← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 73

Sashe 16

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Washe gari*

Da karfe 11 na safe aminu ya yiwa su nauwara sallama Duk jikin shi a sanyaye saboda yasan hindatu ba kyale su xata yi ba Duk da ya rarrashe ta da safen nan sannan yayi mata alk'awarin xai sissiya mata abubuwan da take so kawai don kada ta axabtar dasu nauwara jinshi kawai take a xuciyar ta tace kayi ka gama wlh korar su xanyi yanda har abada baxa ka k'ara ganin su ba

Yana tafiya aikuwa ta shigo gidan tana shewa da jin dad'in tafiyar tashi su nauwara kuwa suna cikin d'akin gaba d'ayan su a tsorace suke don basu san wanne irin *K'ARSHEN WAHALA* xata gana musu ba a cikin kwanaki 2 nan ba Allah sarki su nauwara ai *Innallaha ma'assabirin* (na Zarah mansur
***********

*BARI MU WAIWAYI SU BAFFAH*

Bayan su baffah sun farfado daga suman da suka yi nan suka tarar da mugun labari wanda yayi matuk'ar k'ara tasar musu da hankali don ance gidan d'an nashi basu tarar da komai Duk ya k'one ko'ina kawai dai anyi nasarar samun gawar baba mai gadin su nauwara da wata gawar ta mace daban koda aka duba dakyar aka gane *SAFAH* ce *Allahu Akbar*

Su baffah da inna habiba sun ga tashin hankali wad'annan tsofaffin amman sun yarda da k'addarar ubanjigi hka aka sallaci su aka mik'a su gidan su na gaskiya

Ashe baba mai gadi da yaxo da niyyar taimakon su ya kamo hannun d'aya daga cikin su ashe safah ce Duk kuma a tunanin shi su nauwara suna biye dashi da yake wurin Duk Hayak'i ne basu gane hanya ba sun cikin tafiya Ashe ta wurin kitchen ne aikuwa a lokacin gas ya fashe shine ya tashi dasu safah Allah sarki rayuwa kenan Allah ya jik'an safah da baba mai gadi

Duk a xaton su har da ammi, nauwara da saleem wutar ta k'one su tun da su ba'a ga tasu gawar ba nan dai aka kammala sadakar 7 kowa ya kama gaban shi hankalin Alhj salisu kwance yake cin dukiyar su don yasan ba mai xargin shi (hmm kaji jahili an
gaya mishi hakk'in rai xai barshi ai tun a duniya Allah xai fara hukunta shi Kafin aje gaban shi inda xai yi hukuncin dai dai da abin da ka aikata Allah yasa mu dace duniya da lahira Ameeen thumma Ameeen)

?☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘??
*Written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 28~*

A cikin wad'annan kwanak'in biyun su nauwara a tsorace suke gaba d'aya basa cikin nutsuwa saboda basu san wanne irin cin mutunci hindatu ta tanadar musu ba

Sunyi matuk'ar mamaki sosai har suna tunanin ko ta canja hali ne Don har abinci take basu tana gama wa xata k'walla wa saleem Kira yana xuwa xata bashi abincin kuma sau 3 a rana gashi yanxu da yawa take xuba musu yanda xai ishe su (toh masu karatu ko dai hindatu ta canja hali ne taji nasihar mijin ta aminu)

*********

Xaune yake a kan kujera cikin office d'in nashi yana cike wasu takardu wanda aka tura su wani cos na tsawon 6 month's shi kanshi yaji dad'in hka saboda xai huta da masifar jiddah yana kammala cike wa ya ajiye ta a gefe sannan ya kwantar da kanshi kan kujera tare da lumshe idon shi yana tunanin yanda xai fara binciken yarinyar da xai aura ba mai irin halin jiddah ba, duk da yanda en mata suke kawo musu kanshi wasu Don ya aure su wasu kuma kawai jikin su suka bashi kyauta don yayi lalata dasu

Ko kallo basu isheshi ba saboda ya tsani zina ba k'aramin tsana ba kuwa yayi wa masu yin ta ba shi yasa a kullum yake rok'ar ubanjigi akan ya k'are shi da kusantar ta masu yi kuma Allah ya shirye su, kiran waya ne ya shigo wayar shi a hankali ya bud'e idon shi tare da jan d'an k'aramin tsaki mtswww d'aukan wayan yayi tare da sawa a kunne ya fara da sallama daga can b'angaren umma ta amsa mishi sallamar tashi cikin ladabi ya gaida ita ta amsa mishi tukunna ta fara yi mishi maganar da ta sa ta kirawo shi

"daman abdul abin da yasa na kirawo ka saboda ina son sanin me yasa jiddah tace ka canza mata mota kace baza ka canja ba? "

Haba tuni ran en maza ya 6aci wlh ba don umman shi ce ba sai ya katse kiran amman ya xai yi mahaifiya ce don hka ya d'an sasauta ranshi Kafin yace "umma ki share jiddah wlh ta fiye matsala da yawa last month fa na canja motar ta gashi kuma akwai motocina fah a gidan tana d'aukar kowacce tayi amfani da ita idan tana ra'ayi"

"duk naji ka kuma nasan da hka kawai ka canja mata nace"

"toh wai ina kud'in ta da take samu kowanne month ina take kaisu? "

"ina ruwan ka da kud'in ta, tunda dai hakk'in ta yana kan ka "

Cije leb'en shi yayi cike da jin haushin jiddah bcoz tana son ta dunga had'a shi da mahaifiyar shi amman xai rabu da ita ta gama iskan cin ta xata gane bata wayo wlh

"naji kayi shiru ko baza ka canja ba mata ba nasa ni"

"ya xanyi tunda ta had'a ni dake xan canja mata xata samu sak'on wajen abdulkareem Don ni tafiya xamu yi wani aiki tsawon 6 month's daman yanxu nake son kiran Ki na sanar da ke sai na dawo xan xo kano amman don Allah umma kiyi hak'uri naga kamar ran ki ya 6aci"

Tausayin d'an nata ne ya kamata tace "ba komai abdul Allah ya taimaka yasa a gama a sa'a, Allah ya kai ku lfy ya dawo daku Lfy Allah ya kare min kai yayi mata albarka ya baka 'ya'ya masu albarka "

Sosai yaji dad'in addu'ar da mahaifiyar shi ta yi masa da hka suka yi sallama Sannan ya kirawo abban shi ya sanar dashi shima ba k'aramin addu'a yayi mishi ba

********

A yau ake sa ranar dawowar aminu daga aikin da aka tura shi hindatu tun safe take gyaran gida ana had'a wa miji abubuwan ci da nasha har aka gama tayi wa yara wanka ita tayi suka shirya fes dasu ta fito ta bawa su saleem abinci suka ci suka koshi har suka barshi don yanxu har sun d'an farfad'o daga mugun ramar da suka yi

*4:30*

Su nauwara na xaune a d'aki saleem yana bata labari sai dariya suke ta shigo d'akin nasu cikin murmishi amman ni da ganin murmishin nan nasan shine ake Kira dana mugunta

"Idan baxa ku samu damuwa ina son kuxo ku rakani jifatu xan siyi fruit da drinks nawa sun k'are gashi aminu yana hanya"

Gaban nauwara ne ya fad'i da jin abin da tace sai taji sam bata yarda da abin da tace ba don hka tace "Laaa aunty da kin barmu anan Kinsan xaki sha wahala dani tunda ba tafiya nake ba? "

Harara ta xabga mata a fakaice Kafin ta saki murmishi tace "ba wani wahala gashi har da su usman xamu je kai saleem ka turo ta waje ina jiran ku"

Tasa kai ta fice hankalin nauwara ba k'aramin tashi yayi ba gashi ba yanda xasu iya hka saleem ya turo ta dukka jikin su a sanyaye yake har sun fito ita da yaran ta dakyar suna jiran su nan ta taimaka wa saleem suka sata a mota sannan kujerar ta ta suka sata a boot

Cikin jin dad'i ta fara driven d'in motar har suka fice daga unguwar ni da naji tace jifatu xasu je na kwalalo ido don ganin ai gaba d'aya ba hanyar da xata sada ta da jifatu tayi ba ta dauki hanyar da xata Kai ta................

(masu karatu toh ko ina hindatu xata kai su nauwara?)

???☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 29~*

Hanyar da xata dauke ke ta xuwa tashar mota nan tayi dasu sai da ta shiga cikin tashar tukunna tayi parking tare da fito wa kamar gaske ta fito wa da nauwara kujerar ta sannna ta d'ora ta akai cikin murmishin mugunta tace "saleem fito mana "

Yaron cikin sanyin jiki ya fito daga motar yaran ta suna ciki basu fito ba dummm gaban nauwara yayi mugun fad'uwa jin ana cewa hajia ina xuwa hka gashi sai fad'ar sunayen garuru da akeyi hkan yasa xuciyar nauwara karye wa tare da ayyana mata Anan tashar mota ce wasu hawaye masu xafi suka fara xubo mata a fuskar ta Bata damu ta goge ba cikin haka taji hindatu ta kwashe da dariyar mugunta sannan tace

"yarinya ai yanxu kika fara kuka wlh, yau dai na yadda kwallon mangoro na huta da k'uda kinga daga yau kun fita a rayuwar mu"

Kukan nauwara ya tsanan ta ita da saleem cikin ginshik'in kuka tace "Don Allah aunty kada ki mana Hka Ki tausaya mana bamu da inda muka sani a fad'in garin nan sai ku pls "

"kamar yanda baku Sanmu har kuka yarda da aminu to kuje ku nemi wasu Don nan Inda na kawo ku shine dai dai da rayuwar ku sai ku cigaba da rayuwa anan har ku mutu ko kuma wani mai tausayin ya taimaka ku "

Laluben inda hindatu take ta fara har tayi nasarar riko gefen mayafin ta har ta bud'e baki xatayi magana hindatu tasa hannu ta make hannun nauwara da karfi har sai da ta saki er k'ara saboda xafin da taji ta cigaba da kukan ta saleem ya rungume ta shima yana nashi kukan sunyi matuk'ar ban tausayi duk wanda ya gansu a hka sai ya tausaya musu amman hindatu ko a jikin ta K'arshe ma shige wa tayi cikin mota tayi tafiyar ta xuciyar ta cike da farincikin ta rabu dasu nauwara wani 6arin na xuciyar kuma yana tsoron tunkarar aminu wacce amsa xata bashi idan ya tambaye ta ina su nauwara?, k'wata k'wata sai yanxu tunanin hkan ya xo mata hka ta tafi gida tana tunanin amsar da xata bawa aminu...
Chapter 16 · 0% Book details