← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 73

Sashe 46

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watan su bakwai suna can har abduljabbar yayi tafiya ta tsawon 1 month yana sa ranar Indai ya dawo xasu je kano dakyar ya barta ta koma gidan aunty asma'u Kafin ya dawo satin shi Biyu da tafiya nauwara ta fara rashin lafiya da xaxxa6in dare ta fara xuwa safe sai ya tafi tana yi a tsaitsaye har dai ya kwantar da ita har dasu amai ga rashin jin dad'in bakin ta Indai taji k'amshin abinci to baxa ta iya ci ba tuni aunty asma'u ta fahimci abin da yake damun ta amman duk da hka sai da ta kirawo wata k'awar ta likita ce ta duba ta nan ta gano ciki d'an wata uku daga aunty asma'u har nauwara bansan wanda yafi murna ba ba K'aramar kyauta aunty asma'u tayi wa likita nan ba nan ta rubuta magungunan da xata dunga sha xasu taimaka mata wajen rage amai da samu sauk'in xaxxa6in Sannan tayi mata allura ta tafi

Ba wanda ya fad'a wa abduljabbar an Bari sai ya dawo yaji labarin su umma ma sun ji labarin don aunty asma'u ta fesa musu labarin umma dad'i ya isheta kasa hak'ura tayi sai da taxo abujan ita da aunty sadiya fa'iza da saleem haka suka biyo jirgi duk kunya ta rufe nauwara yini suka yi sai bayan mangarib driver ya kai su airport suka koma kano abba kuwa kiranta yayi a waya yayi mata sannu da jiki Hka aunty asma'u ta cigaba da kula da nauwara sosai Don ba k'aramin son ta take ba
Ranar da abduljabbar xai dawo aunty asma'u da nauwara suka shiga kitchen suna shirya mishi abubuwan ci duk da jikin ta ba k'wari amman a hka take aikin aunty asma'u tayi tayi ta barta ta koma ta kwanta ita xata yi amman sai ta nuna ta gaji da kwanciyar, daman ta kaita wajen saloon anyi mata gyaran gashi da lalle ja da bak'i
Bayan sun gama aikin suka shirya komai a kan dining table sannan ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani swiss less bak'i mai adon flowers pink a jiki d'inkin riga da siket sun xauna mata a jikin ta gashi less d'in ya haska ta abin ka da farin fata ga kuma hasken da ta k'ara na ciki tayi kyau bana Kad'an ba bayan tayi light make up ne ta xura siririyar sark'ar gwal a wuyan ta da d'an kunnen ta ta fesa perfumes design masu matuk'ar k'amshi mai dad'i tana gama wa ta Kalli madubi taga komai yayi kan sofa ta xauna tana ta6a charting a wayar ta ita da fa'iza har tana d'aukan pictures ta tura mata tana cewa ta taya ta gani ko tayi kyau katon heart ta turo mata sannan tace "Woww masha Allah a Gaskia Kinyi masifar kyau kamar ba ke ba kada yaya na ya susuce fah wannan irin haduwa "
Dariya sosai ta bata nan suka cigaba da yin er hirar su hamma ta fara alamun bacci take ji abin ka da me k'aramin ciki bacci baya yi musu wahala suna cikin hira ta 6ingire da bacci akan sofa

Bata dad'e da fara baccin ba abduljabbar ya shigo gidan aunty asma'u ya tarar a falo ta amsa mishi sallamar tashi xama yayi yana cewa
"wai ina habibty take banji motsin ta na? "
"ina tunanin tayi bacci fah "
Cewar aunty asma'u cikin murmishi d'an xaro ido yayi yana cewa
"lafia take bacci da yamman nan? "
Hannu aunty asma'u ta mik'a mishi tana cewa
"a bani goron albishir sai na fad'a maka "
D'an hararar ta yayi yace
"malama ni kawai ki fad'a min ina matata"
"Allah sai ka bani xan fad'a "
Lalubo abin da ke jikin shi yake duk abin da yake aljihun shi ya xube mata har da pistol di'n shi kud'in ta kwashe gaba d'aya ta bar pistol di'n a gaban shi sannan tace
"kawo kunnen ka na fad'a maka"
Mtsww yaja d'an tsaki yace
"wlh kin fiye 6ata wa mutum lokaci ki fad'a min malama "
"Allah sai ka kawo "
Bashi da yanda xai yi Hka ya mik'a mata kunnen shi saboda ya matsu ta sanar mishi cikin murmishi tace
"habibty di'n ka tana d'auke da ciki na tsawon 3 month "
"bana son wasa asma'u ki fad'a min gaskia pls"
Wani hawayen tausayin shi ne ya xubo mata ganin yanda jikin shi yake rawa tace
"wlh da gaske nake tana bedroom d'ina "
Da sauri ya shige ya nufi bedroom d'in aunty asma'u baccin ta take hankali kwance K'arasa wa yayi Inda take yayi mata d'aukan jarire yana juyi da ita a tsorace ta farka daga baccin jin ana juya ta had'a ido suka yi cikin tsananin farinciki ta rungume shi tana cewa
"sannu da xuwa dear, yaushe ka dawo? "
Kwantar da ita akan gadon yayi tare da d'aga rigar ta yana shafa cikinta sai faman murmishin jin dad'i yake ganin yanda yake shafa mata ciki hkan ya tabbatar mata da aunty asma'u ta fad'a mishi muryar shi taji yana cewa
"nagode nauwarahh bansan da wanne baki xan gode miki ba "
Kawai sai ga hawaye yana xuba a idon shi.....

Aishat A muh'd 😘
🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 72~*

A kid'ime take kallon shi ganin yanda hawaye suka xuba a fuskar shi tausayin shi yayi bala'in kamata hannun ta tasa tana goge mishi hawayen cikin sanyin murya tace
"Yah abduljabbar mene na godiya ni don Allah ka daina kukan nan pls "
Hannayen ta ya kamo tare da kissing d'in su yana cewa
"abin da na dad'e ina addu'ar Allah ya bani nauwarah ba dole nayi kukan farinciki ba"
"tashi mu tafi gidan mu don baby na yaji d'umin abban shi "
Murmishi tayi sannan tace
"Haba dear ya kamata ka tsaya kaci abinci sai mu tafi "
nok'e kafad'a yayi yana cewa
,"nak'i wayon yarinya tafiya xamu yi "
Ya fad'i yana d'auko mata hijab bata da yanda xata yi hka ta kar6a ta sanya suka fito cikin mamaki aunty asma'u tace
"ba dai tafiya ba?"
"yini guda muke kitchen don had'a maka abincin tar6ar ka shine xaka wani ce tafiya xaku yi"
Hka dai ya xauna dakyar ya tsaya ya ci abinci bayan sun gama Xasu tafi aunty asma'u ta mik'a mishi kud'in shi kallon ta yayi yace
"ki rik'e su ladan albishir sannan ki saurari xuwan motar ki sabuwa dal ke dai ku cigaba da yi min addu'a baby na ya fito lafia"
Dad'i ya kama aunty asma'u tayi mishi godiya tare da cewa
"Insha Allah addu'a muna nan muna yin ta "
Lokacin da suka K'arasa gida nan ya nuna mata irin kewar ta da yayi ba k'aramin tausayin shi tayi ba, sai da ya huta tsawon sati d'aya sannan suka tarkato sai Kano gidan umma suka fara sauka cikin farinciki umma ta had'a nauwara da abduljabbar ta rungume su Kafin a xauna aka gaisa tukunna ta gabatar musu da abincin da suka shirya musu bayan sun gama ci aka dawo falon umma ana ta6a hira har da aunty sadiya

Da gudu ta shigo falon kan nauwara tayi xata xauna a jikin ta da sauri abduljabbar yace
"baki da hankali ne fa'iza xaki xauna a kanta"
"ya hak'uri Yayah wlh duk murnar ganin ta ne "
Hararar ta yayi su umma suna mishi dariya can sai ga saleem nan ya shigo falon ya xama saurayi yanxu yana ss 3 a nutse ya K'arasa wajen abduljabbar yana gaida shi sannan ya gaida nauwara cikin tsananin jin dad'i take kallon saleem yaron akwai nutsuwa ga hankali ba ruwan shi da shashanci karatu kawai yasa a gaban shi
Nauwara ta so ya barta ta k'wana amma fir yak'i amince wa dole ta tashi suka tafi nasu gidan a falo suka tarar da jiddah da gudu ta tashi ta rungume abduljabbar tana cewa
"Sannu da xuwa sojana nayi kewar ka ba Kad'an ba"
d'an jiyo tayi ta harari nauwara
"Yawwa my jiddah nima nayi missing di'n ki "
Wani irin axabbaben kishi ne ya tokare nauwara xame hannun ta tayi daga nashi ta nufi stairs 6angaren ta ta nufo ta bud'e wasu xafafan hawaye ne suka xubo mata a idanun ta tana son abduljabbar tana bala'in kishin shi amman tasan ba mijin ta bane ita kad'ai dole ta sasauta wa kanta wannan kishin tashi tayi ta fara gyara 6angaren nata sai da ta tabbatar ko ina yayi tsaf yanda take so sannan ta shiga toilet tayi wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani jeans da er top marasa nauyi ta had'e gashin ta da ribbon sannan ta fito xuwa kitchen d'in ta saboda yunwa take ji abinci mara nauyi ta dafa sannan ta fito hannun ta rik'e da plate di'n abincin da fresh milk sai ruwa xama tayi a tsakiyar falon kan carpet ta hau cin abincin sai da ta koshi sannan ta jingina da jikin kujera

Jin an bud'e kofar falon yasa ta juya wa kallo d'aya tayi mishi ta kauda kanta wani irin haushin taji da kishin shi suka had'ar mata saboda da ganin shi tasan anyi wani abun xama yayi kusa da ita ya talla6o fuskar ta yana cewa
"sorry habibty na barki ke kad'ai ko "
D'an murmishin yak'e tayi tace
"Laaa ba komae ai aunty jiddah ya kamata a bata kulawa wajen wata 8 rabon ku da juna "
kallon ta yayi cike da mamakin yanayin ta ya fuskanci kishi ne yake damun ta kamo ta yayi jikin shi yana cewa
"ke ma ai Kina buk'atar kula wa fiye da ita"
Ya K'arasa fad'i yana shafa cikinta kasa magana ma tayi don ji tayi tana bud'e bakin ta kuka ne xai xubo mata

Haka dai ya rarrashe ta har ya kaita bedroom ya kwantar da ita tare da yi mata addu'ar ya rage mata hasken d'akin sannan ya sunkuyo ya sumbace ta sannan yace
"Gud nyt habibty "
Gid'a kai kawai tayi ya fita daga d'akin tare da janyo mata kofar wasu hawaye ne suka xubo daga idonta tashi tayi ta nufi toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo tana rik'on Allah da ya sasauta mata wannnan kishin
Chapter 46 · 0% Book details