← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 73

Sashe 40

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin yayi mata wajen 3 missed calls bata d'auka ba yayi tunanin ko bata kusa da wayar don hka ya tashi ya fara cire kayan jikin shi don shiga wanka bud'e kofar d'akin akayi jiddah ce ta shigo hannun ta d'auke da k'aramin flaks na tea da cups akai ajiye wa tayi kan table shi kuma ya shiga toilet shigar shi kenan kira ya shigo wayar shi da sauri jiddah ta d'auka don jin ringtone na daban ne sauran kiris ta saki Ihu don ganin abin da ya tasar mata da hankali pic d'in nauwara da abduljabbar ne suka haskawa akan wayar wanda ya d'auke su selfie d'axu shine ya d'ora kan wayar ganin sunan *habibty* akan number d'in ya tabbatar mata nauwara ce kuttt wato ita har wani habibty ya saka mata bayan number d'inta da my jiddah kawai ya saka tana kok'arin d'auka ta katse kiran jin alamar fito wa daga toilet yasa ta saurin ajiye wayar da sauri ta fice daga d'akin tana xubar da hawaye tana son abduljabbar batason wata ta ra6e ta sai ita kad'ai fashe wa tayi da kuka kishi ne ke cinta kasa d'aure wa tayi ido jawur ta koma d'akin waya ta tarar yana yi irin kalaman da yake furtawa nauwara yasa ta kasa jurewa batasan lokacin da ta je gaban shi ba tana huci idon ta ya rufe ta fisge wayar tare da makata ajikin bango lokaci d'aya wayar ta tarwatse tayi d'ai d'ai da ita abduljabbar yabi wayar tashi da kallo Kafin ya ankara ta fara jifa da duk abin da ta d'auka tana ta masifa shi kuwa gefe d'aya ya samu tare da xuba mata ido kawai tana ta haukanta lokaci d'aya ta mayar da d'akin kaca kaca duk ta farfasa komai ganin tana kok'arin jiwa kanta ciwo yasa tafiya Inda take ya rik'e ta fisge wa tayi tana cigaba da abin da take hannu yasa ya bata lafiyayyen mari jin saukar shi kan fuskar ta yasa ta nutsu sai a lokacin ta lura da irin 6arnar da tayi mishi a d'aki cikin fusata yace "Kalli hannu na yanda kika yanke ni yanke ni baki da hankali ne an gaya miki kishi hauka ne don kinga ana lalla6a ki banxa wawiya kawai get out"
Xata yi magana a fusace ya nuna mata hanyar kofa yana cewa "live me alone pls Kafin na tattakaki "
Tuni tayi hanyar fita sai faman ihun kuka

Mtsww yaja tsaki d'aya wayar shi ya dauka ya fita daga d'akin ya koma d'aya bedroom d'in da yake bedrooms di'n shi 2 a cikin parlourn bai k'ara bi ta kanta ba ya lalubo nauwara a waya suka d'an ta6a hira kafin suyi sallama sai lokacin yaji xuciyar shi tayi sanyi duk 6acin ran da jiddah ta hadda sa mishi ya samu sauk'in shi

Tun da ta shiga d'akin take faman xabga kuka kamar wanda aka aiko mata da sak'on mutuwar iyayen ta ranar dakyar bacci ya dauke ta saboda yanda kalaman da abduljabbar yake yiwa nauwara sai kuwwa suke mata a kunne Lallai Idan yarinyar nan ta shigo gidan nan xataci uban ta

Bayan sun gama waya ta dawo d'akin ta tarar su fa'iza suna ta xuba surutu ita ma cikin su ta shiga suna hira daga K'arshe suka fara yi mata lectures akan yanda xata xauna da mijin ta da kishiyar ta lafia sosai nauwara ta nutsu take sauraren har dasu aunty asma'u da aunty kausar suma shawarari masu amfani suka bata don xama da kishiya irin jiddah sai a hankali har lokacin da suka kwanta yayin da nauwara ta mik'e toilet ta shiga tayi alwala ta fito shimfid'a abin sallah ta nafilfilo ta fara tare da addu'ar Allah ya basu xaman Lfy da mijinta tare da kishiyar ta tayi wa iyayen ta addu'a sosai

Aunty asma'u tana kwance kan rest chair tana d'an ta6a charting ganin abduljabbar yana kan online yasa ta tura mishi da dariya me gwalo _ke kuma lafiyar ki qlau_ ya turo nata " _ango kenan Allah ka gode wa Allah don ya baka mace mai tsayuwar dare duk gajiyar nan ta hidima bata hanata yin nafilfilo ba_"
" _Alhmdullilah naji dad'in hka nima hankalin ta nutsuwar ta da rik'on ibadar ta da kunya su suka k'ara min kaunar ta baxan iya kwatanta miki yanda nake k'aunar ta ba_"
" _Allah sarki d'an k'anina Allah ya baku xaman Lfy da xuri'a mae albarka_"
" _Ameeen_"
" _bacci nake ji Gud nyt_"
Yana fad'in hka ya sauka itama aunty asma'u sai da ta ta6a hira da mijinta tukunna ta kwanta har bacci ya d'auke ta nauwara tana karatun qur'an murya k'asa k'asa yanda baxata dami mutanen da suke bacci sai da taji bacci yana kok'arin d'aukar ta sannan ta samu ta kwanta........

*Aishat A muh'd*
🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd 😘

*~Pg 65~*

Washe gari ya kama ranar da xasu gabatar da Mother's Day wanda umma ta shirya Anan cikin gidan xasu gabatar tunda gidan babba ne sosai anyi mishi decoration wajen yayi kyau sosae sun gabatar da shi cikin kwanciyar hankali har xuwa lokacin da aka tashi kowa ya kama gaban shi, gidan ya cika makil da en uwa saboda gobe xa'a d'aura aure bayan an sakko daga sallahr juma'a

Daman ana cewa komai nisan lokaci bai shige asa lokaci ba xai xo ya shige kamar ba'a yi ba toh Hka ta kasance ga captain abduljabbar da nauwara ayau aka d'aura auren su bayan an sakko daga juma'a wanda dumbin jama'a suka shaida akan sadaki mafi cancanta saboda neman albarkar aure, kusassun gwamnati da en kasuwa xuwa manya manyan sojoji da k'ananan su sun halarta d'aurin auren abduljabbar, ango sai faman washe baki yake xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki mara misaltuwa yasha wata tsadaddiyar shadda fara sol da ita takalmi da agogo farare ne suma hka hular kanshi fara ce sol komai fari Yayi amfani dashi acewar shi yau ranar farinciki ce dole yayi amfani da farin abu kamar yanda xuciyar shi take cike da farin ciki yayi kyau har ya gaji da had'u wa gashi kannan nashi yasha gyara da sajen nan da ya k'ara mishi kyau Alhmdullilah ya furta lokacin da yaji an shafa fatiha nauwara ta xama tashi murmishi ya saki yayin da abdulkareem yake tsokanar shi

Bayan an kammala daurin auren suka xarce da yin walimah tasu irin ta maxa anci ansha sun sha addu'a daga bakunan mutane na xaman lfy da xuri'a mai albarka

Cikin gida kuwa lokacin da aka sanar an d'aura aure fa'iza dasu hafsat suna ta tsokanar nauwara har da yi mata wak'ar _ta xama d'auko riga ta xama d'auko wando ta xama d'auko buta ta xama......._ ita dai bata kula suba saboda yanda lokaci d'aya gaban ta yayi mugun fad'uwa jikin ta duk yayi sanyi ki shingid'a tayi a jikin kujera ta lumshe idon ta, tana cikin hka aunty asma'u ta shigo tana cewa "fa'iza ku fito xa'a d'auki pictures ango ya shigo dasu abba da abokanan shi "
Xumbur 'yammatan suka mik'e basu bi ta kan nauwara suka fice daga d'akin sai aunty asma'u ce ta kamo hannun ta suka fito tana sanye da wani abu kamar swiss less kamar material fari ne sol dashi har d'an kwalin kanta da aka yi mata wani nad'i mai kyau dashi kamar yanda abduljabbar yayi amfani da komai fari hka nauwara itama shigar komai fari tayi sunyi masifar yi mata kyau tasha make up sai shek'i take tana xuba wani k'amshi mai dad'i a Hka Har suka fito main parlour inda ango da sauran en uwa suke sai faman tsokanar abduljabbar suke da amarya nauwara nan aka shiga pictures da en uwa abduljabbar ko kunyar mutane baya yi yana manne da matar shi a jikin shi sai tsiya ake mishi baran aunty asma'u da abdulkareem shi dai murmishi kawai yake

Dakyar aunty asma'u ta kwace nauwara daga hannun abduljabbar ta mai da ita d'aki ba hka abduljabbar yaso ba yaso su d'an ke6e da amaryar tashi amman aunty asma'u ta kicin kicin ta hana hka yaxo xai fita daga falon ya kamo hannun aunty asma'u ya janyo ta har wurin corridor yace "wlh asma'u ki fita a idona na rufe Haba kinbi kin tak'ura wa min idan da kin hana mu Ke6ewa yanxu naga ai ta xama mallaki na"
D'an d'aure fuska tayi tace "Ehh duk da hka ka bari sai jibi Idan an kawo maka ita sai kayi yanda kake so ba mai hanaka"
Xaro ido yayi yana cewa "what! Me kikace, sai jibi fah naji kince"
Hararar shi tayi tana cewa "Ehh mana ai ba yawa k'wana 2 kawai ya rage"
"shekara 2 ba k'wana 2 ba "
Yana gama fad'in hka ya fice a fusace yayin da aunty asma'u ta kwashe da dariya ashe umma na jin su Murmishi tayi tana girgixa kai tace "Allah asma'u ki kyale min yaro hka kada mun saki baki ya lalla6o ya d'auke ta bamu gama biki ba Kinsan Kad'an daga aikin abdul"
"Haba umma ba sai muje mu d'auko ta ba"
Cewar aunty asma'u har umma xatayi magana wata er uwar tayi kiranta don hka kawai ta shige yayin da aunty asma'u tayi d'akin su nauwara kunnen ta mak'ale da waya suna magana da mijinta
Chapter 40 · 0% Book details