← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 73

Sashe 33

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmishi umma tayi tana kallon aunty sadiya tace "wad'annan yaran ka xauna dasu wlh sai sunsa mutum dariya ko baya so "
Ita ma aunty sadiyar murmishin tayi tana cewa "ina ruwan fa'iza da nauwara ai ina son xama dasu "
Can ta d'anyi shiru Kafin tace "umma ni kuwa Muna neman wata alfarma a wajen ku? "
Gaba d'aya umma ta tattaro hankalin ta kan aunty sadiya tace "ina sauraren ki auntyn yara"
er dariya aunty tayi kafin tace "d'an gida nane (tana nufin abduljabbar don sometimes hka take kiran shi) yake neman aure kuma er gida ce"
Cikin mamaki umma take kallon aunty sadiya tace "neman aure kuma? "
"ehhh shine yace na sanar da ke don kada *YAYI SAKE* (Littafi na na gaba) ko kuma *Abari ya huce*.......(littafin takori ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike), don Kisan da xancen? "

"toh wace Wannan? "Cewar umma cikin murmishi aunty sadiya tace "erki ce nauwarah!"
Cikin tsananin mamaki tace "da gaske kike? "
"k'warai kuwa don ya jima yana sonta fad'ar ce bai ba sai yanxu Allah ya nufa"
"tohh Alhmdllh ai Shikenan ko shine jiya da ya ganta tana xance ya koro ta yana ta masifa "
Murmishi aunty sadiya tayi kafin tace "Kinsan d'an gidan nawa akwai kishi "
Ta6e baki umma tayi tana cewa "toh ni dai aja kunnen shi wlh kada ya sake ya wulak'anta min 'ya, sannan xamu magana da abban su ita kanta nauwara sai mun tambaye ta tana son shi don baxan yi mata auren dole ba "
"d'an gidan nawa ba irin maxan da xa'a kyale bane "
"sai dai munyi shawara a tohh"
"toh Shikenan Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi "
"Ameeen thumma Ameeen " umma ta amsa d'an halak suna shiru sai gashi ya shigo parlourn da sallama cikin tafiyar shi ta kasaita yana sanye da uniform d'in shi sunyi matuk'ar kar6ar shi bayan sun gaisa yace "ni fah daga nan sai abuja ina aiki "
Nan suka yi mishi fatan alkhairi, har ya mik'e xai tafi sai ya koma ya xauna yana cewa "umma ko xan samu kunun gyad'a? "
"ehh akwai kuwa duba cikin flaks kan dining table akwai"
Langa6e kai yayi alamar sai dai a xubo a kawo mishi Murmishi kawai umma tayi tana shirin kiran hajja mai aikin ta sai ga su nauwara xasu tafi skul don hka ta umarci fa'iza ta xuba mishi sai da ta gaida shi sannan ta wuce xubo mishi yayin da nauwara a d'an rud'e ta gaida shi lafia kawai ya iya cewa, gefe d'aya ta koma tana jiran fa'iza amsa waya yake yana kallon ta k'asa k'asa wanda ba lalle mutum ya gane ba tayi mishi kyau

Mik'e wa tsaye yayi yana cewa "umma a barshi kawai sauri nake wlh ana jira na"
"okay ba damuwa Allah ya kiyaye hanya "
"Ameeen " ya amsa yana wuce wa da sauri suma su nauwara suka fita da sauri don har 10:30 tayi

Suna fita farfajiyar gidan suka tarar da Yah abduljabbar a tsaye shi da abdulkareem nan suka gaida abdulkareem yana tsokanar su dariya kawai sukayi ba bakin ramawa ga captain a kusa ya had'e rai K'arshe ma sai mota ya shiga ya xauna ganin hka yasa abdulkareem shima shiga don shine xai kaishi airport har yayi wa motar key sai ya lek'o ta window yana cewa "Captain yace a rage muku hanya ku shigo "
Shiga sukayi daman motar su tana wajen gyara drive ne sai kaisu su dai shiru sukayi sai dai wani lokacin suna d'an k'us k'us a junan su duk abin da suke yana kallon su ta madubin motar yayin da abdulkareem yake dariya k'asa k'asa har yana furta "ana so ana kaiwa kasuwa " har yake d'orawa da " *abari ya huce... Shi ke kawo rabon wani*"
Shi dai baya kula shi da hka har suka sauke su nauwara a skul sannan suka wuce ya kaishi airport sai da jirgin su ya tashi tukunna ya dawo gida wannan kenan.......

*Aishat A muh'd*

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd*😘

_jinjinar ban girma gare ku k'awaye na ummu abdul, aunty deejah 😜,neena cool, maman jafar,mrs muktar, maryam omar, hafsat A Aliyu (baby), Allah ya k'ara xumunci ameeen thumma Ameeen_❤😘

*~Pg 57~*

Yammaci mai cike da wani irin yanayi na lokacin xafi duk da iskar fanka da sanyin ac amman akwai hucin xafi, nauwara ce xaune a falon umma na sama tana sanye da wani three quarter d'in wando fari sol da er riga k'arama red colour mai siririn hannu tayi parking d'in gashin ta da ribbon white nd red sai k'aramin d'an kunnen ta red shima tayi kyau sosai sai k'amshin daddad'an turare take xafi ne ya isheta shi yasa tayi wannan shigar gashi ba'a fiye shigowa falon ba don hka ta bararraje sai faman waya take tana murmishi had'e da wani kakkaryar da kai ana iyayi wani guy sunan shi yusuf sun had'u dashi lokacin da xasu je gidan aunty kausar motar su ta lalace a hanya toh shine ya taimaka musu har aka gyara motar ya roki number nauwara dakyar ta bashi don ya fiye naci

Abin da yasa take son kula shi yana da barkwanci sosai duk wannan abun baisan gidan su ba kawai suna hira a waya da chatting ba k'aramin so yake yiwa nauwara ba gashi ita ba wani son shi take ba kawai tana kula shi don abin dariyar shi

Ya dad'e a tsaye a jikin kofar falon yana kallon ta a k'alla xai kai wajen mintuna 10 ko fiye da hka a tsaye yana kallon ta don tayi mishi kyau a idon shi ba Kad'an ba sai dai xuwa yanxu da ya lura da waya take nan ya fara jin ranshi ya fara 6aci don hka cikin kasaita da tafiyar shi irin ta maxaje ya k'ara sa wajen da take xama Yayi agefen ta daf da ita sannan yasa hannun shi ya kar6e wayar dake mak'ale a kunnen ta cikin tsiwa ta juyo xatayi masifa ta d'auka fa'iza ce dummm gaban ta ne ya fad'i ganin Yah abduljabbar fuskar nan tashi a murtike babu alamar fara'a kamar wanda aka aiko mishi da sak'on mutuwa sai huci yake sakamakon sauraren abin da yusuf yake cewa nauwara cikin d'aga murya yace "stop this nonsense! Kasan dawa kake magana ko bata fad'a maka Anyi mata miji agida ba toh d'aga yau kada ka k'ara kiran ta idan kunne yaji jiki ya tsira stupid boy"
Yana gama fad'in hka ya cilla wayar ta bugi bango nan take ta tarwatse a matuk'ar fusace ya juyo da nufin marin ta sai dai kash suna had'a ido ya sauke hannun shi k'asa saboda ganin hawaye male male a fuskar ta duk jikin ta rawa yake ta Kank'ame jikin ta a tsorace tausayin ta ne tare da wani irin sonta yaji alokaci d'aya ya baibaye shi baisan lokacin da yasa hannu ya rungumo ta jikin shi ba cikin wani irin mayen son nan

Wani irin shock suka ji a jikin su gaba d'aya k'amshin turaren su ya had'u waje ya ya vada wani irin k'amshi mai dad'i, nauwara gaba d'aya ta k'ara kid'ime ma don duk a xaton ta dukan ta xai yi laluben kunnen ta yayi yana cewa "ina sonki nauwarah! ina tsananin kishin ki duk lokacin da wani namiji ya kalle ki I luv you so much my nauwarahhh! "

Ya K'arasa fad'i yana kallon fuskar cikin wani irin Shauk'in so ya gaji da barin abu a xuciyar shi gwara ya bayyana shi ko ya huta, kusan sume wa tayi jin kalamar da bata ta6a tsammanin xata ji ta abakin shi ba gaba d'aya wata irin kunya ce ta lullu6e ta sunkuyar da kae tayi duk ta tak'ura da irin kallon da yake jifan ta dashi toh ganin haka yasa ta cikata ai kuwa a guje ta fad'a d'aki ta rufe kofa had'e da jingina da jikin kofar tana dafe kirji, dariya sosai ta bashi ganin abin da tayi mik'e wa kawai yayi ya fice daga falon don ji yayi kamar ya sauke wani katon nauyi akanshi wasai yake jin shi

Nauwara kam dakyar ta K'arasa kan bed ta xube sai ajiyar xuciya daman Yah abduljabbar son ta yake kenan fa'iza hasashen ta ya xama gaskia wayyo Allah na gode maka da ka bani masoyi kamar Yah abduljabbar gaba d'aya ta rasa mai xata yi tsantsar farin ciki take cikin yau sai dai kawai murmishin jin dad'i take kallo d'aya mutum xai mata yasan tana cikin farinciki
Chapter 33 · 0% Book details