← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 73

Sashe 49

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shirya cikin wata atamfa riga da siket d'inkin tayi fiyau da ita bayan ta fesa turare ta xauna sannan umma ta miko mata yaran Xaro ido tayi cike da mamaki tace
"umma wai duk su biyun.... "
Sai kuma ta kasa K'arasa wa saboda kunya ita har ga Allah ta d'auka d'aya ne murmishin jin dad'i umma tayi sannan tace
"kin ga kyautar Allah ko duk biyun naki ne "
Dad'i ne ya ishe nauwara ta dunga kallon su son su na k'ara ratsa xuciyar ta gashi sunyi kama da sweetheart addu'o'i sosai tayi musu ta tauna Dabino ta basu (duk da an fison da xarar an haifi jariri uwa ta tauna Dabino da yawon bakin ta su had'u sai ta bawa yaro yana da amfani sosai) fa'iza da aunty kausar ne suka shigo cikin murna fa'iza ta rungume nauwara tana cewa
"sis kin ga yaran da kika haifa mana koh masu kyau dasu"
Ita dae nauwara murmishin yak'e tayi don ita kad'ai tasan abin da take ji a xuciyar ta

Sai da suka yi Kwana 2 a asibitin tukunna aka sallame su suka dawo gida en uwan umma da abba da abokan arxiki sai xuwa suke Barka aunty asma'u ma ta taho sai bayan suna xata koma en biyu dai sun yi farin jini sai xuwa ake ganin su abdulkareem shine ya d'auki nauyin yi musu yanka don yace shine uban su ko da abduljabbar yana nan haka ya kawo kaya masu yawa da kyau da tsada yace a sawa yaran umma Abba aunty sadiya aunty asma'u da kausar fa'iza har da saleem kowa sai nuna bajintar shi yake Wajen hidimtawa nauwara da yaran ta har da had'a walimah ta mata xalla su umma suka yi shirye shirye suke yi sosai na suna

Ranar suna aka rad'a wa twins sunan abba ibraheem da sa'eed sunan aminin shi yasa wanda ya rasu don Sun tambayi nauwara me xa'a samu su sai tace su ya dace da su xa6ar musu suna Don hka abba ya sa sunan shi da sunan aminin shi lokacin da nauwara taji ansa sa'eed sai da gaban ta ya fadi ranar yini tayi tana kuka cike da kewar mahaifan ta da er uwar ta, fa'iza tace a dunga kiran ibraheem da na'eem sa'eed kuma da ameer

Mutane da yawa ne suka halacci sunan don Abba da abdulkareem gayyata sosai suka yi anci ansha yara sun sha addu'o'i daga bakunan mutane

Da yamma umma suka shirya walima ta k'ayatar sosai anyi abubuwan ci da nasha kuma an rarraba abubuwa sosai, nauwara ba k'aramin kyau tayi ba ta k'ara wani kyau da haske sai sa tsadaddun suttura take ita da su na'eem da ameer sai daf da mangariba aka tashi mutane suka watse a gajiye nauwara tayi wanka ta kwanta sai bacci aunty sadiya da aunty asma'u suka yiwa yaran wanka suka shirya su cikin kayan bacci sannan suka manna su jikin mahaifiyar su don su ji d'umin ta

Washe gari su aunty asma'u da kausar suka koma gidajen su umma ta cigaba da gyara nauwara tana kula da su sosai, duk Wannan abun da ake abduljabbar bashi da labari ko Kad'an kuma abba yaja kunnen kowa kada wanda ya sake ya fada mishi

*******
Xaune yake yana faman tunani yau a k'alla watan shi 6 da taho wa course di'n da aka tura shi xuciyar shi har yanxu bata huce da abin da nauwara tayi mishi ba amman son nan nata yana mak'ale a xuciyar shi kullum cikin tunanin ta da mafarkin ta yake har mafarki yayi gashi ta haifa mishi yara kyawawa masu kama dashi tana miko mishi yana tafiya don ya kar6e su amman sai nisa suke mishi ya kasa rik'e su har ya farka daga baccin ranar yini yayi yana cikin damuwa yana masifar son yara amman ya tabbatar cikin da ya tafi ya bar nauwara dashi ya 6are Idan ya tuna jinin da ya dunga fita ta jikin ta gashi ba fuskar tambaya su umma da abba kiran gaggawar da akayi mishi waya ya sashi mike wa duk jikin shi a sanyaye ya shirya cikin kakin shi ya fita

*****

Na'eem da ameer sunyi wata 3 yaran sunyi wayo gasu tubarkallah Masha Allah suna da d'an jiki har sun iya xama yaran gwanin sha'awa kullum kamar su da abduljabbar sake bayyana take ana ji dasu en gaban goshin umma da abba ne hka abdulkareem xai ta siyo musu kayan wasa kullum sai yaxo ya duba yaran abokin shi kuma d'an uwan shi yana basu kulawa kamar shi ya haife su

Nauwara ma tayi kyau abun ta duk ramar nan ta ciko ta rage tunanin abduljabbar amman duk da hka son nan nashi yana mak'ale a xuciyar ta wani lokacin ta shige toilet tasha kukan ta ta wanke fuskar ta ta fito tana yak'e, umma ta xo wa da abba shawara akan nauwara ta koma makaranta ai kuwa nan take ya amince da hakan ba 6ata lokaci ta fara xuwa skul sai dai fa'iza ta tsere ta da shekara d'aya tayi farinciki koma warta skul sosai ta rage tunanin da take Idan taje skul ta dawo hidimar yaran ta take hankali kwance...........

Aishat A muh'd
🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 76~*

*BAYAN SHEKARA 2*

Acikin wad'annan shekara biyun abubuwa da yawa sun faru ta 6angaren nauwara ta samu Cigaba sosae ta kammala skul d'in ta cikin nasara, na'eem da ameer kuwa tuni ta yaye su tun Kafin su cika shekara 2 yaran sunyi wayo sosai ga wayo da surutu sun shak'u da nauwara don janyo su take a jikin ta sosai suyi wasa da dariya

Kowa a gidan yana ji dasu na'eem da ameer don yaran akwai shiga rai fa'iza kowa duk inda xata je kafarta kafar su bata barin su a gida tana masifar son yaran sosai har tana tambayar nauwara wani lokacin tace
"xaki bani na'eem da ameer Idan xanyi aure mu tafi tare dasu? "
Murmishi nauwara take tace
"hmm fa'iza ai kema yaran ki ne kada ki damu na baki su"
Dad'i ya isheta sai ta rungume nauwara Idan agaban umma ne hararar fa'iza take tace "kada ma kisa ran tafiya dasu don ba me raba ni da na'eem da ameer sai mutuwa "
Sai ta marairaice fuska kamar xata yi kuka abba da aunty sadiya ma suki Goyan bayan ta suna son en jikokin su Hka xata xum6uri baki tayi gaba wai an hana ta su tayi fushi su umma su dunga yi mata dariya

Kwance take a bed tana bacci hankalin kwance can ta farka a firgice tana karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun sakamakon mafarkin da tayi da ammin ta cikin mawuyacin halin na tashin hankali tuni xufa ta keto mata tana cewa
"me yake faru wa dani ne kullum sai nayi mafarkin ammi na k'wana nan "
Kuka ne ya kufce mata tayi tana cikin yin kuka na'eem ya shigo d'akin da gudu ya haye gadon tare da rungume ta ta baya ya d'ora kanshi a tsakiyar bayan ta jin bata yi mishi wasan da ta saba yi musu ba ya sashi lek'a fuskar ta sai yaga kuka take
"Mamie kuka kike waya doke ki na fad'a wa abba ya rama miki?? "
Da sauri ta goge hawayen fuskar ta tace "na'eem ba wanda ya doke ni kai nane yake ciwo "
Ta fad'i tana murmishin yak'e tuni fuskar shi ta canja alamar sauran kiris ya fashe da kuka ganin hka yasa ta fara yi mishi cakulkuli tuni ya fara dariya har sai da taga ya ware sannan ta rabu dashi
"Mamie kixo muje umma ta baki magani"
Kallon shi tayi cike da mamaki daman bai mance abin da ta fad'a mishi ba kamo hannun ta yayi yana janta alamar ta taso su tafi ganin xai fara kuka yasa ta tashi suka fita daga d'akin falon umma suka shiga kallo d'aya tayi mata ta tabbatar tayi kuka ba k'aramin tausayin ta take ba na'eem ne ya fara cewa
"umma Ki bawa mamie na magani bata da lafia "
"assha sannu nauwara me yake damun ki ?"
D'an yatsine fuska tayi tace "umma rigimar na'eem ne wlh ni lafia ta klau"
"kaiii mamie ke kika ce k'ayya babu kyau "
Ya cigaba da cewa "umma kuka naga tana yi dana tambaye ta tace kanta ne yake ciwo "
Hararar shi nauwara tayi tare da jan kunnen shi Kad'an yayi er k'ara cike da shagwa6a tace "ban hana ka Idan manya suna magana kana sa baki ba xan cire wannan bakin"
Tuni ya marairaice fuska kamar xai fashe da kuka yace
"sorry mamie nah na daina don Allah kada ki cire min baki na ina son shi"
Dariya ce ta kufce mata ganin yanda yayi umma tana daga gefe itama tana er dariya fa'iza ce ta shigo falon ita ameer ta suri na'eem tana cewa
"d'an mamie waya ta6a min kai ?"
"ba mamie bace xata cire min baki ba"
"baki kuma na'eem? "
Ta fad'a tana xaro ido kai ya d'aga mata alamar ehh d'an hararar wasa tayi wa nauwara tana cewa
"ba me cire maka baki kaji d'an mamie "
Murmishi ya saki cikin jin dad'i nan suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa umma tana ankara da nauwara da take goge hawayen fuskar ta akai akai girgixa kai tayi cike da tausayin ta yarinya tana ganin jarabta Kala Kala a rayuwar ta

*******
Tun da yaje course di'n da aka tura shi na tsawon shekara 2 ya dawo cike da nasara bai waiwayi kano ba can abuja ya tsaya jiddah ma ta biyo shi nan don baya k'aunar xuwa gidan nan nasu saboda baya son had'u wa da nauwara baya k'aunar ganin ta
Chapter 49 · 0% Book details