← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 73

Sashe 22

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan komai ya kammala ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin farin jeans da light purple d'in t-shirt mai dogon hannu yayi kyau sosai ya fesa turare sannan ya juyo da kallon shi kan jiddah wadda take cike da matuk'ar tashin hankali cike da takaicin biye mishi bata tsaya tasha pill d'in nan ba cikin d'an murmishi yace

"Yah lafia kuwa?
D'an sakin murmishin yak'e tayi tace "hmm ba komai wai har ka gama shiryawa ?"

"yes i want to go,any problem?"
"okay, safe journey my darling "

Sunkuyo wa yayi tare da bata kiss a kumatu yana cewa "thank u my jiddah, xan turo miki kud'i ta account sauri nake"

Langa6e kai tayi cikin shagwa6a tace "ka k'ara min akai, ina da biki next week na friend d'ina xan yi anko da siya mata gift "

Murmishi kawai yayi sannan yace "okay kamar nawa kike so, sauri nake? "

Fari tayi da idanun ta tace "50k xaka bani da hidimar bikin"

"okay xakiji alert "
Wani tsalle tayi cike da murna ta rungume shi tare da bashi kiss a lips d'in shi girgixa kai kawai yayi tare da yin gaba don kada ta 6ata mishi lokaci

Yana fita da gudu ta nufi bedroom d'in ta tare da d'auko pill d'in nan tasha sannan hankalin ta ya kwanta don tana da yakinin babu abin da xai faru (hmm jiddah kenan ita fa haihuwa ce bata so k'wata k'wata saboda tasan ita take son abduljabbar tun da bashi ya gani yana so ba umman shi ta tak'ura mishi ya aure ta, tana tunanin Idan har ta sake ta haihu abduljabbar xai juya mata baya tun da jikin ta xai lalace anata tunanin fah komai na jikin ta xai saki kirjin ta xai xube ta daina birge abdul d'in ta shi yasa take shan pill ba tare da kowa ya sani ba, batasan ba'a yiwa Allah wayo ba Idan yaso abu xai kasance babu makawa sai ya faru)

A gurguje yaje yayi wa iyayen shi sallama don sauri yake don ma yasa abdulkareem yayi mishi buking d'in jirgi

Har xai fito daga falon umma yaga FA'iza sai marairaice fuska take alamar akwai abin da take so rankwashin ta yayi aka ta saki ihun xafi tana sosawa ta juya xata tafi yace

"me kike so don da ganin yanda kike Akwai abin da kike so"

Fuskar ta babu fara'a xata fara magana yace "Kinsan bana son ana yi min magana fuska babu fara'a oya saki fuskar nan ko na tafi"

Ai da sauri FA'iza ta washe fuska tace "Yah abdul don Allah kud'i nake so "

"me xakiyi dasu? "

"hmm bikin yayar friend d'ina xamu yi "

"ku dai mata baku da magana sai ta biki, kamar nawa kike so "
"30k ya abdul don har anko da gift da xan bata"

"Shikenan abdulkareem xai kawo miki amman ki kula banda kai wa dare, don ko kin dare xan sani kuma Kinsan sauran ai ba sai na fad'a miki ba"

Cikin jin dad'in xa'a bata tace "Insha Allah yaya xan kiyaye ngde Allah ya k'ara bud'i"

Shi dai wuce wa yayi ya bar FA'iza tana tsallen murna Don sunci burin Kece raini a wannan bikin ita da k'awar ta ta

Har yaje abuja da tunanin su nauwara a xuciyar shi gashi bai biya ta wajen su ba har yaxo kwanciya bacci yana tunano yanda take dariya lokacin da ya lek'a su ta window fuskar ta tak'i 6ace mishi mtswww yaja tsaki meke faru wa da nine dakyar bacci ya dauke shi......

???☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 39~*

Hka aka cigaba da d'ora nauwara akan magunguna abin da yake d'aure musu kai likitocin sam har yanxu basu ga mussababin abin da ya makantar da ita ba gasu ga matsalar ba don hka kawai sai suka mayar da hankalin su kan kafar ta ta

Nauwara a kullum addu'ar ta Allah ya saka wa wannan bawan Allah da alkhairi yanda yake kula dasu da nema mata magani don ta warke xata so ta samu lafia don ta ganshi da idon ta ko muryar shi bata ta6a ji xata so ko godiya tayi mishi, yanxu hankalin su a kwance babu tashin hankali gashi talatuwa babu ruwan ta kula dasu take tsakani da Allah ga lafiyayyen abinci tuni su nauwara sunyi kyau kamar basu ba

Aunty sadiya ma taxo don lokacin da aka nemi abduljabbar a wajen aiki da yaxo gidan sallama dasu yake fad'a mata sai da driver ya kai ta da yake tasan asibitin shi suke xuwa ya sata washe gari ta had'a musu breakfast ta tafi musu dashi lokacin da taje sosai ta tausaya wa yaran,duk wani abu dake faruwa abduljabbar yana sani saboda doctor yana kirawo shi ya sanar dashi komai har ana yi gobe xa'a yi mata aikin ya sani

Don hka a daren kawai sai ya tsinci kanshi da tashi yayi alwala ya fara nafila tare da addu'ar Allah yasa ayi aikin cikin sa'a

*WASHE GARI*

Washe gari misalin 11 na safe aka shiga aikin sai wurin 1 na rana suka fito likitocin cike da k'warin gwiwa don Insha Allah suna kyautata xato mai kyau
Aunty sadiya ma tun safe ta xo saboda abduljabbar ya dame ta da waya kan taxo bini bini ya kirawo ta awaya yana tambayar ta abin da ke faruwa sosai aunty sadiya take mamakin abduljabbar yanda duk yabi ya damu da al'amarin yaran nan, sai da aka fito da nauwara sannan aunty sadiya ta koma gida

Alhmdullilah aiki yayi kyau sosai sai dai bata iya tafiya da kafar ta sai an taimaka mata don kamar mai koyan tafiya ta koma

*********
Cikin tsananin tarin damuwa yake ciki idan ba gixo idanu wana sukayi ba sai nace har hawaye ne suke xuba a idanuwan shi

Cikin nutsuwa ta shigo d'akin me gidan nata tayi gayu cikin shadda kalar green riga da xani tasha aiki ba wata kwalliya tayi ba daga powder sai man leb'e amman tayi kyau sai k'amshin turare ne yake tashi a jikin ta baka ce ta haifi su aunty asma'u turus tayi taja ta tsaya cike da tausayin mijin nata tun lokacin da yaje kaduna don xiyarar aminin shi ya samu labarin ya mutu ya nemi ganin iyalan shi aka ce su ma Sun mutu gaba d'aya hankalin shi ba k'aramin tashi yayi ba shine tunda ya dawo yake cikin damuwa

Hannun ta tasa tana goge mishi hawayen da suka xubo cikin muryar kwantar da hankali tace "Haba abban asma'u me yasa baxa ka daina sa kanka cikin damuwa ba sai wani ciwon ya shige shi, Kiyi hak'uri lokacin shine yayi yanxu addu'a yafi buk'ata fiye da komai "

Janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta cikin sanyin murya yace "mata ta na rasa aminini na wanda bani da aboki sai shi ya fad'a min matsalar shi na bashi shawara nima na fad'a mishi tawa naji mutuwar shi da niyyata na d'auko ya'yan shi na rik'e mishi su sai naji wani labarin da ya dad'a gigita ne wai sun mutu gaba d'aya sanadin gobara hakan ya d'aure min kai sosai "

"ya xamuyi da k'addarar ubangiji Allah ya jik'an su da rahma "

"Ameeen thumma Ameeen, na tausaya wa iyayen shi sosai innar shi tana nan bata da cikakkiyar "

Nan dai ta samu ta rarrashe shi har sake tukunna ta gabatar mishi da abincin shi yana ci tana yi mishi hira mai dad'i tuni ya nutsu ya ci abincin sosai (Duk namijin da yayi dace da mace ta gari yaji dad'in shi, don itace mai kwantar mishi da hankali Idan ya shiga wani hali na daban, en uwa na mata ya kamata mu jajurce Wajen kyautata wa maxajen mu don su dunga alfahari damu a rayuwar su)

*******

Tun lokacin da aka yiwa nauwara gyaran kafa abduljabbar ya ke d'okin Friday tayi don yaxo ya ganta shi kanshi mamakin yandayi d'okin xuwa yake

Ranar Friday tun bayan sakkowa daga masallaci ya taho jirgi ma ya biyo don tsabar k'aguwa bai yi tahowar mota ba duk yanda yake son tafiyar mota kuwa, jirgin su na sauka ya kirawo abdulkareem yana airport don hka cikin mintuna 30 abdulkareem ya k'araso airport d'in

Rungume juna suka yi cikin tsananin murna Kafin abdulkareem yace "Amman nayi mamakin xuwan ka fah saboda yanda kace min kana da aiki"

Yatsine fuska yayi sannan yace "ka mance ina patient a hospital ne? "
Dafe kai abdulkareem yayi tare da cewa "auuch wlh har na mance jiya da dare ma na kai umma da FA'iza "

Xaro ido yayi cike da mamaki akan fuskar shi yace "da gaske kake "

Hararar wasa yayi mishi tare da cewa "ah karya nake ma, yau ma munje da yaya (yana nufin abban abduljabbar don yayan shi sai dai kusan sa'annine da abduljabbar) ,bugun kafad'ar shi yayi Kad'an da sauri ya ja baya tare da rik'e wajen

"kai wlh abdul ka fiye mugunta da yawa mene na dukan kuma, kufa sojojin nan hannun ku baya xama waje d'aya "

Murmishi yayi tare da cewa "Allah ya shirye ka abdulkareem wannan d'an bugun "

"hmm ni kuwa naji xafi a jikina "
"Yasu maryam da boy hope suna nan qlau? "

Yana yiwa mota key yace "sunan qlau kai ka tsaya wasa gashi har ta harbu sauran bai fi 3 month's na sake samun new baby ba"

"da gaske kake mutumin? "

"Ah tsaya wasa yaro kasha kallo"
"nima abdulkareem ina son yara da yawa sai dai har yanxu jiddah shiru but ina nan ina addu'a Allah ya bani nima "

Cikin tausayin shi yace "kada ka damu nawan Insha Allah suna nan tafe "

Da hka ya d'auke mishi hankali da hira idan ba haka ba damuwa xai sanya wa kanshi don abduljabbar Akwai shi da son yara sosai.......

????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty }*??

*~Pg 40~*

Wajen 5 na yamma ya shigo cikin asibitin yana sanye da blue jeans da t-shirt black kayan sun kar6e shi sosai agogon hannun shi bak'i ya dace da hannun nashi sai k'amshin turaren shi na kodayaushe yake
Chapter 22 · 0% Book details