← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 73

Sashe 30

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk iya kok'arin da doctor yayi kada cikin ya xube amman kash ya riga ya fice nan suka yi mata wankin ciki bayan ta farfad'o daga suman tayi sunyi mata allurar bacci don ta huta don ba k'aramin wahala tasha ba aka sanya mata drip na ruwa dana jini don tayi bleeding sosai
Yana shigo wa office d'in abduljabbar ya mik'e tsaye yana cewa "Ya doctor dafatan baby na yana nan?"
Cikin tsananin tausayin shi doctor yace "kwantar da hankalin ka captain kayi hak'uri da abin da xan fad'a maka "
D'an kallon abduljabbar yayi ya ga gaba d'aya shi yake sauraro don hka ya cigaba da cewa "I'm so sorry captain cikin da ke jikin matar ka ya xube"
"what! ?"
Abduljabbar ya fad'a da karfi cikin tausayin shi doctor ya cigaba da cewa "duk iya kok'arin mu da muka yi don kada ya xube amman sai da ya fita"
"toh mene mussababin fitar shi?"
Cewar abduljabbar shiru doctor yayi Kafin daga bisani yace "A binciken da muka yi ya nuna mana maganin xubar da ciki tasha Mai karfi har ya d'an ta6a mahaifarta wanda kafin ta samu wani cikin sai an.......... "
"is okay doctor "
Abduljabbar ya katse doctor ya cigaba da cewa "thank u for everything"
Daga hka ya fice daga office d'in cikin wani matuk'ar tsantsar 6acin rai wanda ban ta6a ganin abduljabbar a ciki ba fuskar shi tayi ja saboda 6acin rai motar shi ya fad'a yana fita daga asibitin hanyar airport ya nufa yana xuwa yayi sa'a akwai jirgin da xai tashi adai dai time d'in don hka ticket ya siya sai da xai shiga jirgin ya kirawo abdulkareem yaxo ya d'auki motar a airport bai jira ya fad'i wani abun ba ya shige cikin jirgin har suka isa abuja jirgi yayi landing a k'asa ya kirawo Joseph yaxo ya d'auke shi a mota

Yana parking ya fito direct toilet ya shige ya cire kayan jikin shi shower ya sakarwa kanshi ruwan sanyi yana xuba a jikin shi yayi da xuciyar take wani irin turiri na 6acin rai why! why!! jiddah da xaki yi min asarar d'ana jinina xaki xubar min kamar wani d'an shege bango ya kai wa naushi cikin fusata kamar shine yayi mishi laifin nan fa ya dunga dukan bango har hannun shi ya fara jini sai da yaji kiran sallahr isha'e sannan ya fito ko masallaci bai iya xuwa ba agida yayi sallahr shi ya janyo alqur'an ya fara karatu a hankali yaji xuciyar shi tana sanyi

******

*KANO*

Jiddah bata farka ba sai wajen 9 na safe ba kowa a d'akin sai wata nurse ita ta taimaka mata tayi wanka sannan doctor ya shigo ya Kalli nurse di'n yana cewa "d'an bani minti 5 xanyi magana da ita"
"okay sir! "
Ta fadi hka tare da tashi ta fice kallon shi ya dawo dashi kan jiddah ya fara da cewa "madam me ya kake da shan maganin xubar da ciki? "
Harara Jiddah ta galla mishi sannan tace "ina ruwan ka dani kawai ka tsaya a matsayin ka malam? "
Girgixa kai kawai yayi sannan yace "sakamakon maganin da kika sha toh ya ta6a miki mahaifar ki ke da haihuwa sai ikon Allah kuma"
A fusace tace "Ehh naji sai me kafa dame ni da surutu "
Kallon ta yake cike da mamaki ita bata son haihuwa aka haife ta ai 'ya'ya rahma ne ya juya kawai ya fice xuciyar shi cike da tsananin tausayin abduljabbar bai yi dacen mata sam Allah ya shirya masu irin Wannan halin

Bammmm aka banko kofar room d'in da jiddah da take har sai da ta tsorata ta dauka abduljabbar ne sai had'a ido suka yi da umma fa'iza da nauwara suna bayan ta abin da ya bata mamaki ya kuma kid'ima ta ganin umma tana hawaye Kafin ta ankara taji saukar wani lafiyayyen mari a fuskar ta dukka 6arin biyun ba k'aramin firgita jiddah ta yi ba ganin umma ce ta mare ta cikin fad'a umma ta fara cewa "tur da ke jiddah da mai irin halin ki abin da xaki saka min dashi kenan ko kije kiyi tayi duniya ce ta ishe ki riga da wando "
Tana gama fad'in hka ta juya ta fice a fusace d'ago kai tayi taga fa'iza da nauwara suna hararar ta 6acin rai kwance a fuskar su daganin yanda idon su yayi ja kasan sun sha kuka cikin tsawa tace "uban me kuke min aka xaku fita ko sai naci uban ku? "
"wallahi baki ji dad'in ki ba "
Cewar fa'iza yayin da nauwara cike da tsanar jiddah taja tsaki tace "Allah ya shirya ki wllh tun wuri ki tuba ga Allah tun......... "
A guje suka fice daga d'akin Kafin ta K'arasa fad'i ganin jiddah ta yunk'uro xata tashi "shegu en iskan yara da ku tsaya mana "
Cewar jiddah tana kok'arin koma wa ta xauna taji an rufe ta da duka ta ko'ina a tsorace ta d'ago kanta sai ganin Maman ta tayi tana kuka tana dukan ta "kin cucu kanki jiddah kinci amana kin butulcewa er uwata wadda ta rik'e ki tsakani da Allah shine da rashin mutunci kije ki xubar da ciki toh wallahi ki sani Idan abduljabbar ya sake ki sai dai ki nemi wasu iyayen ba mu ba tunda haifar ki kawai muka yi amman koman ki yaya fatyma ce ta mayar dake hka "
nan fah mama ta dunga dukan jiddah tana xagin ta dakyar nurse's suka kwace ta mama ta fice daga asibitin akabar jiddah cikin wani mawuyacin hali Ko wa ya juya mata baya Wayyo Allahn ta acikin Wannan yinin tayi nadama yafi sau dubu na abin da ta aikata yanxu idan abduljabbar ya sake ni ya xanyi da dumbin son da nake mishi (Hmmm jiddah sai yanxu kika tuna da son da kike mishi ba Kya son had'a jini dashi Wannan ai shine da nasani k'eya ce inji hausawa)

*Aishat A muh'd*😘

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

_wannan page d'in naki ne k'awata *khadijah niger (neena cool)* Marubuciyar littafin *deejah* Allah ya k'ara basirah, Allah ya bar xumunci ameeen_❤😘

*~Pg 53~*

Cikin k'wanaki 2 Jiddah tayi nadama yafi sau ba iyaka gata a kwance gadon asibiti ba wani d'an uwan ta da yaxo jinyar ta sai farida k'awar ta duk tabi ta rame sai da doctor ya tabbatar mata gaf take da kamuwa da hawanjini Sannan ta sasauta wa kanta satin ta d'aya aka sallame ta ta dawo gida

Kullum da tunanin wanne hukunci abduljabbar xai yanke mata amman shiru bai xo ba tun tana fargaba har ta watsar da abin ta koma bakin aikin ta

Tun da abduljabbar ya tafi bai waiwayi kano ba wajen 3 month's da faruwar abun amman yak'i xuwa sai dai suyi waya da en uwan shi ganin hka yasa abba ya yanke shawarar kiran shi

Yana xaune a office yana daddana laptop wayar shi ya fara k'ara ganin sunan abba yasa shi d'auka cikin girmama wa ya gaida shi bayan ya amsa ya d'ora da cewa "abduljabbar ka mance kana da iyalai ka tsallake tsawon wata 3 baka dawo gida ba, naji komai a wajen umman ka jiddah bata kyauta ba taxo har gidan nan ta bamu hak'uri tayi nadamar hkan kuma muna buk'atar ganin ka,ka taushi xuciyar ka kuma kada kace xaka rabu da ita tasan ta *tafka babban kuskure* (littafin rash kardam) kuma ta amshi laifin ta tayi alkawarin baxa ta sake mai mai ta hkan ba" nan abba ya rarrashe sosai sannan daga baya yace yana nan tafe da hka suka yi sallama

A hankali take sauko wa daga upstairs tana sanye da wata shadda blue d'inkin riga da siket tasha aiki shaddar light make up tayi ba k'aramin kyau tayi ba sai yanxu ta tashi daga bacci umma fa'iza da saleem sun fita unguwa k'wata k'wata hankalin ta yayi kitchen saboda yunwar da take ji gaisa wa sukayi da er aikin umma Sannan ta fara kok'arin dafa indomie guda d'aya ta tasha vegetables sannan ta soya kwai guda hud'u juye wa tayi a plate ta d'ora Kwan a gefe sannan ta bud'e frige ta d'auko fresh milk ta fito daga kitchen d'in, kasa K'arasa wa dinning table tayi ta xauna acikin falon ta d'ebo abincin xata kai bakin ta suka had'a ido da abduljabbar cikin mamaki ta tsaya kallon shi, duk abin da take tun saukowar ta yake kallon ta cike da so da k'aunar ta, ba k'aramin kyau tayi mishi ba, a b'angaren nauwara ita ma xuba mishi ido tayi yayi masifar k'ara kyau xuciyar ta tana wassafo mata wani abun da sauri ta kawar da wannan tunanin a axuciyar ta kusa da shi taje ta tsugunna tana cewa "Yah abduljabbar sannu da xuwa ina yini? "
Maganar da tayi ta dawo dashi hayyacin shi yace "lafia, ina umma? " "uhm sun fita unguwa ne "Cewar nauwara daga hka ta tashi ta dawo kan kujera duk uwar yunwar da take ji sai ya kasance ta kasa sakin jiki taci abincin saboda kunyar shi take ji ahankali ta tsinkayi muryar shi yana cewa "yi sauri ki gama ci ki dafa min wani abun yunwa nake ji "
Da sauri tace "toh "
Kasa cin abincin tayi sai kawai ta nufi kitchen cikin sauri da K'ware wa ta shiga shirya mishi abinci shinkafa ta dafa mishi da miyar kwai da hanta sai costlow da ta had'a mishi ta shirya a babban tire ta dauka a dinning table ta shirya mishi sannan ta d'auko mishi lemo da ruwa tukunna ta K'araso inda yake xaune yana sarrafa wayar shi tace "angama shirya komai Yah abduljabbar "
Sai da ya d'auki en mintuna tukunna ya mik'e wajen dinning table ya nufa ya xauna da sauri ta k'araso tayi serving d'in shi tana gamawa ta bar wajen
Chapter 30 · 0% Book details