← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 73

Sashe 27

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wad'annan sai da ta siya musu gold sark'a da d'an kunne har da warwaro guda biyu sai sark'ar kafa irin siririyar nan da ake d'aura wa Kala Biyu iri daya ta siya na fa'iza da nauwara

Gaba d'aya ta rasa da wacce kalma xata gode wa umma banda dumbin dukiyar da suka kashe wajen nema mata lafia har da bata kud'i tayi tsaraba sannan bayan wannan har da siya mata tsadadden sark'a na gold kud'in su d'aya da na fa'iza, bayan sun dawo hotel d'in sosai nauwara ta dunga yiwa umma godia har sai da ta fara yi mata fad'a kan wannan godiyar Ya isa haka

Sai da suka k'ara Sati d'aya suka huta sosai sannan suka fara shirye shiryen taho wa gida ,ranar juma'a misalin karfe 12:30 na rana jirgin su nauwara da suka hau yayi landing a filin malam aminu kano a hankali mutanen ciki suka fara fito wa daga cikin jirgin ummace a gaba bayan ta kuma ............

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd {Aunty }*😘

*~Pg 47~*

A nutse take taka mattatakal jirgin jikin ta sanye da wata gown kalar milk tayi rolling da veil light green tayi kyau sosai, ware ido kawai take tana kallon ko'ina ji tayi an rungumo ta ta baya da sauri ta juya sai suka had'a ido da fa'iza da saleem tuni suka fara tsallen murna umma da aunty sadiya suna yi musu dariya dakyar fa'iza ta cikata suka gaisa da aunty sadiya ta amsa tana taya ta murnar samun lafiyar ta

Daga hka suka shiga mota sai gida nauwara ta baxa idanuwa sai kalle kalle take daman Hka kanon take da kyau,gaskia garin yayi mata kyau har suka K'arasa gida

Aunty sadiya tayi parking sannan suka firfito tana k'are wa gidan kyau yayi bala'in birgeta, direct part d'in umma suka nufa gaba d'aya an gyara ko'ina sai k'amshin turaren wuta da air freshener yake
Ganin lokacin sallah yayi yasa kowa ya tashi domin yin sallah, fa'iza da nauwara bedroom suka shiga
"tun da ke alwala kad'ai xakiyi ki fara shiga don ni sai nayi wanka "
Nauwara ta fad'i hkan tana kallon fa'iza murmishi tayi sannan tace "tohh Shikenan sis "
Toilet ta shige ta bar nauwara tana kwance kan bed tana k'are wa d'akin kallo an shirya shi yayi kyau, tana xaune fa'iza ta fito sannan ta shiga toilet wanka ta fara yi sannan ta d'aura alwala ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana gyara jikin ta (ina fatan mai karatu bai mance da nauwara ba wajen son gayu)

Bayan ta gama k'walliyar ta hannu tasa ta d'auko wata swiss atampha wanda fa'iza ta ajiye mata kan bed daga nin su sabbabi ne riga da xani ne sun amshe ta kayan sosai ta murxa d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosai sai ta fashe jikin ta da turare tana cikin xura d'an kunne fa'iza ta shigo d'akin ware ido tayi sannan tace
"wow sis kinga yanda kika had'u kuwa? "
"koh"
Nauwara ta fad'i tana murmishi "ah da gaske man yarinya kin had'u "
"toh ngde "
"muje falo umma tana jira xamuyi lunch "

Rik'o hannun ta fa'iza tayi suna tafiya suna hira har suka sakko k'asa wajen dinning table suka nufa inda umma take xaune ita ma tayi wanka taci gayun ta baka ce ta haifi su aunty asma'u ba
Da fara'a take kallon yaran nata cikin jin dad'i tace " 'yata Kinyi kyau "
Murmishi tayi sannan tace "ngde umma"
Har fa'iza ta d'auko spoon xata fara serving d'in su da sauri nauwara ta warce tana mata irin hararar wasan nan
"Lallai ma yarinyar nan Kina tunanin xaki kwashe ladan ke kad'ai Kinyi girki sannan xaki wani xo kiyi serving d'in mu"
Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a wa fa'iza baki, dariya suka tuntsire da ita umma tana cewa "da kin barta ta K'arasa aikin ta, kin huta "
"umma xan iya fah"
"toh 'yata"

Nan ta fara xubawa umma farar shinkafa ce da miyar kaji sai costlow, sai snacks samosa da scott eggs sai coconut drink, bayan ta gama xubawa umma nata ta fara xuba wa fa'iza da gangan ta cika mata plate har yana tudu ta tura mata gaban ta tana cewa "oya maxa ki cinye na k'aro miki"
"kuttt Lallai ma yarinyar nan kin rainani da yawa ni kad'ai xan cinye wannan tarin abinci "
Tana magana tana hararar nauwara dariya abin ya bawa umma yayin da nauwara take danne dariyar ta ta don kada ta fito gwalo tayi mata
"ai wallahi sai dai muci don ni Banga inda xan kai wannan abincin ba"
"ah cikin ki xaki kaishi man "
Nauwara ta fad'a tana yiwa fa'iza dariyar k'eta can kuma sai tasa hannu ta dauki spoon tace "hmm daman tsokanar ki nake sis ai tare xamu ci "
Umma dai bata kula su ba abincin ta take ci kawai suma suka nutsu suna cin abinci

Bayan sun kammala suka dawo falo nan aunty sadiya ma ta shigo part d'in umma nan hira suke yi sosai cikin farinciki da annushuwa har abba ya dawo gidan, ya taya nauwara murnar samun lafiyar ta

Da dare bayan sallahr isha'e nauwara da fa'iza sai saleem suna xaune a bedroom d'in umma suna duba tsarabar da sukayi fa'iza sai tsallen murna take ita da saleem yayin da umma da nauwara suke yi mata dariya ......

Tun around 7 na dare ya shigo kano amman gidan shi ya nufa duk yanda xuciyar shi take d'okin ganin yarinyar hka ya danne shi kanshi wani lokacin abin yana bashi mamaki yanda soyayyar yarinyar tayi mishi mugun kamu a wannan daren bacci 6arawo ne ya sace shi.........

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

_this page dedicated to my friend Aunty deejah_😜😘

*~Pg 48~*

Washe gari da safe ta kama ranar saturday ne, bayan sun kammala breakfast ne nauwara tace "umma bari naje mu gaisa da aunty sadiya na Bata tsarabar ta"
"okay hkan yayi dai dai"
Cewar umma, sannan ta juyo da kallon ta kan fa'iza da saleem da suke yin game a waya tace "kuxo ku rakani "
nok'e kafad'a saleem yayi alamar baxa shi ba ita kuwa fa'iza cewa tayi "tabbb baxan je ba game nake"
"xan rama ne duk kinci bashi yara"
"Ehh anji dai "
Fa'iza tace tana yi mata dariya had'e da gwalo kwafa tayi sannan ta fisgi ledar da tsarabar aunty take ta nufi hanyar fita daga falon ko gabanta ba ta gani

Washh nauwara ta fad'i tana dafe goshin ta sakamakon karo da tayi da mutum a tsorace ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da abduljabbar a lokaci d'aya gaban su yayi wani irin wawan fad'uwa, Bata ta6a ganin shi ba a fili sai a picture da jiya fa'iza ta nuna mishi don hka da sauri ta tsugunna k'asa tana cewa
"don Allah yi hak'uri yaya abduljabbar ban kula bane"
Tun da ta fara magana ya xuba mata ido cike da wani irin yanayi a tattare dashi tayi masifar yi mishi kyau tana sanye da black d'in wando sai riga red ta kai mata kusan gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da black d'in veil gaba d'aya ya kasa wani motion sai da yaji ta sake magana tana gaida shi sannan ya basar ya amsa da lafia kawai tashi tayi xata fice har tayi taku biyu ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"keee ina xaki da hka?"
"wajen aunty sadiya xan je "
Nauwara ta bashi amsa k'ara d'aure fuska yayi tare da cewa "da hakan xakije har wurin aunty sadiya ga mai gadi da sauran masu aiki maxa suna kallon ki toh oya jeki, ki canja kaya "
D'an tsaya wa tayi cikin mamakin Wannan fad'an da yake yi mata tsawa ya daka mata yana cewa "Ko bakiji abin da na fad'a miki ba? "
Ai Kafin ya rufe bakin shi tuni ta bar wajen d'aki ta koma tana sauke ajiyar xuciya tare da cewa "shi wannan ya abduljabbar d'in daman Hka yake tabb xa'a sha fama dashi " wani less ta d'auko ash colour da touch d'in pink a jiki d'inkin riga da siket sunyi mata kyau fiye da wad'anda ta cire yanxu

Lokacin da ta k'araso falo yana xaune kan kujera 1siter suna hira da umma cikin mamaki umma take kallon ta tace "Har kin dawo? "
"uhm uhm mantuwa nayi na dawo" ta fad'a tana kallon abduljabbar da ya mai da hankalin shi kan tv, wow gaskia wannan guy d'in akwai kyau jebe shi kamar balarabe maganar da umma tayi ita ta dawo da ita hayyacin ta
"kiyi sauri ki dawo yanxu xan aike ku gidan kausar? "

Da sauri ta fice tana cewa umma "toh, bayan sun gaisa da aunty sadiya sun d'an ta6a hira sannan ta bata tsarabar ta na turare da abayat tayi godiya sannan tayi mata sallama ta fice

Lokacin da ta dawo bata tarar da abduljabbar ba amman taso sake ganin beauty face d'in shi a gurguje suka shirya driver ya kaisu gidan aunty kausar itama ta kar6i nauwara a hannu bibbiyu sun sha hirar su sai bayan mangarib driver yaxo ya dauke su suka rabu cikin kewar junan su

To Hka rayuwa ta cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa a yayin da aka sama wa nauwara skul d'in su fa'iza a ss 2 suka ajiye ta bayan dogon naxari da gwada ta da sukayi ta cancanta da shiga ss 2,ajin su d'aya da fa'iza hakan ba k'aramin dad'i yayi musu ba

Sun mayar da hankalin su sosai wajen karatu har makarantar islamia aka sanya su karatu suke sosai babu wasa gashi basu fiye fita ba sai da dalili rayuwa suke yi mai dad'i cike da kwanciyar hankali..........

```Aishat A muh'd```😘

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

_Ngde sosae masoya na wajen turo min sak'onni Kuna yi min addu'ar samun sauk'i, toh Alhmdllh na samu lafia, ngde sosae Allah ya bar xumunci ameeen_❤😘

*~Pg 49~*

*AFTER 1 YEAR*

A cikin Wannan shekarar abubuwa da yawa sun faru na samun cigaba sosae a fannin rayuwar su nauwara
Chapter 27 · 0% Book details