← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 73

Sashe 19

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"bari na bishi naga asibitin da aka kwantar da ita naga jikin? "

Nan ya fice da sauri ya bar su cikin tashin hankali, lokacin da yaga jikin saude ba k'aramin firgita yayi ba kamar ba ita ba duk kamannin ta ya canja shi ya nemo en uwan ta nan da nan suka xo su ma...

Lokacin da ya dawo ya bawa su nauwara labarin halin da take ciki gaba d'aya ta rud'e kuka kawai take wannnan a daren nauwara batayi runtsawar kirki ba saboda tsabar fargaba na halin da saude take ciki addu'a kawai take yi mata

*BAYAN KWANA 3*

Acikin wad'annan kwanakin uku baxan iya fad'a muku tashin hankali da nauwara ta shiga ba duk wasu abubuwan da saude take musu babu shi abinci ne sau d'aya arana wannan er hayar gidan take taimaka musu don suma ba wasu masu karfi bane gashi saude tana gadon asibiti ko sanin wanda yake kanta batayi

Daren ranar da ta cika Kwana uku a daren saude ta amsa kiran ubangiji gaf da asuba Allah sarki xo kuga tashin hankali wajen nauwara abin ba'a cewa komai sai addu'ar Allah ya jik'an ta da rahma...

Sati Biyu da rasuwar saude kud'in hayar ta ya k'are mai gidan ya buk'aci su tashi xai sa wata idan kuma suna da kud'in biya sai biya hankalin nauwara idan yayi dubu ya tashi ta rasa inda xata tsoma kanta taji dad'i

Har lokacin da ya basu idan basu da kud'in su tashi amman nauwara ta rasa inda xasu je da hka har suka k'ara k'wana d'aya ai kuwa Washe gari da sassafe mai gidan yaxo da yake irin mutanen ne da akan kud'in su basu da mutunci Hka yasa aka watsa wa su nauwara kayan su waje suna kuka da rokan shi yayi hak'uri Amman ko a jikin shi sunci kuka a kofar gidan nan Kafin su tafi su bar nan.......

Hka su nauwara rayuwa ta juya musu suka shiga wata irin rayuwa a wannnan lokaci wadda tafi ta baya tsananin saboda abin da xasu ci gagarar su yake sai sunyi bara suke samu

Basu da wurin k'wana sai dai su samu wata rumfa ko wani lungun su mak'ale su k'wana basa samun yin wanka duk sunyi bak'i sun rame Sun koma mabaratan karfi da yaji don Idan basu yi bara ba xa su samu abun da Xasu ci ba rayuwa ta mara galihu suke tun tana kuka har ta hak'ura suka rungume rayuwar su ta yanda taxo musu

Wataran su samu wani lokacin kuma sai dai su yini da uwar yunwar su da hka suke jurewa har sun saba da hakan sun d'auki tsawon lokaci acikin hka suke gudanar da rayuwar su

Wani yammaci ne mai cike da dada'an yanayi iska tana kad'awa mai matuk'ar dad'i nauwara tana xaune akan kujerar ta a gefen titi saleem ya tsallaka titin don ya siyo mangoro Don mai tallan yaji yake fadawa nauwara yana sha'awar shan mangoro shine ta bashi wata naira 10 yaje ya siyo shiru shiru har yanxu bai dawo ba shine hankalin ta ya fara tashi nan ta fara kiran shi "saleem! Saleem!! Saleem!!! Shiru bata ji alamun ya dawo ba tuni idanun ta Sun kawo k'walla tare da tunanin ina saleem yayi

Adai dai lokacin abduljabbar yayi parking d'in motar shi don amsa Kira ya gama wayar ne sai ya d'ago kanshi ya Kalli wajen sai yaga yana sha'awar fita don ya da sadaka a hankali ya bud'e kofar motar ya xuro kafar shi ya fito yana sanye da black jeans da t-shirt ash colour yayi matuk'ar yin kyau nan ya fara raba musu kud'i yana cikin hka yaji an rik'e rigar shi juyo war da xai yi idon shi ya sauka akan wata kaxamar yarinya akan keken guragu tana kiran saleem ran shi yayi matuk'ar 6aci don Abduljabbar ya tsani kaxan ta gashi wata banxa kaxama ta rik'e mishi riga wayyo a lokacin xan so kuga yanda fuskar abdul ta koma saboda tsanani 6acin

Ita kuma nauwara a b'angaren wani hadadden k'amshin turare ne ya bige wanda bata ta6a shak'ar k'amshi irin shi ba wanda rabon ta shak'i irin Wannan k'amshi har ta mance a rayuwar ta.....

???
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 34~

Ganin tana kok'arin kamo hannun shi yasa shi k'ara fusata bai san lokacin da ya d'aga hannu ya wanka mata mari mai matuk'ar gigita mutum, da sauri tasa hannu ta dafe wurin da ya mare ta wani kuka mai ciwo ta fashe da shi Kafin taji muryar shi mai matuk'ar dad'in gaske amman cikin fad'a

"are u mad, xaki rik'e ni da wannan kaxamin hannun naki me kike so? "

Lokacin da taji muryar shi sai da gaban ta yayi mugun fad'uwa Kafin ta bud'e bakin ta dakyar cikin muryar kuka tace

"I'm so sorry ina neman k'anina, bana gani shiya sa na rik'e ka kayi hak'uri "

Dummm shima gaban shi ya fad'i jin muryar ta, amman sai ya basar yaja tsaki kawai ita kuma nauwara sai taja kujerar ta Xuwa gefe d'aya tana dafe da kumatun ta sai kuka take saboda marin ba k'aramin shigar ta yayi a 6angare d'aya na xuciyar ta tana mai tunanin wannan daddad'ar murya duk da bata ganshi ba amman tasan ba k'aramin kyakkyawa ba ne...

Abduljabbar kuwa yana gama raba kud'in ya jiyo xai shiga mota sai ga saleem yana cewa shima ba'a bashi ba hannu ya xura a aljihu ya xaro 2k ya bashi nan yayi godia tukunna ya shige sai ya bishi da kallo bai tsaya Ko ina ba sai wurin nauwara ya tsugunna a gaban ta yana Bata labarin an basu sadaka har ta 2k mtswww yaja tsaki sannan ya shige mota

Yana shiga sai ya cire rigar nan ta jikin shi wadda nauwara ta rik'e ta ya cillar da ita waje ya bar vest d'in ciki tukunna yaja motar shi ya bar wajen yana Allah Allah yaje gida don yayi wanka don duk a tak'ure yake jin shi...

Rigar nan tashi ba inda ta sauka sai kan fuskar nauwara daman a saitin wajen take sai da gaban ta ya fad'i jin k'amshin turaren nan hannu tasa ta d'auke rigar daga fuskar ta tare da rik'e ta Kam a hannun ta don hka kawai taji tana bala'in son rigar da k'amshin turaren

Sai da mangariba tayi sannan saleem ya tura ta suka bar wajen xuwa wata er rumfa da suke k'wana...

********

Yana xuwa gida wanka ya shiga yayi sosai ya dunga durxa jikin shi wajen wankan sai da yaji fatar shi tana rad'ad'i tayi jawur da ita sannan ya kyale wankan ya fito ya xura farar jallabiya mai gajeren hannu tare da fesa turare silifas d'in mai matuk'ar laushi fari ya sanya a kafar shi sannan ya shige Xuwa masallaci don ba da faralin mangariba

Sai bayan anyi sallahr isha'e ya fito daga masallacin dinning table ya xauna ya had'a tea yasha tukunna ya mik'e xuwa bedroom d'in shi sai da ya sake wanka sannan ya kwantar Ko neman jiddah bai yi ba saboda har yanxu bai huce ba nan da nan bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi...

Cikin bacci ne yayi mafarki da wannan yarinyar almajira dayagani tana gudu wasu mutane sun biyo ta da makami a hannun su suna bin ta a baya tana gudu sosai hannun shi ta kama tana cewa ya taimaka mata firgigit ya tashi daga bacci cike da mamakin Wannan mafarki daga ganin ta sau d'aya sai mafarkin ta

Mtsww yaja tsaki mybe tausayin ta ne yasa shi yayi mafarkin ta daga hka ya juya ya koma baccin shi...

Toh fah abduljabbar tun daga Wannan lokacin yake mafarkin nauwara Kala Kala kuma duk wanda yake yi kuka yake ganin tana yi tana ce mishi ya taimaka mata tun abun baya damun shi har takai yana d'an tsaya wa ya yi tunanin hkan sai ya fara tunanin hanyar da xai bi Don nemo yarinyar

Inda ya fara had'u wa da ita ya fara xuwa sai dai an tabbatar mishi an d'an k'wana 2 ba'a gansu a Wajen ba Duk inda yaga masu bara xai tsaya ya duba ko xai gansu Amman ko mai kama dasu bai gani ba hka ya tattara ya koma abuja

******

Gaf da mangariba sun sha yawo sun gaji da bara basu samu komai ba rabon su da abinci tun kosan safe da aka basu sadaka yunwa sosai suke ji har akayi isha'e tuni yunwa ta fara gala6aitar dasu

Nan suka fara tafiya kawai don neman abin da xa suci saleem a gajiye yake tura ta tsintar kansu suka yi awata unguwa shiru kamar ba mutane gefe d'aya suka samu xama sukayi duk sunyi shiru saboda yunwa kowanne da kalar tunanin da yake yi

Dare ya farayi don 12 na dare ta gota kwatsam sai ga wasu en shaye shaye su 3 sun taho suna rangaji akan hanya daga nin su sunsha sunyi tatul sai suka hango su nauwara cikin maganar en shaye shaye d'ayan yace

"yaa baabaa ga wata yarinya can ko xamu d'an latsa ne?"

Sauran biyun suka kwashe da dariya sannan a tare suka ce

"ai fad'a ma 6ata baki ne kawai muje mu kwashi gara Allah yasa akwai Maik'o "

Suna gama fad'in hka gadan gadan sukayi kan nauwara Bata ankara ba taji an rirrike ta Ana cewa "Yawwa kaga ma gurguwa ce yi sauri kayi ka gama nima na fara don da gani xatayi maik'o "

Hba jin Wannan maganar tasu nauwara batasan sanda ta k'walla wata uwar k'ara ba k'arar da tayi ita ta tashi saleem daga d'an baccin da ya fara ganin abin da yake kok'arin faruwa da auntyn shi ya sa shi tashi xumbur yana tutture su ganin saleem xai 6ata musu lokaci yasa d'aya daga cikin su ya damke shi daman d'aya ya rik'e nauwara kam d'ayan kuwa ya fara kok'arin yaga mata rigar jikin ta har yayi nasarar keta ta..........

??☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*

*Aishat A muh'd {Aunty}*??

_Godia mara adadi gare ki k'awata saNaz Allah ya k'are min ke a duk inda kike Allah ya bar xumunci ameen_❤??

*~Pg 35~*
Chapter 19 · 0% Book details