← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 73

Sashe 36

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon ta kawai yake ita kuma sai wani kauda da kai take don baxa ta iya jure had'a ido dashi ba hannun shi yasa ya d'ago kanta lumshe ido tayi dogayen gashin idon suka kwanta kan fatar ta ya xuba wa kyakkyawar fuskar ido cikin muryar shi mai dad'in gaske yace "bakya jin magana koh? "
Kamar xata fashe da kuka tace "kayi hak'uri na daina Insha Allah " "okay yayi kyau yarinya, mu je kiyi breakfast sai kisha maganin ki xaxxa6in ya sauka ne? " ya K'arasa fad'i yana ta6a wuyan ta "ehhh sai ciwon kai kawai " "okay sannu "
Hannun ta ya rik'e bayan ya d'aga ta daga xaunen da take cikin jin kunya tace "don Allah Yayah ka fara yin gaba Allah kunyar umma nake ji "
Murmishi yayi yana cika hannun ta ya lakuce mata hanci yana cewa "kin fiye kunya da yawa na baki 5 mint Idan baki fito ba xan dawo na d'auke ki, kin yarda? "
Da sauri ta d'aga kanta tana cewa "Ehh Allah na yarda"
Girgixa kai kawai yayi ya fita daga d'akin xauna nawa tayi tana cewa "ohhh ni nauwarah daman Hka Yah abduljabbar yake " ganin taci mintuna 3 da fitar shi yasa ta mik'e wa da sauri ta fita daga d'akin suna xaune kan dining table har da Abba nan ta tsugunna k'asa tana gaida abba ya amsa yana cewa "ya jikin naki 'yata? "
"na samu sauk'i abba"
"toh Allah ya k'ara sauk'i"
"Ameeen abba ngde"
Jan kujera tayi ta xauna kusa da fa'iza tana d'ago kanta suka had'a ido da abduljabbar yana mata alama da ido ta dawo kusa dashi da sauri ta sunkuyar da kanta tabb ina xan iya wannan rashin kunyar ga Abba da umma a xaune duk a tak'ure take cin abincin sbd yanda yake kallon ta duk abinda yake umma da abba suna kallon shi Murmishi kawai sukayi irin nasu na manya cikin k'asa da murya abba yace wa umma "wannnan d'an nawa ya xurma da yawa fah 'yar ki ta rikita min d'a " Murmishi kawai umma tayi da hka suka gama breakfast d'in abba da Yah abduljabbar suka fice daga gidan yayin da nauwara da fa'iza suka dasa sabon hira yayin da fa'iza sai tsokanar ta ke sai dai tayi murmishi tace "Allah ya shirye ki fa'iza........ .......

```Aishat A muh'd```😘
🍀☘☘🍀?
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????

*written by*
*Aishat A muh'd*??

*~Pg 60~*

Hka rayuwa ta cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa tsakanin nauwara da Yah abduljabbar soyayya suka xuba wa a waya kamar bashi ba shi kanshi wani lokacin abin ba k'aramin bashi mamaki yake ba ganin yanda soyayyar yarinyar nan ya kasa danne ta agaban kowa nuna wa yake

Wajen watan shi d'aya da tafiya bai xo kano ba ayyuka sun rik'e shi gashi yana son xuwa ko dan ya sanar da abban shi nan da wata 2 yake son ya auri don baxai iya kai har wajen 2yrs ba bai mallake ta matsayin matar shi ba, su aunty asma'u da aunty kausar fa'iza ta tsegwanta musu soyayyar da Yah abduljabbar da nauwara suke toh suma sunyi murna don nauwara mutum ce ba ruwan ta tana basu girman su a matsayin su na yayyani ai kuwa aunty asma'u ta kirawo shi awaya yasha tsokana K'arshe da ta dame shi sai ya kashe wayar don duk sunyi mamakin yanda soyayya ta canja shi kamar bashi ba,

Ranar juma'a bayan an idar da sallah ya taho da yake jirgi ya biyo nan da nan ya k'araso gida da sallama ya shiga parlourn umma ce cikin murmishi ta amsa mishi yayin da saleem yake yi mishi oyoyo hugging di'n shi yayi yana cewa "saleem ya skul dafatan ana karatu sosai "
"uncle ina yi sosai ka tambayi umma ?"
"ahh d'an nawa yana karatu sosai " Cewar umma yana xama kusa da umma yace "good boy ka cigaba da karatu "
"Tohhh uncle "
Yana gama fad'in hka ya fice daga falon dama fita yake kok'arin yi xai buga ball
"Shigowar yanxu kayi kenan "
"ehhh wlh umma na dad'e banxo ba aiki ne ya rik'e ni "
"ai Kuna ma kok'ari Allah ya taimaka ya kare ku "
"Ameeen umma na "
Sai baxa ido yake yaga ta Inda nauwara xata fito amman shiru ba motsin su a gidan don hka yace "umma wai ina nauwara ne? "
Murmishi tayi tana cewa "suna skul yau lectures d'in yamma ne da su "
"okay shi yasa nake ta neman kiran ta wayar is switched off "
Can ya cigaba da cewa "daman umma ina son xamu yi magana?"
Tattaro hankalin ta kanshi tayi tana sauraren shi yana sosa kai yace "am daman umma akan wannna maganar ne "
"Wacce magana kuma?" Duk da ta fahimci abin da yake nufi sai ta basar "umma maganar gaskia ina son nan da two months xan auri nauwara "
Hararar shi tayi tana cewa "ai sai sun gama makaranta ka jira nan da shekara 2 da en watanni ne ya rage musu fah Kuma kamar yau ne xaka gani"
"kai umma gaskia baxan iya jure ba pls"
Hangame baki tayi tana kallon shi shi kuwa ko a jikin shi tsakanin shi da Allah yake fad'a nan ya langa6e kai tare da marairaice fuska yana lalla6a ta Murmishi kawai tayi yanda yake yi musu biyayya yana kyautata musu a matsayin su na iyayen shi ai sa bashi farincikin shi duk da wani 6angare na xuciyar ta tana d'an shiga damuwa Idan ta tuna jiddah katse mata tunani yayi ta hanyar rik'o hannun ta yace "pls umma ki yarda da abin da nace tun da kinga itama tana sona " murmishi tayi sannan tace "ni ta 6angare na ba komai na amince amman kasan halin jiddah ni bana so mu samu matsalar xumunci da er uwata"
"umma Kinsan dai mamee (mahaifiyar jiddah) bata da matsala da ace jiddah halinta tayi da naji dad'i amman k'wata k'wata bata d'auko halin ta ko d'aya ba Idan na samu time xanje nayi mata bayani da kaina "
"toh Shikenan Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi "
"Ameeen umma na "
Sun d'an ta6a hira sannan ya mik'e tsaye yana cewa "umma Bari naje na d'auko su a skul"
Tana murmishi tace "okay Allah ya kiyaye hanya "
Haka ya fice daga falon umma sai da ya biya wajen aunty sadiya suka gaisa sun d'anyi hira tukunna ya tashi tafi d'auko su nauwara a nutse yake driven har ya k'araso skul d'in yayi parking tukunna ya fito daga motar wow wasu "yammata suka ce ganin wannnan hadadden guy d'in yana fito wa daga cikin motar d'aya daga cikin su tace "kai wannnan guy d'in ya had'u K'arshe irin mijin da nake mafarkin samu Kenan" d'ayar ta gefen ta ce "ni kuwa sai naje naji yanda muryar take don a gaskia baxan iya jure wa ba sai naje wurin shi " wadda ta fara magana ta harare ta yayin da ragowar biyun suka kwashe da dariya tare da tafawa nan ta bud'e handbag di'n ta powder ta d'auko ta gyara fuskar ta tare da fesa turare sannan ta mayar da kayan jikin handbag di'n ta gyara mayafin ta tana wani tafiya tare da kwarkwasa aka nufi wajen abduljabbar da yake a tsaye yana neman wayar nauwara ringin biyu ta d'auko cikin sanyin muryar ta tayi mishi sallama ya amsa mata sannan yace " *habibty* ina skul d'in ku fah ina jiran ku am Kinsan bansan jira koh? "
Cikin murna tace "da gaske? "
"Xanyi miki wasa ne na baku 5 mint ku fito "
Sannan yayi hangin up d'in wayar, cikin tsananin farinciki nauwara ta rungume fa'iza tana cewa "ke lafian ki qlau? "
"Yah abduljabbar ne yaxo d'aukan mu fah"
Xaro ido fa'iza tayi tana cewa "da gaske kike kuwa"
"Idan Munje Kya tabbatar ni kaina ba k'aramin mamaki nayi ba" da sauri kowacce ta d'auki handbag di'n ta suka nufi inda yake

Glass d'in kofar aka kwankwasa da sauri ya d'ago kanshi ya Kalli wajen ya d'auka nauwara ce sai yaga bakuwar fuska nan ya had'e rai kamar bai ta6a dariya ba tuni jikin ta yayi sanyi ganin yanda yayi mata kwarjini ta kasa magana a fusace yace "lafia ?" nan ta dabarbarce ta rasa me xata ce "Idan baki da abin cewa ki bar nan" Mtsww ya saki tsakin da ya dad'a tsorata ta Amman duk da don naci ta dake cikin kwarkwasa da iyayi tace "suna na ruky Idan ba damuwa ina son ka fad'a min sunan ka ka bani contact di'n ka, kana da kyau ina son ka "
Murmishin yak'e yayi yace "are u sure kana sona da gaske?"
Gyara tsayuwar ta tayi tare da fari da ido "yes! off course "
Tana rufe bakin ta taji saukan wani lafiyayyen rabo da sauri ta rik'e kumatun ta saboda ba k'aramin xafi taji ba en wajen suka d'auki ihu ganin hka yasa ta janye tsumman kafafun ta don ba sa'a cikin takaici ta K'arasa wajen da suke xaune ai kuwa suka k'ara sakin ihun k'eta nan ta fara bambamin fad'a daman ance tabarmar kunya da hauka ake nannad'e ta nan taga ba dama sun ishe ta da iska yasa ta bar wajen
Chapter 36 · 0% Book details