← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 73

Sashe 10

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matan shi 2 uwargidan itace hajia Fatima mai yara 4 ta farkon itace Asma'u mai bi mata abduljabbar sai kausar da FA'iza, amman aunty asma'u tayi aure tana xaune a abuja da yaran ta 2 hanan da khalipa sai kausar mai d'a 1 wanda aka samishi sunan kakan shi Wato baban kausar suna kiran shi da naufal, FA'iza kuma ko secondary bata kammala ba sauran 1yr ta gama

Amaryar shi kuwa hajia sadiya Allah bai bata haihu wa ba har yanxu amman ta rik'e 'ya'yan mijin ta tsakani da Allah tana son su don hka xaman lfy sosai ake a gidan Alhj ibraheem Idan ka shiga gidan baxa ka tab'a banbanci yaran wane daga ciki ba sai dai hajia sadiya tasu taxo d'aya da abduljabbar don d'an d'akin tane tana ji dashi jinin su ya had'u fiye da sauran yaran komai tace aabduljabbar har maman shi wato hajia Fatima wadda suke kiran ta da umma ta dunga cewa ke Idan xa'a yi magana komai Kice abduljabbar sai kace shi kad'ai ne d'a a gidan ita dai aunty sadiya da yake hka suke kiranta sai dai tayi dariya kawai

Abduljabbar tun tashin ya kasance yaro ne mai hankali da nutsuwa ba ruwan shi da shiga harkar da ba tashi ba gashi ya tsaya yayi ilimin addini sosai akwai kyauta don abin shi bai rufe mishi ido ba ya samu tarbiyya mai kyau bashi da tarin abokanai sam abokanan shi 2 abdulkareem wato k'anin mahaifin shi sai muh'd abokin aikin shi don tare suka yi karatu har xuwa yanxu da suke aiki

Bayan wad'annan halayar abduljabbar dana fad'i yana da wasu halayar ta rashin son magana ga shi baya d'aukan raini wajen k'ananan shi don ko aunty asma'u cewa yake Ae shine babba tunda shi namiji ne mai rik'e gida ita kam tana k'asan wani, tun yana yaro yake sha'awar xama soja da Wannan burin ya tashi don hka mahaifin shi ya tsaya tsayin daka har yakai da cika mishi burin shi har ya kammala karatun shi ya fito da kyakkyawan result d'in shi wanda mahaifin shi ba k'aramin jin dad'i yayi ba, har yakai da ayanxu yana da mukamin Captain saboda kwazon shi a abuja yake aiki .

Koh 5month's baiyi da yin aure ba auren xumunci akayi musu er gidan kanwar umman su ce take masifar son shi wato jiddah tun tana nuna mishi alamu har yakai ta furta mishi amman bai kula ta ba har ta gaji ta samu umman shi take sanar da ita aikuwa ba b'ata lokaci akayi auren duk da ba'a son ranshi akayi hkan ba ,amman yayi wa mahaifiyar shi biyayya ya aure ta Ko ba komai ya rage xafi da ita Kafin ya samu yarinyar da ta kwanta mishi a rai ya auro don yana da wannan burin

*******
Wace jiddah matar captain abduljabbar 'yace ga malam Aminu da mama hajara ita kad'ai iyayen ta suka mallaka tayi ilimin boko har xuwa degree duk da iyayen ta basu da karfi amman sun bata ilimi gashi umman su abduljabbar tana taimaka mata sosai

A rayuwar jiddah babu abin da ta tsana kamar talauci ta tsani talaka (hmmm ta mance mahaifin ta talaka ne) shi yasa gaba d'aya tarin k'awayen ta ya'yan masu kud'i ne kuma bata tab'a nuna musu iyayen ta na ainahi sai dai ta kaisu gidan su abduljabbar, gashi ta tsani kishiya a rayuwar ta don aunty sadiya ma kishi take (kishiyar umman abduljabbar fah kuji karfin hali wajen jiddah) toh ya kenan daga lokacin da ta fuskanci abduljabbar yana da ra'ayin k'ara aure???

*Aishat A muh'd*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*NA*

*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

*~pg 17~*

Zaune yake akan dinning table yana breakfast k'wata2 Ya kasa cin abincin sai ruwan lipton yake sha shima d'in bai yi mishi ba saboda ya tsani en aiki suyi mishi abinci mugun kyankyami ne dashi gashi Allah ya had'a shi da mata mai shegen son jikin jaraba ji yayi xuciyar shi tana tashi dole ya ajiye cup d'in hannun shi na ruwan lipton d'in had'e da shegen Jan wani tsaki a xuciyar shi kuma yana tunanin sake aure kuma sai ya nutsu ya xaɓo wadda ta K'ware a iya abinci

Tsakin da ya ja shi ya ankarar da jiddah da take tacin abincin ta hankali kwance kallon shi tayi kafin tace

"Lfy kake jan tsaki?"

Wani kallo ya watsa mata mai cike da jin haushin ta kafin dakyar ya iya bud'e baki yace

"ai dole ki tambaye man tun da Kinsan bana son girkin mai aiki nafison kiyi min da kanki but kin k'i jin magana"

"kai ma dai my darling akwai ka da mai da agogo hannu kasan ban iya girki how many times kake wannan maganar but ina fad'a maka gasky fah"

"okay tunda Hkne xan nemi yarinyar da ta iya girki na aura wannan kad'ai shine mafita, tun da girman kai ya hana ki tsayawa FA'iza ta koya miki "

Tun da ya fara maganar take watso mishi harara cike da jin haushin shi shima a fusace ya K'arasa maganar tashi mik'e wa tsaye tayi cikin masifa tace

"wllh baka isa kayi min kishiya kai nawa ne ni kad'ai Banga shegiyar da ta isa ta shigo gidan nan ba kuma girki ne baxan koya ba saboda nayi aure ne don na huta ba don.................. "

Kafin ta K'arasa maganar ta jin saukar wani kyakkyawan mari taji a fuskar ta ba shiri tayi shiru akwai kuwa yayi nasarar fasa mata baki don jinine ya fito daga bakin na ta ai kuwa ganin jini yasa ta kurma wani uban ihu tana kuka dakyar ya iya bud'e baki yace mata saboda tsananin bacin rai

"as frm today ki tabbatar wannan shine last da xaki dunga yi min nonses shouting a kunne stupid gal"

Yana gama fad'in hka ya fice daga gidan cike da bacin ran da jiddah ta hassada mishi,ya bar Jiddah a kwance a falo tana kururuwar kuka kamar wadda aka aiko mata da sakon mutuwar iyayen ta.
direct wajen motar shi ya nufa Joseph dake xaune da mai gadi suna hira yana ganin boss d'in shi ya fito cikin bacin rai da gudu ya K'arasa wajen shi tare da bud'e mishi mota ya shiga shima ya xauna a sit d'in driver key ya sawa motar suka fice daga gidan harba motar yayi kan titi sannan cikin tsoro yace

"boss ina xamuje???"

Shiru yayi sai da ya kwashi wajen 5mint kafin ya iya cewa "gidan mu xaka kai ni"

"okay boss"

Daga hka yaja bakin shi yayi shiru saboda yana tsoron sake wata maganar ya janyo wa kanshi wani punishment d'in don boss ba sauk'i baya d'aukan raini.

A bangaren jiddah kuwa dakyar ta iya yin shiru ta janyo tissue akan dinning table ta goge jinin da ya fito wajen har ya d'an kumbura waya ta janyo number d'in umman abduljabbar ta dialing tana jin umma ta d'auka nan ta fashe da kuka tuni umma ta rikice tana tambayar ta lfy dakyar ta iya xayya ne mata abin da abduljabbar yayi mata har da Karin wani abun nan umma ta cika tayi fam da ita tace bari yaxo ya same ta anan tayi hangin up d'in wayar ta ajiye tana mai sauke ajiyar xuciya Kafin ta tashi ta shige bedroom wanka tayi ta shirya cikin wata super holland dinkin riga da siket ya kamata tsam ta bulbule jikin ta da turare tare da yafa wani mayafi K'arami kamar ba matar aure ba wani uban hill ta sanya da wata katuwar handbag wayar ta da key d'in mota ta d'auka fice wa tayi daga gidan ta tafi wurin aikin ta (sorry masu karatu namance ban fad'a muku jiddah tana aiki ba, ita ma'aikaciya ce diamond bank).

Abduljabbar yana shiga falon umma da sallama dakyar ta iya amsa mishi sallamr saboda tasan mahimmancin sallama ba don hka ba ko uhm baxa tace mishi ba saboda ya b'ata mata rai dukan mace ai ba d'abi ace mai kyau ba, jikin shi ne yayi sanyi ganin yanda umma ta had'e rai xube wa yayi a k'asa yana gaida ita nan ta shiga yi mishi fad'a sosai shi dai hak'uri yake bata kawai don in ranshi yayi dubu ya b'aci saboda baya k'aunar a had'a shi da mahaifiyar shi nan dakyar ya bata hak'uri ta hak'ura daga nan part d'in auntyn shi ya shige wato aunty sadiya kishiyar umman shi don yasan yanxu abba yana office

Jagwab ya xube kan kujera cike da bacin rai kallo d'aya auntyn tashi tayi mishi ta gane ran en maxa ya b'aci yau bata yi mishi magana ba sai da ta had'a mishi lafiyayyen breakfast don tasan bai wani karya ba idan da sabo ta saba Idan yana gari sai yaxo gida yake cin abinci sam baiyi dacen mata ajiyar xuciya ta sauke cike da jin tausayin shi tace

"ya kamata kaci abincin mayi magana daga baya"

Hka ya ciccusa abincin ba don dad'i ba duk da favourite food d'in shine b'acin ran da yake tare dashi shi yasa ya kasa cin abincin cikin jin dad'i da hka ya gama ci tissue ya d'auko ya goge bakin shi Kafin ya nutsu ya kwashe yanda suka yi da Jiddah da k'arar shi da takawo wajen umma cikin tsananin tausayin shi aunty tace

"kayi hak'uri abduljabbar wataran sai labari a gaskia bata kyauta ba amman dukan da kayi mata sam bai dace ba ka daina saurin duka sannan idan kana da ra'ayin sake aure ni baxan hana ka ba saboda hkan raya sunnah ne kuma kai Allah bai had'a ka da mace ta gari ba ka cigaba da hak'uri d'ana"

Da hka ta lalla6a shi har hankalin shi ya kwanta kafin ya fice daga gidan office d'in abban shi ya shige............

**********

La'ilaha illallahu muhammadun rasulillahi sallalahu alaihi wassalam, la haula wala quwwati illa billahil aliyar axeem da wannan addu'ar nauwara ta farka a matuk'ar raxane sai dai me kafar ta ce tayi mata wani irin nauyi gashi wani irin duhu take gani a idon ta duhu dulum Don hka cikin rud'ewa ta fara kiran sunan saleem da karfin gaske da sauri saleem wanda yake a gaban ta yace
Chapter 10 · 0% Book details