← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 73

Sashe 39

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A parlour ya tarar da jiddah ta xabga uban tagumi tsaya wa yayi yana kallon ta xuciyar shi cike da tausayin ta a hankali ya K'arasa inda take hannu yasa ya janye tagumin da tayi tana ganin shi ta kwanta a jikin shi ta fashe da kuka sosai ta bashi tausayi amman hkan baxai sa ya hak'ura da auren da xai yi ba ko rarrashin ta bai yi ba sai da taci kukanta ta more sannan ya d'an rarrashe ta ganin hka yasa xata bud'e baki tayi magana ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru Sannan yace "kiyi hak'uri da abin da xakice min sai anjima yanxu na gaji ina buk'atar hutu kije ki kawo min wani abun mara nauyi naci yunwa nake ji"
Yana gama fad'in hka ya tashi ya nufi bedroom d'in shi kwafa tayi tana cewa "wlh sai na koyawa yarinyar da ta aure ka hankali sai na nuna mata ba'a had'a miji da jiddah ba boka ba malam kissa ma kad'ai ta isheta da kafar ta xata bar gidan nan " Mtsww taja tsaki tukunna ta mike kitchen ta nufa ta ga mai dafa musu abinci ya gama duba wa tayi don taga abin da ya dafa jellop d'in taliya ta debar mishi wadda taji kifi da nama ga vegetables sannan ta had'o mishi da lemo da ruwa ta d'auka dakin shi ta shige ta tarar ya fito daga wanka yana d'aure da farin towel ya goge gashin shi da wani k'aramin towel d'in kunnen shi mak'ale da waya ya rik'e ta a tsakanin kafad'ar shi yana magana sai faman doka murmishi yake takaici ya ishi jiddah ga wani irin kishi da ya lullu6e ta abincin hannun ta ta ajiye akan k'aramin table d'in d'akin a fusace ta juya xata tafi jin ko kula da ita bai yi ba caraf taji ya kamo hannun tare da janyo ta jikin shi sai da ya d'auki en mintuna tukunna ya kashe wayar Har da sakin wata ajiyar xuciya sam ya mance da wata jiddah a jikin shi sai da yaji shashshak'ar kukan ta Sannan ya dafe kanshi yana fad'in auuch! cak ya d'auke ta ya d'ora ta kan bed ya shiga yi mata abubuwan da dole ta russuna ai kuwan K'arshe har dariya ta dunga yi kamar ba ita ba yana d'an murmishi yaja hancin ta yana cewa "Yah ko da akwai wani abun dafatan kin koshi Idan baki koshi ba sai na cigaba don ba gajiya nake "
Yana fad'i mata hkan yana d'aga mata gira murmishi tayi ba dole ta dunga kishin abduljabbar ba mutumin da yasan ta kan mace kullum kamar k'ara mishi kyau ake tunawa da auren da xai yi nan da en K'wanaki yasa ta fara xubar da hawaye kallon ta yayi tausayin ta ya kamashi don yasan abin da yake damunta bai wuce kishin shi ba shi kanshi yasan jiddah akwai shegen kishin tsiya

D'aukan ta ya sake yi suka shiga toilet don dai duk don taji dad'i shi yasa ya sauke fushin da yake da ita taji da abu d'aya kada abun yayi mata yawa

Bayan sun fito a toilet d'in ya gyara jikin shi tare da sanya wani three quarter fari ne sol da wata black d'in riga mara hannu ya fesa perfumes Kala Kala sannan ya xauna ya d'an tsakuri abincin Kad'an yaci yana bawa jiddah a baki to itama batayi musu ba ta kar6a tana ci saboda yunwar take ji don bata iya cin abinci kirki saboda ta sawa ranta kishin tsiya

Suna gama ci ya d'an yi tsalle kamar sau goma tukunna ya sha ruwa ya kwanta da yake a gajiye yake nan da nan bacci yayi awon gaba da shi yayi da jiddah ta xuba mishi ido kamar yau ta fara ganin shi xuciyar ta sai sak'a mata abubuwa take

Misalin karfe 4 na yamma mutane suka fara taruwa a gidan su Abduljabbar k'awayen umma ne da na aunty sadiya sai nasu aunty asma'u da aunty kausar sannan nasu fa'iza da amarya nauwara goggagun en boko kowa ka ganshi da shiga ta Kece raini wannan yana wane wannan har da mameen jiddah da k'awayen ta itama, acikin k'awayen amarya can na hango irin su sadeey saNaz, neena cool, miss zahra Gasu nan dai da yawa sai iyayi ake xuba wa 😜

A garden di'n gidan xa'a yi an gyara shi yasha decoration wajen yayi kyau sosai, ango da en abokanan shi suka k'araso gidan yasha wata tsadaddiyar shadda light pink irin d'inkin xamani takalmi da agogo bak'ak'e yayi amfani dasu hular kanshi baka ce da ratsin pink da fari ajiki sai k'amshi yake xubawa ba k'aramin kyau yayi kannan nashi da sajen nan sun sha gyara sae sheki suke da d'aukan ido hular nan an turo ta gaban goshi sai faman xabga murmishi yake yana xuba ido yaga ta Inda nauwara xata fito Wowwww masha Allah abin da ya fad'i kenan ganin aunty asma'u ta fito rik'e da hannun nauwara tasha wani tsadadden swiss less kalar pink da touch d'in black ajiki takalmi da poss di'n hannun ta bak'ak'e ne nad'in kanta da aka yi mata shima pink nd black haka sark'a da d'an kunne har abin hannu gashin kanta yasha gyara an xubo mata dashi baya tasha make up sosae tayi masifar yin kyau har suka k'araso inda yake kanta a sunkuye tak'i ta d'ago dashi sai da aunty asma'u ta d'an ta6a shi sannan ya dawo hayyacin shi kwashe wa da dariya suka yi ita da abdulkareem "Wannan kallon fah kada kasa ta fad'i fah " Cewar aunty asma'u tana yi mishi dariyar shak'iyan ci hararar ta yayi hannun shi ta kamo ta had'a da hannun nauwara lumshe idon shi yayi jin tattausan hannun ta d'aya hannun shi yasa ya d'ago kanta lumshe ido tayi duk kunya ta rufe ta kamar ta nutse a k'asa take ji k'asa jure wa yayi ya fara matso da fuskar shi saitin tata, tuni aunty asma'u ta fahimci abin da yake niyyar yi da sauri ta tafa hannu tana cewa "Wayyo ni asma'u abdul wannan wacce irin rashin kunya ce a gaban mutane kake kok'arin yin...... "
bata K'arasa fad'i ba ganin umma ta k'araso wajen tuni ya janye fuskar shi tare da hararar asma'u ganin ta katse mishi hanxari dariyar mugunta suka yi mishi ita da abdulkareem yayin da kunya ta ishi nauwara "ku fah kawai ake jira kuka xauna anan"cewar umma Hka ya janyo hannun ta suka nufi inda xa'a yi kamun kujera d'aya ce irin mai fad'in nan Kad'an Hka suka xauna slow music ne ke tashi a wajen sunyi matuk'ar dace wa da junan su Hka kowa yake cewa har aka fesa wa ango da amarya turare suka cigaba da kamun su har xuwa lokacin gaf da mangariba tukunna aka tashi mutane sun fara tafiya abduljabbar yak'i sakin nauwara aunty asma'u kuwa k'in tafiya tayi don ganin yanda yake rawar jiki tasa mishi ido hararar ta yayi yana cewa "kin fiye sa ido wlh ki tafi harkar gaban ki k'i kyale ni da mata ta "
"Ahayye yaro Allah baxan tafi ba kafata kafar nauwara"cewar aunty asma'u "selfie kawai xamu d'auka yanxu xata taho fah ni ba wani abun xan yi mata ba"
"Duk da hka ayi a gabana"
Hka dai ya share aunty asma'u ya dauko wayar shi yana cewa "oya gyara habibty xamu yi selfie "
A kunyace ta d'ago da kanta shi kuwa ya matso da kanshi kusa da kanta ya d'an kwanta a jikin ta Kad'an ya d'auka sunyi kyau a photon aunty asma'u ma sun birge ta sai da tayi musu pictures tukunna ya tashi tare da sunkuyo wa saitin fuskar ta ya sakar mata kiss a kumatu tare da yin gaba hangame baki aunty asma'u tayi ganin rashin kunyar abduljabbar tana cewa "Lallai abdul daman Hka kake?" shi dai bai kula ta ba ganin an shiga masallaci ita ma janyo hannun nauwara suka yi cikin gida dakyar take tafiya saboda kunya aunty asma'u tana ce mata ta saki jikinta ta daina jin kunyar ta ita yayar tace...... .....

Aishat A muh'd 😘
☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd 😘

*~Pg 64~*

Aunty asma'u har d'akin su ta rakata ganin yanda take jin kunya tana shiga fa'iza da sauran k'awaye da en uwan su fa'iza sa'annin su nauwara enmmata suka saki shewa suna ga amarya ga amarya kowa yana kok'arin janyo ta don ta xauna kusa dashi aunty asma'u tace "Allah Kuyi mata a hankali kada ku fad'ar da ita kunsan halin dai abdul yanxu yasa ku tsallen kwad'o " wata a cikin su Mai suna hafsat tace "Haba aunty ai muma bama so taji ciwo ba mukai amarya ba lafia ta kasa cin amarce "
Shewa suka saki tare da tafawa fa'iza tana dariyar mugunta tace "Hkne hafsat kada yayan mu ya kasa cin amarci yanda ya kamata "
Dariya suka tuntsire da ita aunty asma'u ta harari fa'iza tana cewa "Allah ya shirye ki fa'iza ai ni naso wlh a had'a bikin nan da naki ko ma huta "
"Haba aunty asma'u Kinsan ni yarinya ce me na sani ai kwa tausaya min na girma tukunna " pillow aunty kausar ta cilla mata yayi da aunty asma'u ta kawo mata bugu da sauri ta kauce tana 6uya a bayan nauwara nan dai suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali da nishadi

Da sauri ta fito daga toilet tana d'aure da babban towel jin sai Kiran ake wayar ta ake Mik'o mata wayar fa'iza tayi tana murmishi tace "ango ne fah yake kira"
Warce wayar ta tayi tare da hararar fa'iza murguda mata baki tayi tana kok'arin d'auka wayar ta katse don hka sai ta xauna akan rest chair tana Kok'arin kiran shi jin ta shiga yasa ta gyara kwanciyar ta tana jira ya d'auka
Chapter 39 · 0% Book details