← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 73

Sashe 35

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata atishawa tayi da K'arfi da sauri ta fara laluban tissue sai gani tayi an Mik'o mata karfa tayi ta toshe hancin tana ta faman jera ta sai da ta lafa ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da Yah abduljabbar yana xaune dab da ita ai tuni ta rikice duk kunya ta kamata cikin sauri ta tsugunna tana gaida shi bai amsa ba sai ma hannun shi da yasa ya xaunar da ita kan kujera suna kallon juna kanta a sunkuye tak'i ta d'ago shi kuwa idon shi a kanta hannun shi suna rik'e da hannayen ta cikin muryar shi mai dad'in gaske yace
"ashe har yanxu murar batayi sauk'i ba, mai yasa kika fiye shan sanyi da yawa? "
Cikin marairaicewa kamar xata yi kuka tace "Allah na tuba baxan k'ara ba don ba k'aramin wahala nake sha ba"
Kallon lips d'in ta kawai yake yana ayyana wani abun a xuciyar shi Kafin yace "kuma umma tace kin k'i shan magani why? "
"wahalar sha yake bani gashi ni bana son d'acin shi "
"okay, amman baki isa ba Kina fama da ciwo bakya son shan magani Kina wahalar min da kanki ,Kalli fuskar ki yanda tayi ja don hka je ki d'auko hijab d'in ki muje doctor ya duba ki "
"ni dai baxan je ba xata warke ka barshi don Allah"
D'aure fuska yayi tare da cewa "ke ina wasa dake don kinga ina lalla6a ki oya jeki ki d'auko hijab nace"
D'ago kanta tayi ta kalle shi ya d'aure fuska sosai dole ta mik'e ta nufi bedroom ya bita da kallo cike da kaunar ta,lokacin da ta shiga d'akin har yanxu fa'iza bacci take don hka ta janyo hijab ja ta sanya had'e da flat shoe ta fito da yake har lokacin bata da waya a hannu tunda ya rotsa mata kuma ya hana su umma da abba su bata lokacin da ta fito yana tsaye yana waya da hannu yayi mata alamar su je don hka tayi gaba yana bin ta a baya har suka K'arasa wajen motar shi ya bud'e mata ta shiga sannan ya rufe shima ya shiga ya xauna sai da ya gama wayar sannan ya juyo ya kamata tana kallon shi da sauri ta kauda kanta cikin jin kunya gira ya d'aga mata yana cewa "Wannan kallon fah kamar xaki had'iye ni"
Tsit tayi don bata san me xata ce mishi ba can dai tace "Nifah ba kallon ka nake ba"
Murmishi yayi tare da cewa "Haba yarinya fad'i gaskia kawai Kice Nayi miki kyau kuma kunya ta hana Ki fad'a "
Shiru tayi bata k'ara cewa komai ba har suka k'araso asibitin da alama shine doctor d'in shi da yake duba shi don suna shiga office d'in ya fara tsokanar shi "Captain ko wannan ce amaryar tamu ne? "
Shima Murmishi yayi yana xama kan kujera yana cewa "kamar ka sani kuwa"
"Amman ka iya xa6e Allah ya tabbatar da alkhairi " "Ameeen doctor"
"ah amarya k'araso mana kin tsaya a tsaye, wlh captain baka da kirki mai makon ka fara xaunar da ita Kafin ka xauna"
"ita fah nan duk tsoron allura take ji shi yasa take nokewa "
Dariya doctor ya tuntsire da ita "xaki xama matar soja shine kike jin tsoro "
Duk kunya suka bata ta kasa cewa komai kafin ta ankara taji atishawa ta taho nan ta dunga yi da sauri Captain ya k'arasa ya rik'e ta ajikin shi yana yi mata sannu doctor ma yana gefe yana xuba mata sannu sai da ta lafa ya mik'a mata hankicif d'in hannun shi ta goge hancin sannan ya rik'o hannun ta ya xaunar da ita shima ya xauna ya Kalli doctor yace "kaganta mura ce take damun ta ruwan sanyi take sha har da k'ank'ara gashi tak'i tasha magani ina abuja banyi niyyar xuwa ba wannan week d'in but saboda murar nan naxo don hka ka duba"
Cikin tsokana doctor yace "daman ina xaka iya xama amarya ba lafia"
Nan dai ya duba ta had'e da bata magungunan da xata sha suka yi mishi sallama su tafi suna isa gida ya bata maganin ba don taso ba tasha saboda ganin yanda ya had'e rai yana gama bata yace taje ta kwanta ta huta shima ya nufi nashi gidan don har yanxu su umma basu dawo ba lokacin da ya K'arasa gida jiddah bata nan don hka bedroom d'in shi ya wuce wanka yayi sannan ya xube kan bed ya xurfafa a tunanin yanda xai shawo kan abba nan da two months su aura mishi nauwara.....

*Aishat A muh'd*

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd*😘

*~Pg 59~*

Hannun ta d'auke da babbar robar ice cream sai sha take suna hira da fa'iza kallon ta fa'iza tayi tana cewa "yanxu nauwara baxa ki daina shan wannan sanyin ba? "
"ke wai ina ruwan ki jikin ki ko jikina"cewar nauwara tana ajiye robar ice cream da ta shanye "xan kirawo Yah abduljabbar na fad'a mishi abin da kika gama sha yanxu ni bansan yanda ma na biye miki har na rakaki siya"
Cikin dushewar murya tace "Idan ma baki rakani ba nasan hanya " ta6e baki fa'iza tayi tana fad'in "ni dai wlh kada ki hanani bacci yau tunda kinki daina shan sanyi kuma sai na d'auke d'ayan na cikin frige baxa ki sha ba"
Harara ta dalla mata tare da cewa "ke kin isa ma" ta K'arasa fad'i tana mik'e wa tsaye xuwa tayi ta sanya wa frige d'in key fa'iza nayi mata dariya bata kula ta ba kwanciya tayi don ta fara jin bacci itama fa'izan kwanciya tayi don dare yayi

Cikin dare nauwara hanci ya toshe ga wani axabbaben ciwon kai da xaxxa6i suka rufe ta lokaci d'aya tana yiwa fa'iza magana amman sam bataji ba saboda muryar ta bata fita sosai dole tasa hannu ta tashe ta cikin yanayin bacci fa'iza tace "wai lafia xaki tashi mutum yana cikin bacci? "
Ganin nauwara tana kuka wiwi yasa ta watstsake wa tana cewa "me ya same ki? "
Cikin dushewar murya tace "fa'iza ki taimaka min kaina ciwo yake ga xaxxa6i kuma hancina ya toshe"
Nan ta ce "tohh yanxu ya xa'a yi? Ita dai ta kasa cewa komai don hka fa'iza ta tashi ta paracetamol ta d'auko mata ta hado mata da maganin da abduljabbar ya siyo mata na mura dakyar ta lalla6a ta tasha maganin ba'a dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita sai da fa'iza ta kashe ac tare da rage k'arfin gudun fanka sannan ta koma ta kwanta

Washe gari da safe da fa'iza ta tashi tana bud'e idon ta suka had'a ido da nauwara tayi wanka ta shirya gaban ta kuma d'ayan robar ice cream di'n nan take sha ido ta xaro tare da d'ora hannu akai tace "wayyo nauwara baki da hankali ne Kina cutar da kanki toh Allah baxan xuba ido ina gani Kina cutar da kanki ba "
Cikin sanyin murya gata a dashe tace "ya xanyi fa'iza na k'asa hak'ura da sha xata warke da kanta "
"Har kin mance da wahalar da kika sha jiya da dare ? " cikin takaici fa'iza ta fad'i hkan ba saurare me xata ce ba ta fice daga d'akin ta nufi bedroom d'in umma ta tarar da Yah abduljabbar a d'akin nutsuwa tayi ta gaida shi sannan tace "umma kiyiwa nauwara magana tak'i ta daina shan kayan sanyin nan wlh jiya da ciwon kai da xaxxa6i ta k'wana ga hanci a toshe dakyar fah tayi bacci gashi yanxu ina tashi na ganta tana shan ice cream "
Da sauri umma ta mik'e tsaye tana cewa "Bari naje wurin ta ai jiya ina kallo Kece mai rakata ta siyo ice cream di'n "
Ficewa daga d'akin umma tayi yayin da fa'iza ta bita shima kasa jurewa yayi tashi yayi ya bisu ya tarar da umma sai rarrashin ta take ta rage shan sanyin sai ta warke a fusace abduljabbar yace "umma ki daina wani lalla6a ki barni da ita tunda ita batasan ciwon jikin ta ba"
Ya Kalli fa'iza yace "daga yanxu na kafa dokar daina shan ice cream a gidan nan naga wanda ya k'ara siya kuma duk lokacin da tasha ruwan sanyi ki fad'a min"
"toh yayah Insha Allah xan fad'a maka " Cewar fa'iza tana yiwa nauwara gwalo a fakaice sannan ya juya kan nauwara yasa hannun shi ya riko kunnen ta da karfi har sai da ta saki k'ara saboda xafi da sauri umma tace " kayi mata a hankali man abdul "
"umma kyale ni da ita Idan ba ta daina ba duka xan mata idan jikin ta ya fad'a mata taji" yana fad'i yana harar nauwara da sauri ta sunkuyar da kanta "ban da duka dai nasan baxa k'ara ba ma" umma ta fad'i hkan da saurin ta ta d'aga kan ta alamar ehh harara ya sake dalla mata ai kuwa ta langa6e kai tare da marairaice mishi fuska kamar xata fashe da kuka d'auke kanshi yayi baxai iya jurar ganin tana yi mishi Hka ba "Wlh umma ke kike dad'a shagwa6a ta" Cewar fa'iza murmishi umman tayi tace "tohh ina ruwan ki "
Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin fa'iza ma ta bita da sauri ganin Yah abduljabbar ya xauna kan bed d'in da nauwara take yana rik'e hannu shine ta fice don ta basu waje
Chapter 35 · 0% Book details