← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 73

Sashe 20

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banda ihu da ambatar Allah babu abin da nauwara take cewa kuka take yi sosai tana neman taimako har sun kekketa mata riga ga saleem shima an rirrik'e shi sai kuka yake yi yana kiran sunan nauwara...

Gudu sosai yake yi akan hanyar shi ta dawowa daga abuja saboda ganin dare yayi mishi gashi ko driver bai nema ba da kanshi yake driving

A hankali yake jin ihu yana tashi daga wani b'angare kuma da alama ihun mace ne da yaro k'arami bai san lokacin da ya taka birki ba tare da fitowa daga motar yana sanye da kakin shi da sauri yayi hanyar da yake jin ihun
Ganin wasu matasa su 3 suna kok'arin yiwa wata yarinya fyad'e yasa bai san lokacin da yayi wani wawan tsalle ba ya kaiwa d'aya daga cikin su naushi ba ai kuwa tuni ya xube a wajen da sauri sauran suka cika saleem da nauwara xasu gudu ai kuwa ya damko su tare da gwara kansu lokaci d'aya suka saki ihu tare da xube wa a k'asa belt d'in jikin shi ya ciro ya fara dukan su sai da yayi musu lilis tukunna ya kirawo number d'in police tare da yi musu tare da yi musu kwatancen wajen suka ce Gasu nan xuwa...

Kan yarinyar ya koma gaban shi yayi wata iriyar fad'uwa ganin yarinyar da yake mafarki da ita ce kullum tana neman taimakon shi da sauri ya kau da kanshi daga kanta saboda ganin sun yaga mata riga jikin ta ya bayyana a waje mik'e wa tsaye yayi yana tunanin da me xai suturta mata jikin ta kafin ya ankara yaga en sanda sun kusa k'araso wa inda suke tuni hankalin shi ya tashi saboda baxai so su ganta a haka ba

Cikin xafin nama ya cire rigar kakin shi ya sanya mata sai lokacin ya ankara ashe ta suma da sauri ya d'auke ta cak ya sanya ta a bayan motar ya kamo hannun saleem ya sashi a motar tukunna ya K'arasa wajen en sandan nan yayi musu bayanin fyad'e suke yunkurin yi mata Don hka su tafi dasu xuwa station su hukunta su dai dai da laifin su yana gama yi musu bayanin komai ya juya ya shiga mota yayi mata key ya bar wajen, su kuma en sandan nan suka damk'e su tare da tura su a cikin mota sukayi gaba

Gudu sosai ya dunga yi har ya k'araso hospital d'in da suke xuwa yana parking ya fito daga motar ya d'auki nauwara suka yi hanyar shiga cikin asibitin saleem yana binshi a baya

Da sauri nurse suka kar6e ta tare da kaita wani d'aki sannan suka kirawo doctor nan ya fara binciken yarinyar har numfashin ta ya dawo dai dai sannan ya sanya mata drip saboda yunwar da ta gala6aitar da ita sannan ya fito daga d'akin xuwa office inda ya bar abduljabbar a xaune

Bayan doctor ya xauna ya d'ago kai ya Kalli abduljabbar ya fara da cewa "Alhmdullilah yalla6ai ta farfad'o daga suman da tayi kuma basu yi nasarar yi mata fyad'e ba, tsoratar da tayi shi yasa ta suma, gashi tana xama da yunwa don tana d'aya daga abin da ya k'ara gala6aitar da ita "

"okay doctor xa'a kiyaye hkan, bayan hka ina son ka duba min yaron nan shima "

"toh yalla6ai "

Nan ya danna k'ararrawa wata nurse ta shigo da sauri yace "Yawwa sister wannan yaron xaki xo min dashi "

"okay sir "

Ta fad'a tana satar kallon abduljabbar don guy d'in ya had'u ta ko'ina, Kafin ta shige ta xo da saleem nan doctor ya d'ora shi kan gadon dake office d'in ya shiga duba shi

Shima saleem d'in babu abin da yake damunshi fiye da yunwa nan ya yiwa abduljabbar bayani Sannan ya Kalli nurse d'in nan yace

"Don Allah sister xan d'an had'a ki da wani aiki wannan yaron xaki had'a wa tea yasha sannan a d'an samo mishi abin da xai ci mai d'an nauyi, baya nan ga magani xan rubuta miki kije pharmacy ki siyo sai ki bashi yasha"

"okay sir ba damuwa "

"Yawwa ngde sosae "

Har ta kama hannun saleem xata fice daga office d'in abduljabbar ya dakatar dasu ai kuwa jikin ta na rawa ta dawo ta tsaya sai wani karairaya take mai da kallon shi yayi kan doctor yace

"Ko xaka yi mata magana ta xauna ta kula su xuwa lokacin da xa'a sallame su Idan yaso sai na biya ta"

"toh kinji fah xaki iya? "

Cikin mak'ale murya tace "Why not doctor xan iya sosai ma"

Murmishi doctor yayi tare da fad'in "Thank u sister"

Daga hka ta fice daga office d'in ita da saleem abduljabbar ma tashi yayi tsaye tare da yiwa doctor sallama sai da safe xai dawo daga hka ya fice daga office d'in

Yana xuwa gida wanka ya shiga yayi sosai ya fito sannan ya shirya cikin sleeping dress farare sol dasu ya fesa turare sannan ya had'a coffee yasha yana gama wa ya kwanta kan bed ko tunanin neman jiddah bai yi ba saboda har yanxu yana jin haushin ta tare da k'aro karfin Ac Wannan daren bai yi bacci sosai ba xuciyar shi cike da tunanin wad'annan yaran ko ina iyayen su suke har suka barsu suna yin bara tunani dai barkatai ya dunga yi a cikin Wannan daren Kafin dakyar bacci ya dauke shi...

☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘?

*Written by*

*Aishat A muh'd {Aunty }*??

_wannan page d'in sadaukar ce ga en group d'in saNaz novella da ruky & ashba novels grp da classic novels da en group d'in hausa novels babu abin da xance muku sai dai nace ngde da yanda kuke k'aunar littafin nan_❤??

*~Pg 36~*

Washe gari misalin karfe 9 na safe nauwara ta farka daga baccin allurar da doctor yayi mata, cikin kuka ta farka kuwa don tuno abin da ya kusan faru wa da ita jiya nan nurse d'in nan da saleem suka rarrashe ta dakyar tayi shiru sai faman ajiyar xuciya take

A hankali ya turo kofar bakin shi d'auke da sallama ya had'e cikin wani blue jeans da t-shirt fara mai dogon hannu ta d'an kama shi Kad'an hkan ya bayyanar da alamar karfi a tattare dashi kannan nashi yasha gyara sai faman kyalle yake ga agogon hannun shi black ba k'aramin dace wa yayi da tsintsiyar hannun yayi ba da yake ya d'an nannad'e hannun rigar Kad'an tuni sassayan k'amshin turaren shi ya cika d'akin gaban nauwara ya fad'i jin k'amshin turaren shi ai wannan k'amshin turaren kamar ta ta6a jin irin shi

Ita kuwa madam nurse an ga d'an hadadden guy tuni an fara gyara xaman riga tare da fara gwalangwaso (nace Idan dai abduljabbar kike yiwa Hka Kya yi Kya gama lol)

Manyan ledar hannun shi ya ajiye bayan ya yiwa su nauwara kallo d'aya cikin muryar shi mai dad'in gaske yace "am don Allah Idan ba tak'ura xaki gyara min jikin su ga komai nan a ciki har da takeaway na breakfast "

Cikin iyayi da fari da ido tace "ba damuwa yalla6ai "

D'an Murmishi yayi wanda iyakar shi fatar bakin shi yace "Thank u "

Yana gama fad'in hka ya fice xuwa office d'in doctor ta bishi da kallo Kafin ta dawo da hankalin ta kan ledar da ya ajiye ta shiga duba wa kaya ne doguwar riga da riga da siket set bibbiyu sai takalmi flat shoes Kala 2 sai under wears da kayan namiji set 4 na saleem kenan har da takalmi ga turarruka har Kala 2 sai hijab 2,da mayuka su cream sai shampoo and conditioner da kuma na shafa wa akai sai hand dryer Gaskia da ganin kayan ya kashe kud'i sosai

D'ayan ledar kuma dangin kayan tea ne sai kuma fruit da takeaway d'in da yayi musu don hka tashi tayi ta hadawa saleem ruwan wanka da kanta tayi mishi saboda baxai iya fitar da kanshi ba don ba k'aramin daud'a Yayi ba ai kuwa tun daga gashin kanshi ta fara wanke wa nan tayi mishi wanka bayan sun fito ta shirya cikin d'aya daga cikin kayan nan ta gyara mishi farcen kafar shi da na hannu Haba tuni saleem yayi shar dashi kamar ba shi ba sai dai er ramar da suka yi da kuma duhun da sukayi wannan kuma wahala ce sai a hankali

Bayan ta gama da saleem nan ta shigar da nauwara toilet d'in itama daga kanta ta fara wanke wa tana warware gashin tace masha Allah a xuciyar ta ganin dogon gashi mai kyau ga santsi da laushi don ma baya samun gyara wanke mata shi tayi tas sannan tayi mata wanka suka fito ta shirya ta cikin wata gown kalar ash tana da kwalliyar red flowers a jiki sai mayafin ta k'arami shima red nan ta busar mata kai da hand dryer ta shafa mai Sannan ta tufke mata shi d'an kwalin rigar ta d'auka tayi mata rolling d'in kanta dashi ta fesa mata turare

Masha Allah ba k'aramin kyau nauwara tayi ba kamar ba ita ba abu biyu ne Yayi mata cikas makanta da gurgun ta, sai da ta yanke mata farce Sannan ta had'a musu breakfast sukaci suka koshi suna gama ci ta basu magungunan su suka sha sannan ta fita don kirawo doctor

Tana fita saleem ya k'araso kusa da nauwara ya kama hannun ta tare da cewa "Aunty nauwara wlh Kinyi kyau sosae "

Murmishi tayi kafin tace "kai ma nasan saleem kayi kyau sosai Allah ya sakawa mutumin nan da ya taimake mu da alkhairi"

"Ameeen aunty nauwarah kingan shi kuwa kyakkyawa dashi kamar balarabe"

"kai saleem " ta fad'a tana dariya shima saleem dariyar yake yana cewa "da gaske nake wlh"

Shigowar doctor ne da abduljabbar ya katse su da yin hirar su duk sunyi ji dad'in ganin yanda nurse d'in nan ta gyara su ba kyiwa sai da doctor ya k'ara duba su sannan yace da abduljabbar yana da magana dashi su koma office

Bayan sun isa office d'in sun xauna doctor ya fara da cewa "yalla6ai kasan yarinyar nan bata gani kuma bata iya tafiya koh"
Chapter 20 · 0% Book details