← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 73

Sashe 28

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata kyakkyawar yarinya ce er kimanin 18 years na hango ta fito daga mota duk uniform d'in yasha maker da irin hodar Kala Kala duk anyi kaca kaca da uniform d'in da gudu tayi cikin gida tana tsalle tsalle yayin da wata mai irin shekarun ta ta biyo ta a baya da gudu suka shige parlourn gidan

Rungume wata mata naga sunyi gaba d'aya sai kyalkyala dariya suke yi Kafin d'ayar ta xaro wayar ta k'irar iPhone 6 ta shiga d'aukan su selfie sai da tayi wajen 10 pictures sannan umma tayi magana cikin gajiya wa tace
"ke fa'iza wannan pictures d'in ya isa hka yarinya gaba d'aya bata da aiki sai pictures "

Cikin shagwa6a wadda aka kirawo da fa'iza tace "hmm umma tsabar farinciki ne fah, a yau muka yi graduation party na candy umma ai gwara mu yi murna"

Nauwara cikin dariya tace "wlh umma gaba d'aya chargen wayar ta ya k'are saboda selfie kowa ta gani sai tace sai sunyi pic "
Hararar nauwara tayi sannan tace "ehhh d'in Naga ajiye wa xanyi don tarihi wani baxa ka k'ara ganin shi ba har abada "

Sai lokacin umma hankalin ta yayi kan uniforms d'in jikin su "Hmmm Lallai yaran nan hka kukayi da uniforms d'in naku ?"
"Laaa umma dama baki gani ba wlh tsabar murnace "
Cewar fa'iza "Allah ya shirya, Allah ya taimaka yasa a samu result mai kyau "
"Ameeeeeeen umman muuu"

Suka had'a baki suka fad'a cikin tsananin farinciki ana hka aunty sadiya ta shigo cikin murna suka rungume ta ita ma kafin daga bisani fa'iza ita ma ta fara yi musu pictures har sai da aunty sadiya ta gaji tace
"Ya isa hka fa'iza ni na gaji "
Dariya suka tuntsire da ita umma tana cewa "kema kin gaji kenan ai Idan suka fara Wannan selfie d'in basa gajiya wa "

Umma ta cigaba da cewa "toh maxa aje ayi wanka a cire uniform d'in da duk ya fita hayyacin shi,axo ayi lunch"

"toh ummaaaaaaa "
Da gudu suka haye upstairs yayin da umma da aunty sadiya suka bisu da kallon farin ciki

Bayan sun yi wanka da sallah nan aka tsaya kyakyalen jiki wannan yana wane wannan har suka gama suka shirya cikin wata swiss atampha kalar blue sunyi kyau sosai daman sun dinka ta don xuwan wannan ranar sai dai nauwara tafi kyau

Masha Allah abin da umma da aunty sadiya suka fad'i ganin yanda yaran suka yi matuk'ar kyau, suna gama yin lunch suka shige gidan aunty kausar

******

Xaune yake a katafaren office d'in shi Idan dai hka lissafin sa yake toh yau nauwara da fa'iza suka ka kammala sec sch, ya soma gajiya da wannan dakon son da yake mata ya kamata ya samu mafita a kullum yaje kano ya dawo ganin ta ba k'aramin dad'a rikitashi yake ba abin ba k'aramin bashi mamaki yake ba tun yana danne wa yana k'arya ta abin har ya dawo yana gasgata hkan wayar shi ya d'auko number d'in umma ya kirawo sun d'au wajen mintuna 10 suna magana Sannan ya kashe wayar duk jikin shi ya mutu a kasalance yake jin su gashi yau ko er hayaniyar su bai ji ta waya ba

Dakyar ya iya tashi ya tafi gida ko abincin dare bai iya ci ba ya kwanta cike da tunanin nauwarah a xuciyar shi yana Mai addu'ar Allah ya sa rabon shi

********

A yau candyn su nauwara da Sati d'aya suka tarkata inasu inasu sukayi gidan aunty asma'u abuja kenan suka bar umma da saleem

Sunje sun tarar da ita da tsohon ciki tashi dakyar xama dakyar don hka taji dad'in xuwan emmatan umma duk da tana da en aiki amman wani abun sai na ka

Da wani yammaci aunty asma'u ta aike su siyayya a sahad store daman kiris suke jira don hka cikin d'oki suka shirya driver ya d'auke su sai sahad store lokacin da suka fito a mota sai kallo ya koma kansu don ba k'aramin kyau suka yi ba har sun d'an diririce saboda kallon da ake musu dakyar suka lala6o nutsuwa suka shiga cikin store d'in

Suna cikin siyayya wani hadadden guy yace "Hello Babs"
D'ago kai suka yi a tare suna kallon shi ya cigaban da cewa "I'm fysal "

Had'a ido suka yi fa'iza da nauwara gira nauwara ta d'aga mata yayin da fa'iza ta kashe mata ido d'aya lokaci d'aya suka saki murmishi cikin iyayi fa'iza tace
"kana buk'atar wani abun"

Shima cikin murmishi yace "mene sunan wannan"
Ya nuna nauwara dake gefe a tsaye "oh sunan ta nauwara "
"nice name ke fah?"
"fa'iza "
"OK fa'iza ko xaki magana da sister d'in ki ta ban 2 mints "
"okay Wannan ba matsala ne ba "
Ta K'arasa kusa da nauwara tana yi mata magana k'asa k'asa suna d'an murmishi

A nutsu ya sako kafar shi cikin store d'in yana sanye da black d'in jeans da t-shirt yellow mai dogon hannu ya sanya takalmi bak'i mai ratsin yellow a jiki da black d'in glass yayi mugun kyau ba Kad'an ba sai tashin k'amshin turare yake Mai dad'i emmatan wajen gaba d'aya sun raja'a da ganin kyakkyawan guy d'in nan har da maxa en uwan shi ya birge su

B'angaren wurin turarruka ya nufa dummm gaban shi ya fad'i ganin wasu masu kama da nauwara da fa'iza suna tsaye da wani guy sai faman murmishi suke yi a tafiyar shi irin ta sadaukan maxa ya d'an K'arasa kusa dasu ko babu tantama wad'annan su fa'iza ne me ya kawo su abuja, me suka xo yi?, a matuk'ar fusace ya k'arasa wajen idanun shi sunyi jajur dasu saboda tsanani 6acin rai.........

Toh fah su nauwara da fa'iza ko mai xai faru dasu

*Aishat A muh'd*😘

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

*~Pg 50~*

A gaban su ya tsaya sai huci yake hannu ya fidda ya xuba ma nauwara mari sannan ya juyo kan fa'iza ya bata mari lokaci d'aya suka saki wani irin ihu tare da d'ago kai don ganin wanda ya mare su Wayyo Allah sauran Kad'an su saki fitsari a tsaye tsabar tsorata ganin ya abduljabbar tsaye kansu ,jikin su sai rawa yake sun kasa cewa komae cikin fusata fyasal yace
"me suka yi maka kake dukan su?"
Wani d'an iskan kallo abduljabbar ya yi mishi tuni ya shiga taitayin shi saboda tsabar kwarjinin da yayi mishi bai iya cewa komai ba hannun su nauwara da fa'iza ya kama suka fice a motar shi ya watsa su har suna gwarewa da kansu wani ihun suka k'ara saki sai kuka suke sun tsorata da ganin yanayin abduljabbar

Driven da ya kawo su fa'iza ya sallame shi ya koma gida xai kawo su nan kuwa ya juya ya tafi cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya shigo motar kifa kanshi yayi kan steering motar wani axabbaben kishi ne yake damun shi cikin tsawa yace
"Wlh ku rufe min baki ko yanxu ku ci duka"

Ba shiri suka had'iye kukan sai na xuci suke a hankali ya fara driven har suka k'araso gidan aunty asma'u duk wani motsin ta yana kallon ta, ta madubin motar yana hango shatin hannun shi a fuskar ta sannan ga fuskar tayi ja abin ka da farin fata

Suna shiga gidan sum sum sukayi xa su shige d'aki ya daka musu tsawa "uban waye yace ku tafi oya kuxo Kuyi tsallen kwad'o "

Had'a ido suka yi fa'iza da nauwara cikin matuk'ar kad'uwa wata tsawar ya dad'a daka musu ba shiri suka fara cikin rawar jiki hawaye majina duk sun had'e a fuskar su ga gumi da suke nauwara tafi ma iya tsallen kwad'on saboda bata da k'iba fa'iza tafi ta jiki Kad'an, abin ya bashi dariya ganin sun xube kamar wasu sumammu danne dariyar tashi yayi sannan yace "wa yace ku tsaya, oya ku cigaba ba sai Kinyi 50 minutes Kuna yi"

Cikin rawar murya suka fara bashi hak'uri "Don girman Allah Yah abduljabbar kayi hak'uri baxa mu k'ara ba"
k'ara d'aure fuska yayi tare da cewa "lokacin da xaku xo abuja kun sanar da ni shine har wani tsaya wa kuke da samari ko wai Kun girma koh??? "
Girgixa kai suka yi cikin kuka suka ce "baxa mu k'ara ba kayi hak'uri pls"

Nan suka dunga magiya suna bashi hak'uri har aunty asma'u ta sakko downstairs cikin mamaki take cewa "ah yau abduljabbar ne a gidan nawa tabbb yau wacce rana xa'a yi mana ruwa da k'ank'ara "
Harara ya dalla mata sai lokacin ta ankara dasu nauwara da fa'iza tsugunne a gaban shi tace "lafia kuke kuwa, wannan kukan fa"

"ritsa su nayi a sahad store suna hira da saurayi "
"a'a abdul ai ni Aiken su nayi siyayya sai dai idan tsayar dasu yayi "

Aunty asma'u ta fad'i hkan "hmm ni ai surutu naga suna yi alamar sun dad'e da tsaya wa, don hka Kuyi maxa ku tattara kayan ku Kano xan mai da ku tunda bakwa jin magana"

"Haba abdul d'in umma d'an lelan Abba kayi hak'uri ka barsu suna taimaka min "
"sai dai da sharad'in baxa su sake fita ba"
Cikin sauri suna had'a baki suka ce "ehhh Yah abduljabbar mun yarda "
Harara ya watsa musu da sauri suka mik'e d'akin da aka basu suka shige kan bed suka xube sae mayar da numfashi suke "daman Hka Yah abduljabbar yake fa'iza?"
Nauwara ta tambayi fa'iza "kuttt ai ya mafi hka wlh" fa'iza ta bata amsa daga hka fa'iza ta shige toilet tana cewa "Bari naje na gasa jikina don sai nayi ruwan xafi wlh"
Nauwara batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba hararar ta fa'iza tayi ta shige toilet ita ma dariyar ta fara a cikin toilet da ta dunga tuno yanda suke tsallen kwad'on
Chapter 28 · 0% Book details