← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 73

Sashe 3

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye take cikin wata gown d'in shadda dark blue tasha make up Sosae tayi masifar yin kyau d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosae sai tayi amfani da sark'a white mai touch d'in blue a jiki ta sanya white shoes nauwarah kenan sarkin son gayu kenan suna masifar kama da ammin ta don ita ta kwashe kusan kyan nata don tafi safah da saleem kyau shi yasa abban su yafi k'aunar ta cikin takun ta kamar mai tausayin k'asa ta fito xuwa falo sai kace wata babbar mace don bata fi 16yrs ba a duniya amma idan tayi wani abun ka d'auka wata babbar ce.....

Kuma sunyi dace da iyaye don dai dai gwargwado sun basu tarbiyya suna da iIlimi na addini da na nasara mai jan kunnu wa Duk kud'in mahaifin su bai hana su tsaya wa k'in neman ilimi ba..

Tana k'araso wa falo ta tarar da ammi sai saleem suna xaune suna kallo cike da shagwaba ta kwanta a jikin ammi tace

" _ammi Har ynx aunty safah Bata dawo daga schl ba_"

" _ehhh Kinsan lectures d'in yamma ne da ita yau_"

Ammi ta bata amsa turo baki tayi gaba sannan tace " _tabbb ammi anya xan iya kai wannan time d'in a schl kuwa ae gudu wa xanyi_"

Harar ta ammi tayi kafin tace " _daman ke ina xaki iya raguwa dake xan kuwa gaya wa abban ki kada ya b'ata kud'in shi a banxa ya kai Ki har malaysia karatu gwara ya barki anan_"

Marairaice fuska tayi tare da langab'e kai tace " _ya hak'uri ammi na da wasa nake wlh kinsan yanda nake da burin yin karatu sosae kada ki fad'a wa abba plss_"

Dariya kawai tayi tana cewa " _ohh nauwarah ran da bamu a duniyar har tausaya miki nake wanda xai iya da shagwabar ki_"

Kicin kicin da fuska tayi can kuma sai ga hawaye yana xuba a fuskar ta cikin kuka tace " _don Allah ammi ki dai na wannan xance ae rasa ku arayuwa ta nasan ba k'aramin *K'ARSHEN WAHALA* xan shiga ba_"

Sosae ta fashe wa ammi da kuka nan ta fara rarrashin ta tana cewa " _ae mutuwa tana kan kuwa nauwarah ba mai guje mata fatan Allah ya sa mu cika da imani_"

Dak'yar ta lalla6a tayi shiru har safah ta dawo daga schl suka cigaba da hira kiran sallahr mangariba ne ya tashe su daga hirar....

*12 pm*

Innalillahi wa'inna ilaihir rajun ta farka a firgice daga wani mummunan mafarki da tayi gaba d'aya ta jik'e da gumi ta kai idon ta kan safah da take baccin ta hankali kwance shiru tayi tana tunanin abin da ta gani a mafarkin wai abban ta ne ya rasu gashi ana xaman makoki suna ta kuka ita dasu ammi daga nan ta fara......

Xumbur ta mik'e ta tsaye ganin an kunna hasken d'akin ido hud'u sukayi da abban ta sosae tayi mamakin ganin shi a irin wannan lokacin tashi tayi ta nufi wajen shi kawai ta tsaya kallon shi ta kasa cewa komae hannun ta ya kama ya xaunar da ita a gefen bed sannan shima ya xauna a hankali yake magana don kada ya tashi safah a bacci yace

" _kema Kinyi irin mafarkin da nayi ko na dad'e ina irin wannan mafarkin amma na yau yasha banban da na ko yaushe_"

Ita dai nauwarah kallon shi kawai take shima bai damu da irin kallon da take mishi ba ya cigaba da cewa

" _ban tab'a gaya muku bane ko ammin ku bana gaya mata saboda ban son tashin hankali ku mak'iya sun yi min yawa nauwarah an dad'e ana bibiya ta don aga baya na na amma Allah bai basu ikon hkan don hka ina son ki kula da 'yan uwan ki da ammin ku, bana son ki fad'a wa kowa munyi magana dake wannan ya xama sirri a tsakanin mu_"

Nauwarah wadda ta kusan suman xaune bakin ta na rawa tace " _Abba su wane? Kuma me suke so a wajen ka? Sannan ka fad'a wa police mana? Kuma ta yaya xan iya kula da ammi safah da saleem???_

Murmishi ya saki kafin yace "_xaki iya kula da su man sannan rayuwata da dukiya ta suke nema, hmm nauwarah ke yarinya ce shi yasa amman ae idan baka iya kama 6arawo ba shi ya kama ka sanar da police ma bata taso ba gobe xan yi tafiya xuwa kano wajen wani aminina akwai maganar da xamu yi dashi na yarda da dashi fiye da yanda kike xato nasan baki san shi ba"

Abba ya d'an sauke numfashi Kafin ya cigaba da cewa " _xan baki wata jaka tana d'auke da dukkan wata muhimmiyar dukiya ta don ku samu damar kula da kanku Insha Allah baxa su ci galaba a kanki ba kuma ina son idan Allah ya nufa sun samu galaba a kaina ku gudu xuwa kano xan rubuta miki address d'in shi gobe na baki nasan shi kad'ai xai iya taimaka muku tsakani da Allah_"

Hannun nauwarah ya kama ya damk'a mata wata jaka sannan ya rungume ta har sai da k'walla ta xubo mishi tashi yayi tsaye tare da cewa

" _Allah yayi muku albarka ya k'are min ku a dukk inda kuke_"

Bud'e baki nauwarah tayi xata yi mgn da sauri yasa hannu ya rufe mata baki ya nuna mata safah dake motsi da sauri ya fice daga bedroom d'in bayan ya kashe hasken d'akin........

*_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*NA*

*_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘

*~pg 5~*

Tun da abban ta ya bar d'akin take xaune cike da tsoro da tashin hankali akan abin da ya sanar da ita me yasa abban ta ya yanke hukuncin sanar da ita bai sanar da ammi da safah ba ae ita tayi k'ank'anta da asanar da mata da wannan rikitaccen labarin mai kama da film Ko mafarki *ADALILIN SON* matar shi da dukiyar shi ake neman ranshi to suwaye wad'annan marasa imanin tunanin da take da kuka su suka hassada mata matsanancin ciwon kai idon ta duk sunyi jawur dasu sai rad'ad'i suke yi mata kamar an xuba barkono

Dakyar ta iya mik'e wa tsaye ta bud'e wardrobe d'in ta ajiyar jakar tayi sannan ta nufi toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo batasan adadin nawa tayi ba sai da taji jiri ya fara d'aukar ta sannan ta xauna ta janyo al qur'an ta fara karatu cikin muryar ta mai d'an karan dad'i tana hka har asuba tayi tana idar da sallah bacci yayi awon gaba da ita akan abin sallahr

Wajen 10 na safe Abba ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya farare sol dasu da yake ranar juma'a ne ya xauna akan dinning table ammi tana had'a mishi breakfast ya xuba mata ido ko kiftawa ba yayi har ta gama had'a mishi ta juyo don tayi mishi magana ta ga ya xuba mata ido yana kallon ta Murmishi ta saki wanda ya dad'a fito mata da Kyan ta kafad'ar shi ta dafa sannan tace

" _Abban safah irin wannan kallon hka Lfy?_"

Ajiyar xuciya ya saki tare da rik'o hannun ta yace " _bakomai gani nayi yau Kinyi min kyau sosae_" dariya ya bata ta kyalkyale da dariya don wannan kalmar kullum sai ya fad'a mata dariyar da take ta bashi shima dariya don hka yayi murmishi kawai kafin tace

" _nima kayi min kyau wlh fiye da koyaushe, amman kayi sauri ka gama don nafi son ka dawo da wuri saboda bana son dare yayi muku a hanya_"

" _an gama ranki ya dad'e_"

A hankali ya fara cin abincin yana ci yana kallon ta tun tana jin dad'in hka har ta fara jin tsoro anya wannan kallon nashi na lfy ne kafin ta samu tayi magana safah da nauwarah sun k'araso wajen suka gaida iyayen nasu cikin girmama wa gaba d'aya nauwarah jikin ta a sanyaye yake ko gayun da ake yau babu shi ta samu waje ta xauna tare da xabga tagumi ammi ta xuba mata ido kafin tace

" _lfy qlau kike nauwarah duk Kinyi wani iri gashi Kinxo kin xabga tagumi_"

Kafin tayi magana caraf safah tace " _wlh umma na tambaye tun d'axu tace ba komai koh tsokana ta yau bata yi ba_"

Har ta bud'e baki xatayi magana suka had'a ido da Abba yayi mata alamar kada ki fad'a musu don hka tayi murmishi yak'e tace

" _ammi ba komai na tashi da ciwon kai ne_"

" _Allah ya sauwake kiyi maxa ki karya sai kisha paracetamol_"

Kad'an ta iya cin abinci ta ture ta xauna har abba ya gama suka mik'e tsaye don raka shi har wajen motar da xai tafi a ciki suka rakashi duk sai da ya rungume su sannan ya shiga mota driven shi har ya kunna mota sun kusa fita daga get ya bashi umarni ya dawo baya ammi suka tsaya kallon shi cike da mamakin shi sai da ya dad'a fitowa ya rungume su ya dunga kallon su gaba d'aya sun tsorata da hkan nauwarah kuwa tuni ta fara kuka ganin hka yasa ya koma mota drive yaja mota yana ta kallon su har suka fice daga gidan gaba d'aya mai gadi ya mayar da kofa ya rufe da gudu nauwarah ta shige falo tana kuka sosae ammi da safah sai saleem suka nufi falon gaba d'aya jikin su a sanyaye dakyar suka lallashi nauwarah tayi shiru safah ta vata magani bata dad'e da sha ba bacci yayi awon gaba da ita.......

Tsaye yake a K'arshen layin da alamar jiran wani abun yake ganin wata mota ta shige yasa shi sakin wani murmishin mugunta tana shigewa ya dauko wayar shi a aljihu ya kira wata number bata dad'e tana ringing ba aka d'auka cikin wata katuwar murya yace

" _Oga an cika aiki nan d'an lokaci xakuji kyakkyawan labari_"

Daga d'aya bangaren aka kwashe da wata mahaukaciyar dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace
" _aikin ka kyau mu had'u anjima da yamma a guest house d'ina mu K'arasa biyan ka_"

Daga hka ya kashe wayar cikin farinciki ya tsayar da keken napep ya shiga suka tafi..........
Chapter 3 · 0% Book details