← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 73

Sashe 13

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shower ya sakarwa kanshi ruwa yana ta xuba tunda ga kanshi har kafar shi sai da ya d'an samu sauk'in abin da yake damunshi Kafin yayi wanka sosai ya fito daga toilet d'in d'aure da towel a kugun shi da ka ganshi kaga cikakken namiji jarumi saboda yanda jikin shi yake a murd'e goge kanshi yayi da wani k'aramin towel Kafin ya shafa wani mai cream ya feshe jikin shi da wani body spray mai masifar k'amshi tukunna ya shirya cikin uniform d'in shi na army sunyi matuk'ar yi mishi kyau sannan ya taje gashin kanshi tare da shafa mai sai sheki yake yi ya fesa wani perfumes na kai Kafin ya fesa na jiki tuni d'akin ya d'au k'amshi mai sanyin k'amshi sai a lokacin na k'are mishi kallo sosai

Captain abduljabbar Kyakkyawa ne na ajin K'arshe dogo ne shi sambal dashi sai dai yana da faffaden kirji dai dai misali fari ne sol dashi don umman shi ya biyo duk cikin yaran ta shine ya d'ebo kyanta, akwai dogon hancin tare da wani baki d'an k'arami sai dai leb'en shi masu d'an fad'i ne Kad'an gasu lips d'in red colour ne amman red d'in mai d'an haske sai idanun shi masu kalar haske ne kwayar idon kalar su irin sexy eyes girar shi kuwa had'e take sumar kanshi mai kyau ce gata baka ga laushi da santsi kamar yana relaxer sai dai natural hair ne irin na asalin Fulani bai cika yin dariya ba sai murmishi yana dimple idan yayi magana ko dariya suna lotsawa da kuma wani a k'asan ha6ar shi kai gasky abduljabbar ya had'u ta ko'ina hand some guy

Bayan ya gama sa takalmin shi ya mik'e tsaye tare da d'aukan bindigar k'irar pistol yasa ta a cikin belt d'in ta ta jikin wando sannan ya fito xuwa falo ya tarar driven shi joseph a tsaye bakin kofar shigo wa falo kukun shi kuma yana shirya mishi table don yin breakfast joseph yana ganin shi ya sara mishi tare da kamewa yana cewa "Gud mrng boss?"

Kallon shi yayi tare da d'aga mishi hannu kawai yayi gaba xuwa Wajen da dinning table yake coffee mai xafi ya iya sha sai plantain da eggs yana kammala ci ya yago tissue ya goge bakin shi sannan ya mik'e ya fice daga falon xuwa farfajiyar gidan tuni Joseph ya bud'e mishi kofa ya shiga sannan ya rufe da sauri ya shiga sit d'in driver yayi wa motar key suka fice daga gidan direct office d'in shi ya shige dashi.

********

Zaune take acikin office d'in ta ta buga uban tagumi duk abin duniya ya ishe ta saboda yau wajen 15days abduljabbar bai kirawo ta ba kuma duk weekend ya saba yi agida but tsawon kwanakin nan baixo ba Lallai Wannan ba k'aramin fushi yake da ita ba tayi xurfi a tunani sosai taji an kwankwasa table d'in da karfi firgigit tayi ta dawo hayyacin ta, Kafin ta d'ago kanta don ganin waye ido hud'u suka had'a da farida kawar ta cikin sanyin murya tace "farida yaushe kika shigo ?"

"daman ina xaki san na shigo irin wannan dogon tunani hka lafia mai yake damun ki? "

Wadda aka kirawo farida ta tambayi jiddah ajiyar xuciya ta saki kafin tace "hmm kawata Wlh ina cikin damuwa abduljabbar ne yake fushi dani tsawon kwanaki 15 bai neme ni ko awaya gashi ko weekend bai xo ba na rasa yanda xanyi ki taimaka min kawata ina cikin wani hali saboda shi akan abincin da masu aiki suke yi ne baya so wai kuma ban iya kula da miji ba kinji fah? "

Dariya farida ta tuntsire da ita Har abin ya kular da jiddah taja tsaki mtsss tana cewa "matsala ta dake faridah kenan maimakon ki bani shawara yanda xan bullo kyasa ni agaba Kina yi min dariya "

Dakyar ta iya tsayar da dariyar ganin ta kular da jiddah tace "Kafin ince miki komai xo kiga wani abu"
Tsaye ta mik'e tare da kamo hannun jiddah xuwa window d'in dake cikin office d'in tare da nuna mata wata shegiyar mota k'irar CRV kalar green sai d'aukan ido take sannan ta takamo hannun ta suka xauna ita dai jiddah binta da kallo kawai take baki sake.........

*```Aishat A muh'd*```??
[4/9, 16:44] Umar Dalha: ????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????

*NA*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

_Aunty ameerah (group admin ( *mata masu sarauta*) wannan page d'in naki ne ngde da yanda kike k'aunar littafin nan tnx for luv nd support_❤??

☘ *~Pg 22~*☘

Cikin murmishi farida tace "kinga wannnan sabuwar motar to yau na fara amfani da ita Alhj nane ya siya min ita kud'i xaki tanada na rakaki wajen wani malam"

"malam" jiddah ta mai 2 ta cikin mamaki "k'warai da gaske malam xai yi miki aiki tamkar yankan wuk'a sai Kinxo kina juya abduljabbar son ranki "

"hmm wannan miskilin ne xai jiyo vakisan irin su asiri bai fiye kamasu ba, ni dai baxan iya asarar kud'i na abanxa ba wlh kawai ki fad'a min hanya mafi sauk'i,ke da kika ga xaki iya sai kiyi tayi Allah ya shirye ki"

Ta6e baki farida tayi kafin tace "Shikenan tunda hka kike so Indai baki bi hanyar da nabi na mallake Alhj na to na tabbatar Kina tare da wulakancin d'a namiji"

"Ehh na dai ji Kinsan na tsani bin malamai a rayuwa ta don na mallaki wani ina tsoron had'u wa ta da Allah, duk da bani da mutunci amman ina tsoron bin malamai"

Jiddah ta fad'i hkan tana danna computer dake gaban ta hararar ta farida tayi kafin a fusace tace "Eeee mu da yake bama jin tsoron Allah kike nufi ai Shikenan "

"Ohh farida matsala ta dake saurin fushi da hasala I'm so sorry my frnd yanxu ban shawara ya xanyi mu shirya da wannan miskilin mijin nawa"

"messages xaki tura mishi na yaudara masu kwantar da hankali ki nuna mishi Kinyi nadama, sannan ki kirawo shi Ki dad'a bashi hak'uri har da kukan kissa xaki had'a "
"yayi k'awar tawa hka nake son ki "

Dariya suka sa tare da tafawa Kafin Jiddah tace "ni fah baxan iya girki ba wlh don ban ma iya ba sam"

"yanda xa'a yi tun da baya son girkin er aiki na mace to ki samu kuku namiji ya dunga yi mishi saboda ko acan abuja ai kuku ne mai yi mishi, idan banda shirmen ki jiddah me yasa baxa ki bar aikin ki Kina binshi ba "

Harara Jiddah ta watsa mata sannan tace "tabbb na bishi ya kashe ni kenan, Kinsan halin Abduljabbar ai, kuma gaskia baxan iya barin aiki na na bishi ba gwara ya dunga xuwa weekend ne "

Dariya suka sake sawa tare da tafawa daga hka suka cigaba da hirar su .

Kamar yanda farida ta bata shawara Hka kuwa akayi tana dawowa daga office ta xube a falo wayar ta ta d'auko ta shiga shirya mishi kalamai masu dad'in gaske ta tura mishi sannan ta mik'e taje tayi wanka tana fito wa ta shirya cikin wata atamfa riga da siket tayi kyau kan bed ta kwanta tare da dialing d'in number abduljabbar sai da tayi 6 missed calls Kafin Ana 7 ya d'auka cikin d'aga murya yace "Lfy kike damuna da Kira hka?"

Kukan kissa ta saki tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi mishi kunsan mata da miji sai Allah nan dai ya hak'ura sannan tace "yaushe xaka xo nayi missing di'n ka Wlh? "

"ohhh sai yanxu kika yi missing d'ina ai na d'auka aikin ki yafi komai mahimmanci a wurin ki"

Cikin muryar shagwa6a tace "haba my darling kasan kafi komai mahimmanci a waje na "

"hmm a hkan bayan kin k'i bina abuja kin kwammace kullum ina hanyar kano duk weekend "

"ai ni bana son nesa da gida ne kuma don Allah a bar maganar"

Murmishi yayi mai sauti har tana jiyo shi yace "mybe sai nan da two weeks xaki ganni"

Marairaicewa tayi cikin shagwa6a tace "hba my darling ka rage don Allah "

"okay bani K'arshen satin nan ranar Friday da yamma xuwa dare xaki ganni, xan kirawo ki xuwa anjima yanxu xan fita byeeee "

Yayi hangin up d'in wayar ya bar jiddah cike da jin dad'i ganin ya sauko cikin sauk'i nan ta kirawo farida ta bata labarin yanda suka yi da abduljabbar ..........

Hmmmm masu karatu anya ba tuban muxuru jiddah ta yi ba ku dai Ku cigaba da bina don ganin yanda xata kasance.

*```Aishat A muh'd*```??

????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘
*NA*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 23~*

Ranar Friday da misalin 6 na yamma ta dawo daga aiki a gajiye take xube wa tayi a falo sai da ta huta tukunna ta samu ta shiga toilet tayi wanka taci kwalliya cikin wata shadda brown colour dinkin doguwar riga anci dauri da make up tukunna aka fara laluben abin da xa'a tanadar wa abduljabbar na ci nan ta yanke shawarar kiran umman abduljabbar dialing d'in number ta tayi bayan sun gaisa cikin marairaice murya tace "umma kinga yau abdul xai dawo gashi ban tanadar mishi abin da xai ci ba saboda bana jin dad'i yinin yau "

"Asssha mai ya same ki? "

"ciwon kai umma har yanxu bai dai na ba"

"kada ki damu 'yata yanxu xan sa FA'iza da driver su kawo mishi sannu kinji dafatan kinsha magani"

"Ehhh umma na sha"

""toh xasu kawo miki yanxun nan"

"Shikenan umma ina jira ngde sai anjima "

Nan suka yi sallama dad'i ya ishe jiddah jin xata samu abin da xata taryi abdul d'in ta don hka da sauri ta tashi kitchen ta shige ta fara fito da plates dasu cup, spoon da fork sannan ta shiga ciro drinks a frige masu sanyi ta ajiye su tana gama shirya wajen ta xube akan kujera tana washhh alamar ta gaji ,k'arar danna door bell ne ya dawo da ita daga duniyar chatting sai da ta yamutsa fuska Kafin tace "larai!!! " ta kwala wa er aikin ta kira da sauri ta shigo falon tana amsa wa da "na'am hajia "
Chapter 13 · 0% Book details