← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 73

Sashe 25

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koma wa d'akin FA'iza tayi inda ta tarar nauwara ta fito daga wanka tana tafiya da sauri umma ta K'arasa ta rik'e ta ganin sauran Kad'an ta bige da wardrobe "har kin fito kenan ?"
"Ehhh umma"
Gefen gadon ta xaunar da ita tare da Mik'o mata mai ta shafa sannan ta bud'e wardrobe d'in FA'iza ta d'auko mata wata atamfa riga da siket d'inkin da gani sabuwa ce tare da d'auko mata sababbin underwears sai da ta damk'a mata su a hannu sannan ta fita daga d'akin don ta bata damar shirya wa a nutse, xanyi magana da abdul ya kamata a nema mata magani makanta bata da dad'i balle ga matashiyar yarinya k'arama

Bayan ta tabbatar ta gama shirya wa ta sake koma wa dakin ta tarar ta gama shirya wa tsab turare ta d'auko ta fesa mata sannan ta kamo hannun ta suka fito parlour nan suka tarar da saleem a xaune kallon cartoon yake a mbc 3 ya saki jikin shi kamar d'an gida ko dan anbashi damar hkan ne amman ae sauran gidajen da suka xauna ba'a basu damar hkan ba har gwanda gidan saude

Yana ganin nauwara ta tashi da sauri ya rungume ta dariya suka cikin murna yace "aunty nauwara cartoon nake kallo"
"Ah haba d'an k'anina"
"da gaske nake ko umma?"
Ya fad'a cikin tabbatar da hkan dariya umma tayi sannan tace "da gaske yake mana, kema Insha Allah xaki samu lafia Ki dunga gani kamar kowa"
Murmishi nauwara ta iya tare da yiwa umma da d'anta addu'a fatan alkhairi sun gama yi musu komai a rayuwa

Kan dining table umma ta xaunar da nauwara saleem ma ya xauna da kanta tayi serving d'in su ta damk'a wa nauwara spoon a hannun ta sannan tace "ku saki jikin ku, kuci abinci idan bai isa ba gashi nan ina xuwa "
Tana gama fad'in hka ta juya ta tafi ta bar su nauwara suna cin abinci tunani nauwara ta fara da yanda umma ta kar6e su babu tsangwama ko kyamatar su sai ma dad'a jansu a jikin ta da take toh ai daman na Allah basa k'are wa a duniya nauwar

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty }*😘

*~Pg 44~*

8 na dare suna xaune a parlour FA'iza ta shigo falon agajiye ta xube kan kujera tare da fad'in "washhh umma na gaji wlh "
Harara umma ta watsa mata sannan tace "Yayi miki kyau FA'iza sai yanxu kika ga damar dawowa? "
Marairaice fuska tayi tace "umma wallahi duk laifin aunty kausar ne ta xaunar da ni "
Sai lokacin ta hangi nauwara da saleem cikin alamar tambaya tace "su waye wad'annan umma? "

Murmishi umman tayi kafin ta bata amsa da "k'annan kine daman Kece Mai mitar duk su kausar sun tafi sun barki a gida to ga en uwa nan"

Wani ihu tayi tare da bugu tsalle har tana tsorata umma dasu nauwara ta rungume umma cikin tsananin farinciki tace "Allah umma da gaske???"

Cikin dariyar yanda FA'iza take murna tace "k'warai kuwa "
"umma naje mu gaisa da su? "
Ta fad'a tana B'uye fuskar ta a jikin umman "Ohh ni 'Yasu ke da en uwan ki je ki mana"

Duk abin da suke nauwara tana jin su da kunnen ta Murmishi kawai take faman yi cike da kaunar FA'iza da iyalan gidan gaba d'aya Ohh ni nauwara Allah ya bani lafiyar idanuna don naga wad'annan bayin Allahn da suka taimaka min
Da sauri FA'iza ta washe baki jin abin da umma tace kai tsaye inda nauwara take ta nufa tana xuwa ta mik'a mata hannun ta don su gaisa sai taga bata Mik'o mata nata hannun ba umma da taga hka sai tace
"FA'iza ai bata gani da idanun ta, batasan kin miko hannun ki ba "

Lokaci d'aya jikin FA'iza yayi sanyi cikin tausayin nauwara ta kamo hannun tasa a nata sannan tace "sannu sis nice to meet you, What is your name???"
Da Murmishi akan fuskar ta tace "Nauwarah sa'eed haruna ga little bross d'ina saleem "

"wow nyc name"
"thank u "
Nauwara ta fad'i FA'iza cikin jin dad'i tace "You're welcome"

Hannun ta rik'e tace "tashi mu tafi d'akina akwai labari"
Mik'e wa tsaye tayi fa'iza tana rik'e da hannun suka nufi upstairs
"Muna cikin hira da er tawa shine kika d'auke min ita "Cewar umma da sauri fa'iza ta juyo cikin marairaicewa tace "yi hak'uri umma hira xamu yi ki barmin ita pls"
"Shikenan na baki aron ta don naga yanxu dare yayi ne "
Cikin dariyar jin dad'i fa'iza tace "thank u so much my umma"
Daga hka suka wuce d'akin fa'iza ko 5 mint da shiga basu yi ba abduljabbar ya shigo da sallama da gudu saleem yaje ya rungume shi yana yi mishi oyoyo
"saleem ya kk, dafatan xaman gidan namu yayi maka dad'i ?"
"uncle wlh umma tana da kirki sosai ina son ta kamar ammi na"
D'an murmishi yayi Kafin yace "good "

Zama yayi kan kujera yana gaida umma bayan sun gama gaisa wa yake mik'a mata ledar hannun shi yana cewa "gobe monday Insha Allah saleem xai fara xuwa skul d'in su fa'iza "
Fara'ar umma ta k'aru tana cewa "Masha Allah hakan yayi kyau Allah ya k'ara bud'i "
"Ameeen "

Umma ta bud'e ledar sababbin uniforms ne har guda Biyu da school bag sai takalmi dasu safa sai tarkacen books na skul, "saleem ga kayan ka na makaranta gobe xaka fara xuwa "
Tsallen murna ya fara yana cewa "nagode uncle da umma "
"toh kwashe kake su d'aki ka kwanta domin ka tashi gobe da wuri "

Cikin tsananin murna saleem ya d'auki kayan nashi d'akin shi ya nufa xuciyar shi cike da tarin farinciki
Da kallo umma da abduljabbar suka bisa daga bisani abduljabbar yace "umma gobe xan shige abuja naxo muyi sallama don baxan samu damar shigo wa ta nan ba"
"to Shikenan, daman ina son yin magana da kai akan nauwara "

Nutsuwa yayi tare da mayar da wayar shi cikin aljihun jeans d'in shi ya ce "ina sauraren ki umma"

"nan da two weeks xan je ganin doctor a birnin jiddah na k'asar saudia why not mu tafi da nauwara akan matsalar idon ta ko Allah xai taimaka a dace"
Wani irin dad'i abduljabbar yaji acikin xuciyar shi daman yana da wannan burin sai gashi umma ta fad'i hka don hka yace "okay umma Wannan ba matsala "

"Amman saleem xai xauna a gida shi da fa'iza saboda skul"
Jijjiga kai yayi alamar toh kawai sannan ya mik'e tsaye yace "umma sai munyi waya na wuce "
"Allah ya kiyaye hanya "
"Ameeen "
Daga hka ya fice daga gidan, umma ma d'akin ta ta shige don yau girkin aunty sadiya ne

Lokacin da ya shiga gida jiddah na xaune a parlour tana faman chatting tana ganin shi ta mik'e tsaye da sauri Kafin ta K'arasa wajen shi tuni ya fara hawa stairs don hka ta bishi da sauri har bedroom d'in shi Kafin ya ankara ta fad'o jikin shi tana kukan kissa tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi mishi

Hannu yasa ya tunkud'a ta waje tare da sa key ajikin kofar don Har yanxu bai huce daga abin da tayi mishi ba, ita kuwa jiddah mik'e wa tayi tsaye tare da ta6e baki ta wuce bedroom d'in ta don gobe akwai aiki...

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty }*😘

_wannan page d'in sadaukar wa ce gare ki k'awata Fatima (ummu abdul) ngde da yanda kike k'aunar littafin nan Allah ya bar xumunci ya raya mana Abdul da sauran kannen shi masu xuwa, Ameeen_❤😘

*~Pg 45~*

B'angaren fa'iza da nauwara kuwa Sun dad'e basu yi bacci ba saboda hirar da suka tsaya yi nauwara ta saki jiki sosai suna hira da fa'iza kamar sun shekara da sanin juna daga K'arshe bacci 6arawo ne ya sace su

Washe gari da safe fa'iza ta shirya cikin shirin tafiya skul tare suka fito da nauwara tana yi mata jagora har down stairs suna sakkowa saleem ya fito daga d'akin shi cikin shirin tafiya skul shima yayi kyau sosai

Fa'iza tana ganin shi ta saki baki cikin sauri tace "saleem yaushe aka saka ka a skul d'in mu"
Saleem cikin jin dad'i yace "aunty fa'iza jiya uncle da dare ya kawo min uniform ya sanya ni a makarantar ku "
Baxan iya kwatanta muku dad'in da fa'iza taji ba balle nauwara kuma har da hawayen farinciki addu'a sosai ta dunga yiwa bayin Allahn nan

Suna kammala breakfast saleem da fa'iza suka tafi skul yayin da aka bar nauwara ita d'aya xaune a falo yau gaba d'aya cike da farin ciki take har umma ta sauko k'asa
"aa nauwara ke kad'ai xaune a parlour duk sun gudu skul sun barki "
"Ehh umma ji nake kamar na bisu "
Cikin tausayin ta umma tace "kwantar da hankalin ki nauwara Insha Allah komai xai xo ya shige "

Har k'asa ta sakko ta gaida umma ta amsa mata cikin fara'a sannan tace "dafatan Kinyi breakfast? "
"Ehh munyi dasu fa'iza da saleem "
"okay yayi kyau hkan, Bari nima naje nayi "

Daga hka umma ta K'arasa wajen dinning table, bayan ta kammala breakfast d'in ta dawo cikin parlourn xama tayi kusa da nauwara ta kamo hannun ta fara magana kamar hka
"nauwara jiya da dare bayan kunshiga d'aki abduljabbar yaxo munyi magana nan da two weeks xan je jiddah domin ganin doctor shine muka yanke magana xamu tafi dake a duba miki idanun ki "
Chapter 25 · 0% Book details