← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 73

Sashe 57

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da yaji lokacin da xai shiga d'akin jiddah waya take da farida kawar ta tana cewa
" ni fah har yanxu buri na bai cika ba tunda bai sake shegiyar yarinyar nan ba duk da sharrin da muka had'a mata na tura wani d'akin ta matsayin d'an iskan da suke watse wa Wlh na d'auka lokaci d'aya xai dankara mata saki har uku gashi har ta haifa mishi twins ina tsoron ya dawo da ita gidan nan na tsani er iskar yarinyar nan "
Abin da yaji kenan ya banko kofar da k'arfi har jiddah ta tsorata a firgice ta mik'e tsaye ganin yanda ya koma lokaci d'aya ita bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba amman ta maxe tace
"sojana xuwan yaus........ "
Kafin ta K'arasa fad'in "yaushe" ya kwashe ta da wani mugun mari Kafin ta dawo hayyacin ta ya sake bata wani daga nan ya fara ball da ita da kafar shi tana ihun kuka tare da bashi hak'uri belt d'in jikin shi ya cire ya fara tafkar ta son ran shi yana cewa
"jiddah kin cuce ni kin raba ni da nauwara daman sharri kika k'ulla mata xaki yi bayani duk abin da kike min ban ta6a d'aukar mataki ba a kanki amman wannan Karon xan baki mamaki wallahi"
Sai da yayi mata lilis ko motsi bata iya yi balle kuka sai faman ajiyar xuciya take saki tsugunna wa yayi dai dai kan ta yace
"na tsane ki jiddah kin raba ni da sanyin idaniya ta muradin rai na kije kema na sake ki baxan iya xama da ke ba"
Wani irin ihu ta saki Duk da muryar ta bata fita sosai bai kula ta ba ya janyo ta tun daga upstairs har k'asa xuwa farfajiyar gidan ya watsa ta a bayan mota sannan ya kirawo Joseph ya fad'a mishi ya kai jiddah gidan su sannan ya wuce cikin gidan xuciyar shi kamar xata tarwatse saboda yanda take bugu yana shiga cikin d'akin shi ya fara jifa da komai na d'akin yana fasa su tuni d'akin yayi kaca kaca duk ya yanke a hannun shi fuskar shi ta yi jawur da ita hannun shi yasa cikin lallausan gashin kanshi yana yamutsa shi ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i
Bayan ya gama tarwatsa komai na d'akin a k'asa gefen bed ya xube yana wani irin shashshak'a idanun shi sunyi matuk'ar yin ja can kuma suka fara xubar da wasu xafafan hawaye suna sauka kan face d'in shi Allah sarki abduljabbar ya bani tausayi sosai yanxu mai xai cewa nauwara da wani ido xai kalle ta har ya bata hak'uri shi yasa ake son mutum ya dunga bincike Kafin ya aiwatar da abu kada yaxo yana da nasani wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe shi tuni ya fara karkarwa hannun shi ya mik'a ya d'auko picture d'in nauwara tayi kyau sosae tana sanye da english wears tana er dariya mai ban sha'awa duk dimple d'in ta biyun sun lotsa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara irin wanda mutum ya shiga cikin mugun damuwa yayi rungume photon yayi a kirjin shi yana wani irin kuka kamar ba soja ba kodan so ba ruwan shi

Lokacin da joseph Yayi parking a kofar gdn su jiddah dakyar ta iya fito wa ta shiga gidan duk jikin ta jina jina tana wani irin kuka ita duk duka nan da yayi mata bai dame ta ba irin sakin da yayi mata yaraf ta xube a tsakar gidan nasu da sauri mamee ta k'araso inda take hankalin ta a matuk'ar tashe ta d'ago ta cikin kid'ima da ganin yanda Jiddah ta koma duk fuska a kumbura yasa tace
"lafia jiddah me yafaru wane yayi miki hka??? "
Jiddah ba baki dole Hka ta hak'ura ta had'a ruwa mai d'umi ta gasa mata jikin ta sannan ta bata paracetamol ta kora sannan tace
"kiyi min bayani jiddah wane yayi miki hka"
"Abduljabbar ne? "
Nan take mamee ta had'e rai sai da gaban jiddah ya fad'i tace
"me ya had'a ku ki fad'a min gaskia bana son k'arya "
"wai wai akan hmm....."
Ta kasa K'arasa fad'i saboda tsoro batasan wanne irin abu mamee xata yi mata ba Idan taji abin da ta aikata kuma dole ta fad'i gaskia ko don ta samu ta roki mamee tasa Abduljabbar ya mayar da ita baxa ta iya rayuwa babu shi ba tayi nadama kuma irin wadda ake so baxa ta k'ara gigin aikata hkan ba ta tuba tsawar da mamee ta daka wa jiddah shi ya katse mata tunanin da take yi harara ta watsa mata sannan tace
"kin xaunar dani ke fah nake jira??? "
Tsugunna wa tayi a k'asa ta rik'e kafafun mamee cikin kuka ta fara rokan ta ta yafe mata kuma wallahi ta tuba baxa ta k'ara ba nan ta kwashe komai ta fad'a wa mamee tun daga lokacin da farida ta bata shawarar ta kai wani d'akin nauwara matsayin tana aikata fasikanci da maxa don abduljabbar ya sake ta har xuwa yau da asirin ta ya tonu yayi mata sannan uban dukan tare da yi mata saki bata rufe bakin ta ba mamee ta dalla mata mari har biyu Sannan ta fashe da kuka tana cewa
"ashe duk abin da kika aikata a baya jiddah baki yi nadama sai da kika kuma aikata wani kin raba mata da mijin ta saboda shegen kishin ki wallahi abduljabbar yayi min dai dai naso ma yayi miki abin da yafi hka da nasan Hkane wlh da ban kula ki ba ga Ki ga gidan sai kixo mu xauna tare kici uwar da xaki ci bari baban naki ya dawo"
Tana gama fad'in hka ta hankada jiddah ta fad'i sannan ta mik'e tsaye ta fita waje tana goge hawayen fuskar ta ta bar jiddah tana cin uban kuka a d'aki tayi nadama ta tuba kuma ba tuban muxuru ba na tsakani da Allah Indai abduljabbar ya mayar da ita xata xauna da nauwara tsakani da Allah

Baban jiddah da mamee ta fad'a mishi komai ba abin da yace kuma ko kallon jiddah Inda take bai yi ba hakan ba k'aramin k'ara tsurar da jiddah yayi ba

******

Tana nan kwance taji k'arar Shigowar message d'in takai hannu xata dauki wayar don ta duba su umma suka yi sallama suka shigo d'akin murmishin yak'e ta hau yi nan suka gaisa aka hau yin hira na'eem da ameer suna mak'ale a jikin ta umma ta kalli nauwara da ammi tace "Ohh na mance waya ta a gida ina son kiran Abba naji fa'iza ta taho kuwa"
"gaskia ya kamata a kirawo aji "
Cewar ammi "nauwara ban wayar ki na kirawo shi"
Umma ta fad'i tana mik'a hannun ta ba tare da wani abun ba ta mik'a mata kura wa screen d'in kallo umma tayi mamaki d'auke a fuskar ta ganin mssg da abduljabbar ya turo mata bud'e wa tayi a hankali ta fara karanta wa xumbur ta mik'e tsaye tana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihir rajiu da sauri ammi da nauwara suka yo kan umma suna tambayar ta lafia amman ta k'asa magana da sauri nauwara ta d'auki wayar ta duba wa tayi ita ma ta karanta wani kuka ne ya kufce mata daman tasan ai K'arshen alewar k'asa shekara wajen uku baka xaune gidan miji sai gidan iyayen shi daman ai wannan abin ne xai biyo baya balle ga irin xargin da yake mata wayyo Allah gani gare ka ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki....

Aishat A muh'd

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 85~*

Cikin tashin hankali ammi tace "nauwara lafia me yafaru? "
Cikin kuka da takaici tace "ammi ya.... ya sake ni"
Rik'e nauwara ammi tayi tana girgixa ta "me kika ce bangane ba? "
"umma Yah abduljabbar ne ya turo min mssg ya sake ni baxai iya cigaba da xama dani ba ammi na rayuwa ta ishe ni daga wannan sai wannan Yah Allah gani gare ka "
Ta fashe da wani irin marayan kuka ammi ma sosai abin ya bige ta amman ta jure tana rarrashin nauwara da umma da take xaune ta xabga tagumi ko magana ta kasa yi saboda bak'in ciki

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da doctor muh'd Abdullah yake fad'i yana ja da baya daga jikin kofar shiga room d'in da aka kwantar da nauwara yaxo xai shiga yaji wannan labarin waje ya samu ya xauna dafe kanshi yayi idanun shi sunyi ja alamar yana cikin tashin hankali na abin da yaji wani tausayin nauwara ne ya ke ratsa xuciyar shi tashi tsaye yayi ya fita daga asibitin kai tsaye airport ya nufa don d'auko fa'iza duk da baisan ta ba amman yaga photon nan ta a wayar nauwara kuma xai gane ta

Bai sha wahalar samun fa'iza ba tana tsaye rik'e da trolly sai handbag a hannun ta tana ta faman kiran wayar umma ba'a d'auka ba hka wayar nauwara ma gaba d'aya ta d'an rud'e ko lafia sallama taji anyi mata cikin wata murya mai dad'i da sauri ta jiyo suka had'a ido da doctor muh'd Abdullah yana mata murmishi gaban fa'iza ne ya fad'i lokaci d'aya dakyar ta iya amsa mishi sallamar
"am Kece fa'iza koh sister d'in nauwara? "
Cikin mamaki fa'iza tace "Ya akai kasanni malam? "
er dariya yayi sannan yace
"ba abin mamaki ba ne don na sanki so ki kwantar da hankalin ki ba sace ki xanyi ba"
D'an hararar shi tayi tana cewa
"bansan ko kai wane ba baxan bi ka ba"
D'an ta6e baki yayi Kafin yace
"Sunana doctor muh'd Abdullah nine likitan da yake kula da nauwara "
D'an murmishi tayi sannan tace "okay yanxu suna ina? "
"Tana hospital sai ta k'ara samun sauk'i xan sallame ta "
Ya K'arasa fad'i yana rik'o trolly di'n hannun ta ya sa a mota tukunna suka shiga suna er hirar su har suka k'araso asibitin har room d'in da nauwara take ya nuna mata cikin tsananin farinciki ta nufi d'akin
Chapter 57 · 0% Book details