida wanka ta iya yi tabi lafiyar gado don ba k'aramin gajiya tayi ba nan da nan bacci yayi awon gaba da.......

Aishat A muh'd

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

_dedicated to khalfana (sister d'in neena cool), muna godiya sosae Allah ya bar xumunci, ina miki fatan alkhairi_❣😍

*~Pg 95~*

Tana xaune a dinning area tana breakfast duk yau tashi tayi jikin ta a sanyaye saboda yau ammin ta da inna, aunty safiyya xasu koma kaduna jin tayi an rufe mata idanun ta k'amshin turaren shi kad'ai taji ta gane ko wane cikin mak'e murya yace
"canki wane?"
tana murmishi tace
"Haba kasan na gane ka kawai ka bud'e min ido "
Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yayi cike da k'aunar ta ya bud'e mata idon tare da janyo kujera ya xauna a kusa da ita yana kallon ta ita ma shi take kallo sun sauke en mintuna suna kallon junan Kafin nauwara ta fara janye idonta tana cewa
"dafatan ka tashi lafia? "
D'an ta6e baki yayi tare da cewa "ehhh to lafia ba lafia ba? "

D'an xaro ido tayi cike da mamaki tace "Idan ba lafia ka tashi ba to yana ganka qlau da kai??"

"Idan kin ga gangar jikina lafia to nan "
Ya dafe xuciyar shi ya cigaba da cewa "ba lafia yake ba yana cike da son ki da kaunar ki ta Kasa samun nutsuwa Har sai ta ji d'umin mahad'ar ta "
Ya gama fad'a yana kashe mata ido hararar shi tayi shi kuwa ya wani marairaice fuska sosai ya bata dariya ganin yanda ya wani langa6e kai kamar k'aramin yaro ganin har yanxu ta kasa sakin jiki dashi ba kamar da ba kuma yasan sai a hankali gashi kuma cike da wata iriyar sha'awar ta yake d'aure wa kawai yake yi, don baya son ya matsa mata yafi son ya gama goge laifin shi gaba d'aya a gurin ta .

"na had'a maka tea ne? ", girgixa kai yayi cikin kalar tausayi yace " Idan da ni kike to a koshe nake, umma ta aiko min da shi yanxu ma da kika ganni abuja xan tafi ana nema na"

Cikin d'an mamaki tace "daga xuwan xaka koma?"

"toh ya xanyi tunda yanayin aikin namu kenan, da dai ni d'an gata ne da sai ki shirya mu tafi tare"
Da sauri ta girgixa kai tana cewa "a'a ni ina kusa da umma "
D'an murmishi yayi yana shafa sajen shi yace "ba wani nan kema nasan kina son ki ganki kusa da mijin ki kawai irin kawaicin nan ne irin na mata ko ba hka ba? "
Ya tambaye ta yana d'aga gira haushi ya rufe nauwara don ta gane abin da yake nufi hararar shi tayi tare da mik'e wa da sauri ta bar wurin bin ta yayi da kallo Kafin ya dunkule hannun shi ya daki table d'in yana cewa

"ohhh my god na kwafsa ashe Hka na saki baki ina magana gashi nan garin gyaran gira........ "
Da sauri ya mik'e tsaye ganin sauran 30 mint jirgin da xai bi xuwa abuja ya tashi don hka Agurguje yayi sallama da en gidan ya tafi ko gimbiyar tashi bai samu ganin ta ba.

Sai wurin 12 su ammi suka tafi umma sai godiya take musu ita kawai hka taji tana bala'in son ammi nan aka rabu cike da kewar juna.

Tun da ya tafi abuja kullum abduljabbar cikin waya yake yiwa nauwara ban da text mssg di'n shi na ta taimaka ta yi picking d'in wayar shi dakyar da yarda take d'aukan wayar tashi tun tana k'in yin magana har yakai da ta saki jiki suna d'an ta6a hira hkan ba k'aramin jin dad'i yayi ba, na'eem da ameer ma sai dad'a girma ake suna ta xuwa skul d'in islamia da boko ga nauwara da saleem suna yi musu lesson a gida baki ya dad'a bud'e yanxu ai ta xuba surutu ga wayo.

Saleem ma yanxu kok'arin had'a degree di'n shi yake an fara xama babban mutum ba ruwan shi akwai nutsuwa da hankali, bai fiye fita irin yawo nan ba daga makarantar boko sai islamia don ya dage da neman ilimi addini sosai, idan ya dawo xaka same shi yana yiwa twins lesson ko ki ganshi a kitchen ya xage yana taya umma ko nauwara girki suyi tayi mishi dariya amman shi ko ajikin shi kawai girki yana burge shi, kullum nauwara gode wa Allah take da yayi musu wannan gatan na dace da en rik'o na gari, gashi saleem kamar su d'aya da abban su har dariyar shi da murmishi shi yasa take yawan kallon shi kallon shi da take yana tuna mata da abban su wani lokacin har tambayar ta yake lafia irin wannan kallon sai dai kawai ta girgixa kai tare da yin murmishin yak'e tace ba komai.

Sai da abduljabbar yayi wajen 4 weeks bai xo kano ba sai da waya saboda tarin ayyukan da ke gaban shi gashi gaba d'aya a tak'ure yake d'aure wa kawai yake ana hka ya d'an samu sararin aikin yana shirye shiryen tahowa, wani aiki ya ttaso mishi dole ya hak'ura da xuwan ya tafi duk haushin aikin ya ishe shi kamar xai yi kuka a lokacin hka yaji aikin da ya d'auke shi wajen 1 month again.

Da sauri ta fito daga toilet jin k'arar wayar ta tana d'aure da towel ajikin ta ganin abduljabbar ne me kira yasa ta d'auka tare da yin sallama amsa wa yayi duk suka yi shiru lokaci d'aya Kafin daga can abduljabbar yace

"habibty nah nayi missing di'n ki sosai don hka ki shirya tar6ar mijin ki ranar Friday nan da k'wana 2 kenan "

Ji tayi gaban ya fad'i jin irin muryar da yayi amfani da ita wajen maganar tayi shiru don ta rasa mai xata ce

"ya kika yi shiru ko baki farinciki da xuwan nawa ba "
"hmm ni na isa nace haka, Allah ya dawo da kai lafia "
"Ameeen habibty, ina twins d'ina? "
"suna parlour wajen umma "
"Yayi kyau, ina son don Allah ki je part d'ina da kanki nake son ki gyara min please "
Shiru ta d'an yi Kafin tace "okay ba matsala xan yi yanda kace "
"that's my girl, ngde sosae Allah yayi miki albarka "
"Ameeen "

Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunanin abin da ya kamata tayi mishi wanda xai ji dad'i nan ta xurfafa a tunani...........

Aishat A muh'd.

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 96~*
Chapter 66 · 0% Book details