← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 73

Sashe 37

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su nauwara da fa'iza suka kallon abin da yake faruwa da farko wani kishi ne ya kamata ganin yana kula ta amman ganin yanda suka rabu yasa su kwashe da dariya tare tafawa ita kanta tasan Yah abduljabbar daban yake acikin maxa yana da kyau, kud'i da muk'amin min shi hkan baisa ya kauce hanya ba sam baya kula mata da hka suka K'arasa wajen shi bayan sun shiga motar suka gaida shi cikin girmamawa kamar yanda suke mishi da ya amsa cikin jin dad'i fuskar nan tashi a sake yau sai faman murmishi suke yiwa junan su yayi mata kyau yau fiye da koyaushe ko dan yau ta fara ganin shi da manyan kaya yadin kufta ne a jikin shi kalar dark blue d'inkin xamani irin wanda matasa suke yayi yanxu takalmin shi da hula bak'ak'e ne amman hular da ratsin blue a jiki agogon hannun shi bak'i ne shima ba k'aramin kyau yayi ba Idan ka kalle shi bakace yana da mata ba
fa'iza tana sit d'in baya tana kallon su ba k'aramin birgeta sukayi ba sun dace da junan su da hka har suka K'arasa gida yana gama parking wuf fa'iza tayi ta bud'e kofar ta fice ita ma nauwara xata fita ya kamo hannun ta yace "kamar baki farincikin ganina ba kuma don ke na ajiye aikin dake gabana naxo"
"Ayyah Yayah nayi murnar ganin ka mana Allah kawai na gaji ne "
"alright so bari na barki ki huta xuwa anjima na dawo ki kular min da kanki " murmishi kawai tayi tare da fita daga motar bai tafi ba har sai da ya daina ganin ta sannan tafi nashi gidan......

Aishat A muh'd ??

*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd 😘

*~Pg 61~*

A ranar umma ta fadawa abba abin da abduljabbar yake so dariya kawai yayi sannan yace "ni awaje na ba matsala sai yaxo neman aure a wurina tunda nine uban 'ya" ita dai umma dariya kawai tayi, don hka Washe gari da yaxo umma ta fad'a mishi hkan don dad'i baisan lokacin da ya rungume umma ba cikin dariya tace "baka da kunya koh abdul? "
Sosa kai yayi cikin murmishi yace "afuwan ummana dad'i ne ya ishe ni "
"toh ba wannnan ba ka sanar da jiddah? "
"ban fad'a mata so nake yau na fad'a mata yanxu ma daga nan sai gidan mamee xan sanar da ita "
"don Allah kada kaje ka biye wa jiddah ka lalla6a ta kasan halin ta dai gata da shegen kishin tsiya "
Maganar umma ta K'arshe ta bashi dariya yace "Kada ki damu umma xanyi yanda kika ce "
Nauwara ce ta k'araso wajen xuba mata ido yayi kamar yau ya fara ganin ta duk kunya ta gama lullu6e ga umma xaune awajen gyaran murya umma tayi firgigit ya dawo hayyacin shi yana shafa kanshi kallon ta umma tayi tana cewa "Yayan ku xaki kawo mishi abinci "
Dakyar ta iya cewa "tohh umma" saboda kunya ta wuce xuwa kitchen cikin en mintuna ta shirya mishi table d'in dake gaban shi da abinci ta juya xata tafi yace "baki serving d'ina ba? "
Harara umma ta watsa mishi tace "yi tafiyar ki nauwara kyale shi "
Da sauri ta wuce xuwa d'akin su yayin da abduljabbar yace "Haba umma kada kisa ta fara rainani "
"ba dai nauwaran da nasani ba na tabbata ba daga k'aramin gida ta fito iyayen su tabbas sun basu tarbiyya mai kyau "
Da hka ya fara cin abincin bayan ya kammala yayi sallama da umma ya tafi gidan mamee babar jiddah bayan sun gaisa yake sanar da ita auren da xai k'ara da nauwara sam bata nuna mishi komai sai ma addu'ar fatan alkhairi da ta bishi da ita nan ya cika ta da kud'i yayi gaba

Sai da ya biya ta wajen abdulkareem suka sha hirar su sannan ya K'arasa gidan shi har cikin bedroom d'in ta ya bita tana kwance sai faman chatting take tana ganin shi ta mik'e tsaye tayi hugging di'n shi shima k'ara rungume ta yayi a jikin shi sannan yace "Ina son yin magana dake so ki biyo ni xuwa d'akina "
Cikin er dariya tace "toh ina xuwa"
Fice wa yayi daga d'akin ya barta tana dad'a gyara jikin ta mybe wata samu war ce tunda ake neman ta lokacin da ta K'arasa d'akin yana wanka sai da ta jira shi ya fito ya shirya cikin sleeping dress cotton farare sol dasu ya fesa different body spray nd perfumes masu matuk'ar k'amshi mai dad'i ya dawo kan bed ya xauna jiddah sai binshi take da kallo xuciyar cike da kaunar shi hannun ta dukka biyun Ya rik'o mai da kalar fuskar shi yayi bata wasa ba a nutse ya fara da yi mata nasiha Sannan ya gangaro kan batun auren shi da yake so yayi wani irin mik'e wa tsaye tayi tare da fincike hannun ta idanun ta Sun rufe da kishi tace "aure kuma abdul, wa xaka aura? "
Babu d'ar ko Kad'an a tare da shi kai tsaye yace "nauwara ita xan aura"
"what! Wacce nauwara ?"
"wadda kika sani dai ta gidan umma"
"kuttt lalai ma na yarda kai mara mutunci ne ka rasa wanda xaka aura sai Wannan mai kama da aljanu wayyo Allah na shiga uku Wlh baka isa ba baxan xauna da kishiya ba ba gwanda kowacce ba da wannnan yarinya"
Tass kake ji ya wanka mata lafiyayyen mari sakamakon Cakumo wuyan rigar shi da tayi kafin ta dawo hayyacin ta ya saki kifa mata wani da sauri ta sake shi gashin ta yaja sai da tayi wata k'ara don axaba idanun nashi sunyi ja dasu sai faman huci yake yau jiddah ta kaishi bango shi take xagi "ni sa'an ki ne da xaki xage ni baki sanni ba but yau xaki san Kala ta Abduljabbar an gaya miki kishi hauka ne akan ki aka fara kishi da xaki xo Kina yi min rashin hankali"
Belt d'in da ya cire yasa hannun shi ya d'auko ta guda d'aya ya xuba mata ta saki ihu don ta shige ta ba Kad'an ba ya daga belt d'in xai sake xuba mata ai kuwa kafa mai naci banba ki ba da gudu ta bar d'akin sauran Kad'an dariya ta kubce mishi ganin yanda take gudun cillar da belt d'in yayi ya kwanta xuciyar shi gaba d'aya ba dad'i jiddah tayi masifar 6ata mishi rai sai juyi yake yana xuba tsaki yana son ya kirawo nauwara yaji muryar ta ko yaji dad'i a xuciyar shi wani 6angare na xuciyar yana hanashi saboda bai kamata ya kirawo ta a wannan lokacin ba a matsayin shi na me mata duk da sun samu sa6ani da jiddah toilet ya shiga ya d'aura alwala ya fito ya shimfid'a abin sallah nan ya fara nafila don neman za6in Allah

K'wana jiddah tayi tana kuka duk idanun ta Sun kumbura ana fito wa daga masallaci sallahr asuba ta janyo akwatin ta ta saka a motar ta da gudu ta fice daga gidan yana jin fitar ta karshe ma sai yaja bargo ya lallu6a bacci ne yayi awon gaba da shi daman daren jiya bai samu cikakken bacci ba

Tana xuwa gidan su ko xama batayi ba mamee da babanta suka fatattake ka kuma sun yi ratsuwa da Allah Idan bata koma gidan ta ba basu ba ita ta nemi wasu iyayen tun da daman ai umma ce ta rik'e ta har ta girma a wajenta ta aurawa abduljabbar ita mene bata yi mata sannan don tsabar butulci irin na *D'AN ADAM* (littafin rufaida Omar) xata ce baxata xauna dashi ba ita bata ga abin da ta aikata musu a baya amman basu rabu da ita ba suka kyale ta shine dan iskan ci xaki xo kawo mana yaji ai kishi ba hauka bane nan suka yi mata tas ba yanda xata yi Hka ta dawo gidan abduljabbar don duk iskan jiddah da rashin mutuncin ta tana son iyayen ta Bata son 6ata musu rai motsin dawo war ta shine ya tashe shi daga bacci wanka yayi ya shirya cikin black trouser da purple d'in t-shirt ya fito ya fice daga gidan gaba d'aya

Jiddah fa ta shiga tashin hankali nan da nan tabi ta rame abduljabbar ya daina bi ta kanta kawai abin da yake gaban shi yake ana cikin hka abba ya yanke lokacin auren nan da two months Insha Allah kamar yanda abduljabbar yake so

Nan fah umma aka shiga hidima ba kama hannun yaro uwar amaryar uwar ango turkashi duk ita kadai 6angaren su aunty asma'u da kausar su kuma yanda xa'a gudanar da programs di'n bikin suke shirya wa yayin da ango abduljabbar ya sakar musu bakin aljihu

Gyara sosai umma ta xage tana yiwa nauwara ciki da waje duk abin da akasan uwa tana yiwa erta umma tana yiwa nauwara shi mai gyaran jiki wata k'awar umma ta d'auko shuwa arab ce ita take gyara nauwara ga abubuwan gargajiya irin na da umma tana yi mata nan da nan ta k'ara wani irin kyau jikin ta ya goge ya k'ara kyau in banda sul6i da taushi sai k'amshi fatar jikin ta take

Umma da kanta ta had'a lefe nagani na fad'a anyi 6arin kud'i ba Kad'an ba komai yaji don tsayawa fad'a muku abubuwan da suke ciki 6ata lokaci ne mai karatu sai Kuyi hasashe harda jiddah aka had'o wa na fad'ar kishiya kamar yanda al'ada take kuma umma ce take mata har gida tayi mata nasiha tana tafiya ta hau jifa da kayan kamar wata mahaukaciya duk tabi rikita kanta sosai take jin haushin umma, gashi abduljabbar ya fita harkarta k'wata k'wata ga ba me bata shawara don tuni sunyi fad'a da farida k'awar ta tun lokacin da ta xubar da cikin nan abu goma da ishirin suka had'ar ta ga lokaci sai taho wa yake ta tsani kishiya tana masifar son abduljabbar shi yasa take bala'in kishin shi ta d'auki alk'awarin duk wadda tayi gigin auran mata miji xatayi da tasani........

_Kuyi hak'uri fans wlh jiya nayi muku typing da yawa na goge shi ban sani ba_

*Aishat A muh'd*😘
🍀☘☘
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd {Aunty}😘
Chapter 37 · 0% Book details