Sashe 26
Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sakin baki kawai nauwara tayi gaba d'aya ta rasa me xata cewa umma tsabar farinciki sai kawai ta fashe da kukan farinciki
"Haba nauwara kukan me xaka yi kuma kawai Ki gode wa Allah don shi yayi silar had'uwar mu "
Har yanxu dai ta kasa cewa komae ganin haka yasa umma ta rungume ta tare da bubbuga bayanta cikin sigar lallashi tace "nace Ki shiru nauwara ai Kinsan baxa mu barki da haka ba alhalin muna da kud'in da xamu taimake ki, kisani fa mun dauke ku tamkar su fa'iza "
Cikin muryar kuka tace "umma bani da kalaman da xan gode muku sai dai addu'a da xan dunga yi muku har K'arshen rayuwa ta Allah kada ka nufe ni da yi muku butulci akan abin da kuka yi mana "
"kada ki damu nauwara fatan mu shine Allah ya baki lafia "
"Ameeen umma na gode hak'ik'a ke uwa ce ta gari "
Murmishi kawai umma tayi nan ta fara bawa nauwara labari masu dad'i da hka har abba da aunty sadiya suka shigo falon bayan an gama gaisa wa umma ta sanar da abba da aunty sadiya maganar xuwa jiddah sosai sunji dad'in hkan tare da addu'ar Allah yasa a dace
Daga hka Abba ya fita ya barsu umma suna hira kamar ba kishiyoyi ba ba ruwan su da irin jahilcin kishin nan tsabtattacen kishi suke irin na matar k'warai da suka shud'e
Lokacin da fa'iza da saleem suka dawo a skul umma take basu labari tsallen murna suka dunga yi cike da farin ciki sannan suka rungume nauwara har suna kok'arin yar da ita sai da umma tayi musu magana tukunna suka cikata
******
Alhaji salisu tun lokacin da yaran shi suka kawo mishi labarin sun kad'e su nauwara sun mutu dad'i ne ya kama su nan suka sallami yaran da mak'udan kud'ad'e tare da ce musu Indai wani aikin ya taso xasu nemo su saboda sun yarda da iya aikin su
Nan ya tsunduma da cin dukiyar marayu baji ba gani cikin kankanin lokaci ya xama gawurtaccen attajiri K'arshe ya ginawa innar shi katafaren gida ta dawo da xama ciki ya bar baffan shi da innar marigayi Alhj sa'eed acikin tsohon gidan su ko da baffa yace xai yi mishi magana inna tace a barshi kawai Indai dukiya ce anan duniya xai barta yaje yayi taci don hka kawai suka xuba mishi ido
A bangaren Alhj lawan shana kuwa nan ya fara nuna wa Alhj salisu hassada akan yanda yanxu ya fishi kud'i bana wasa ba, sannan yak'i ya sakar musu yanda suke so shi da er shi bayan da taimakon su ne har ya cimma burin shi tun da dasu aka sha wahalar komai don hka suka fara shirya mishi gadar xare......
Tuni ya mulmule ya narka wata uwar k'iba sharholiyar shi kawai yake sha kamar baxa'a mutu ba aje a tarar da abin da aka aikata ba, hankalin kwance don ya mance da wani yayan shi Alhj sa'eed balle su nauwara burin shi d'aya ne ya cika mallakar dukiyar d'an uwan shi kuma ya samu sauran abu d'aya da har yanxu yake masifar wahalar shi .....
******
Acikin Sati biyun nan komai ya kammala na tafiyar su nauwara da umma xuwa k'asar jiddah duk wani abu an gama sai jiran ranar tafiya kawai
Ranar Tuesday da misalin karfe 7 na dare jirgin su umma ya tashi daga airport d'in malam aminu kano xuwa k'asar jiddah, en rakiya aunty sadiya da fa'iza sai saleem suka dawo gida cike da kewar umma da nauwara ttare da yi musu addu'ar Allah ya sauke lafia kuma Allah yasa a dace da abin da akaje nema...........
🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀
*written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*😘
*~Pg 46~*
Nauwara sun sauka a k'asar jiddah lafia a wani hadadden hotel sukayi masauki Mai 2 bedrooms da falo d'aya ,sai da suka huta washe gari suka fara xiyartar asibitin da umma take ganin doctor
Bayan sun gama da bincikar umma aka dawo kan nauwara nan fa suka fara dogon bincike akan nauwara wanda daga K'arshe suka rik'e nauwara akan xasu kwantar da ita
Cikin k'wanakin nan suka tsanan ta bincike har suka yi nasarar gano matsalar wata jijiyace wadda take taimaka wa wajen gani ta samu matsala da dole sai anyi mata aiki tukunna, bayan sun yiwa umma bayani ta kirawo abduljabbar take fad'a mishi abin da suka ce
Haka kuwa akayi sun yiwa nauwara aikin ido amman sai nan da wasu en k'wanaki xasu bud'e mata idon suka cigaba da kula da ita tare da bata magunguna da suka kamata
Nauwara ba k'aramin kyau ta k'ara a en k'wanakin nan ba tayi fari ta k'ara k'iba Kad'an kamar ba mai jinya ba, wanda ya san ta da ba Lallai ya gane ta ba don gaba d'aya ta canja kamar wadda aka k'arawa kyau ita kanta umma ido take xuba mata a xuciyar ta tana fad'in Masha Allah daman wahala ce ta mayar da ita hka
*ABUJA*
Kwance yake a kan 3siter ya rungume pillow a kirjin shi ya xurfafa a tunani sosai na yanda xuciyar shi take kok'arin kar6ar wani sak'o wanda sam bai san lokacin da ya shiga cikin xuciyar shi ba har yana kok'arin mamaye mishi xuciya
A kullum sai yayi tunanin yarinyar nan yafi sau a kirga a rana ban da dare wanda kusan k'wana yake tunanin ta a xuciyar shi baya iya samun ishsshen bacci da farko ya d'au ka tausayi ne sai tausayin ya rikid'e ya koma soyayya
Soyayyar ma irin xaxxafar nan ai abin kunya ne yaje ya furtawa K'aramar yarinyar so ai wannan xubda girma ne K'arshe raina shi xatayi (a tunanin abduljabbar fah), don hka xai cigaba da addu'ar Allah ya cire mishi son ta...
Hannun shi ya sa a gashin kanshi yana yamutsa shi Mtsww yaja tsaki tare da tashi ya xauna remote ya d'auka canja tasha ya fara har yaxo kan tashar mbc 2 suna film d'in rush hour kallon film d'in ya fara yi ko xai d'auke mishi hankali daga tunanin da yake damun xuciyar shi.........
********
Daren washe gari umma da duk wani masoyin nauwara addu'a yake mata don gobe xa'a xata fara bud'e idon ta, suna yi mata addu'ar Allah ya sa an dace
Washe gari sai wajen 12 na rana doctor ya shigo d'akin da aka kwantar da nauwara umma ce a bayan shi sai wasu nurse guda 2 tana kwance ta amsa sallamar su nan ya umarce ta da ta tashi xaune bayan ta xauna yayi wasu en dube dube sannan yayi addu'a a hankali ya fara kunce farin abin da aka rufe idon nauwara dashi
Umma sai addu'a take acikin xuciyar ta gaban ta yana fad'uwa,a hankali ya gama warware wa sannan yace "open your eyes "
A hankali ta d'an bud'e idon ta sai taga wani mugun haske da sauri ta runtse idon wannan abin ya faru ne cikin seconds d'aya xuwa biyu cikin xakuwa umma tace "nauwara bud'e idon ki mana"
Jin muryar umma yasa ta fara bud'e idon a hankali har ta gama bud'e su gaba d'aya akan umma ta xube idanun ta tayi tsiro tana kallon ta kawai can kuma sai ta fashe da wani irin kuka na farin ciki ne Ko akasin hka ohho ganin hka yasa umma ta rungume ta ita ma tana goge kwallar idon ta cikin tausayin nauwara
"umma ina gani wlh ai Kece umma na? "
Cikin dariyar farinciki tace "Alhmdllh Masha Allah, Allah mun gode ma, k'warai kuwa nauwara nice umman ki"
Dariya doctor da nurses d'in nan suka yi sai da ya dad'a duba nauwara sosai sannan suka taya ta murna tare da cewa nan da k'wanaki uku xai sallame su
Abduljabbar ne farkon wanda umma ta fara yiwa albishir nauwara ta samu lafia tana gani anyi nasarar aiki, ba k'aramin dad'i yaje ba kawai sai yace "umma ina xuwa xan kirawo ki "
Yana katse kiran sujjadar godiya ga Allah yayi sannan ya koma ya xauna xuciyar shi fal farin ciki
A b'angaren umma kuwa tana jin yace hka murmishi kawai tayi ta kirawo Abba da aunty sadiya ta sanar dasu Sannan ta kirawo fa'iza Haba fa'iza najin hka ta buga uban tsalle tare da ihu wanda yasa umma sai da ta cire wayar ta a kunnen ta don tana baraxanar kashe mata dodan kunne
Nauwara na xaune a gefe sai murmishi take yi sake Kira fa'iza tayi umma tana ganin hka ta mik'a wa nauwara wayar sun dad'e suna hira da fa'iza tare da saleem cikin tsantsar farin ciki
Haka suka cigaba da kula da nauwara har ta warke garau sannan suka basu sallama hotel d'in da suke xaune suka koma bayan sun huta suka shige makkah don gabatar da umarah
Nauwara tayi wa iyayen ta addu'a sosai na Allah ya jik'an abban ta tare da bayyana ammin ta don tana ji ajikin ta ammi tana raye bata mutu ba, sosai umma ta bata kudi don siyan abubuwan da take so komai Kala 2 take siya ita da fa'iza irin su gowns, abayat, mayafai dasu flat shoes sai arabian perfumes masu matuk'ar k'amshi sannan ta siya saleem nashi, ta juya xata tafi wajen ammi ta hango wani agogo mai matuk'ar kyau hannu tasa ta d'auke shi tana dad'a ganin shi na maxa ne sai dai yayi bala'in birge ta duba price d'in shi tayi taga kud'in shi da yawa har ta yanke tunanin mayar da wasu kayan ta d'auke shi taji umma tana cewa
"Yayi miki kyau ne nauwara?"
Kunya ce ta kamata tana d'an sunk'e kai tace "Laaa umma da yaya abduljabbar xan siyawa tsaraba Naga kud'in da yawa bari na mayar da wasu kayan sai na siya"
Cikin murmishi tace "aa d'auki kawai ba sai kin mayar da kayan ku ba "
Nan ta d'auke shi har da k'ara mishi da turare, abba ma turare ta siya mishi sai aunty sadiya ita ma turare da abayat, duk a kud'in da umma ta bata ta siya Idan ka d'ebe agogon da ta siyawa abduljabbar shi kad'ai wanda umma ta biya kud'in