← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 73

Sashe 47

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A Wannan lokacin jiddah ta fara ta ta rashin mutuncin ta da taji nauwara wai ciki ne da ita gashi yanda ta ga ana wani lalla6a ta daga abduljabbar d'in har mahaifiyar shi da sauran en uwan shi ta rasa inda xata sa kanta taji dad'i shine ta fito da salon cusguna wa nauwara amman bata ta6a kulata don hka sai ta yanke shawarar mai gaba d'aya

*BAK'AR RANA!!!*

Cikin nauwara ya kai tsawon 6 month's ya girma sosai kamar yau ta gama ayyukan ta kamar ko yaushe ta saboda yau abduljabbar xai shigo kano kuma a d'akin ta xai sauka ta gama shirya mishi komai tana shirin shiga wanka bacci ya dauke ta daman a gajiye take bata farka ba sai bayan sallahr la'asar dakyar ta iya mik'e wa ta shiga toilet don yin wanka ta gama wankan kenan tana cikin d'aura towel sai taji wata muguwar k'arar abu kamar k'arar harbi gabanta ne yayi mugun fad'uwa jikin ta ya hau 6ari da sauri ta yayibo hijab d'in da ta shigo dashi toilet d'in ta fito a kid'ime

Turus tayi taja ta tsaya cikin tsananin kad'uwa ganin abduljabbar ne da sauri ta kawar da kanta saboda ganin yanda fuskar nan tashi a murtike ba alamar fara'a idanun nan nashi jawur dasu jikin shi sai faman 6ari ya ke saboda tsabar 6acin rai da sauri ta K'arasa wajen shi tare da kok'arin rik'e mishi hannu wata irin tsawa ya daka mata wadda har sai da d'an cikin ta ya motsa Kafin ta dawo dai dai taji saukan wani lafiyayyen mari guda biyu cikin kid'ima ta d'ago kanta ta kalle shi Idan idon ta ba gixo suke mata to hawaye ne ke fita a cikin su cikin fusata yace
"na tsane ki nauwara na tsane ki na tsane ki nayi nadamar had'u wa ta dake nayi dana sanin auren ka kin cuce ni kin yaudare ni kinci amana ta me na rage Ki dashi a tsawon xaman mu "
Daskare wa tayi a wajen jin maganganun shi tamkar a mafarki cikin rawar murya tace
"me nayi maka Yah abduljabbar meya faru ka sanar da ni don Allah "
A matuk'ar fusace yace "Har ni kike tambayar abin da kika aikata?? "

Hannu ya dad'a fiddawa xan mare ta caraf yaji an rik'e hannun nashi da sauri ya d'ago kanshi don ganin waye hada ido yayi da umma kafin ya ankara yaji an mare shi cikin tsananin mamaki ya ke kallon umma ranta a 6ace tace
"da hankalin ka abdul xaka dunga dukan mace mai ciki ko ka haukace ni?"
"umma bakisan me tayi min ba fah kama ta nayi Tana...... "
"shiiiii ban tambaye ka abin da ya faru ba shin yau ka ta6a ganin nauwara inace ke ne mutum na farko da xaka fara bada sheda akan ta shine babu bincike ba komai ka hau kai ka xauna ko "
"umma ba wani bincike asirin tane ya cika kawai don na hak'ura da ita har abada"
"wlh wllh Idan ka sake ta sai dai ka nemi wata uwar bani ba kaji na rantse "
A xuciye ya fice daga d'akin yayin da umma ta juya wajen nauwara sai taga tayi baya xata xube cikin sauri ta K'arasa ta rik'e ta cikin tashin hankali ta fara kiran sunan ta amman shiru kake ji ta suma........

Aishat A muh'd
🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 73~*

" Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun nauwarahhh!!!" umma ta fad'a da k'arfi tana jijjigata amman ko motsi Bata yi ba, a tsaye yake a falo xuciyar shi sai tafasa take saboda 6acin rai ruwa ya d'auko a frige yasha wajen rabin robar ragowar ya d'aga robar ya xuba a kanshi sannan yayi cilli da robar yana huci a dai dai lokacin yaji umma tana k'walla wa nauwara kira da gudu yayi bedroom d'in ta jiddah da take tsaye kusa dashi kamar ta yi rawa don murna tabi bayan shi da sauri

Yana shiga d'akin idanun shi suka yi mummunan gani nauwara a kwance jini yana bi ta kafar ta ga umman shi na kuka tana kok'arin d'ago ta cikin sauri ya K'arasa xai taimaka mata
"wlh abduljabbar kada ka kuskura ka ta6a "
Cikin tsawa ta fad'i hkan da sauri ya janye hannun shi ya fice daga d'akin toh jiddah ma batayi gigin k'araso wa ba ganin ba fuskar magana

Hka umma dakyar ta iya kai nauwara mota daman jiddah ce ta kirawo ta a waya taxo abduljabbar xai kashe nauwara lokacin ma fitar ta kenan daga gida xata je gidan aunty kausar bata jin dad'i shine ta taho hankalin ta a matuk'ar tashe shine taxo ta tarar da wannan tashin hankali
Tun Kafin su K'arasa asibitin umma tayi wa aunty sadiya waya kan ta same ta a asibitin a lokaci d'aya suka iso asibitin ganin umma tana kuka aunty sadiya a tsorace take tambayar ta lafia bud'e mata bayan motar tayi ba k'aramin firgita tayi ba da taga halin da nauwara take ciki da gudu ta shiga cikin asibitin bata dad'e ba suka dawo da wasu nurses biyu da d'an k'aramin gadon da ake tura mara lafia suka d'auki nauwara aka dora ta akayi emergency room da ita
Nan doctors suka Duk'ufa akan ta har Allah ya taimaka suka samu ta farfad'o bayan sun tsayar da jinin dake xuba a jikinta, suka sanya mata drip bayan sun mata allurar bacci sannan suka fito lokacin da likitan suka fito Har abba da abdulkareem sun k'araso hankalin su a tashe

Suna xaune a office d'in doctor suna sauraren shi bayan ya gama rubutu acikin file ya rufe shi sannan ya fara da cewa
"Alhmdullilah munyi nasara ta farfad'o yanxu muna buk'atar jini don a k'ara mata bcoz tayi bleeding da yawa "
"doctor cikin fah ya xube ne?? "
Umma ta tambaya cikin tsananin tashin hankali da tsoron jin abin da doctor xai ce d'an murmishi yayi sannan yace
"babu abin da ya samu babyn yana nan lafiyar qlau "
Ajiyar xuciya umma ta saki wadda sai da kowa ya ji a wajen abba yace
"ina abduljabbar ne ko ba yau naji yana cewa xai shigo kano ba?"
Nan take fuskar umma ta koma yanayin 6acin rai tsantsa ba wanda ya sake magana ganin hka yasa doctor ya fahimta akwai wata maganar Mai mahimmanci da xasu yi ta sirri don hka ya tashi ya bar musu office d'in
Yana fita umma ta fad'a musu komai da abin da ya faru sannan ta d'ora da cewa
"wai a fad'ar shi ya shigo d'akin ta ya kama wani namiji a kwance kan gadon ta ba kaya a jikin shi sai short nicker ga under wears d'in nauwara a had'e da kayan shi da ya cire ita kuma nauwara tana toilet bai yi nasarar kama shi ba har Harbin da yayi mishi bai same shi ya gudu "
Cikin kukan takaici umma ta cigaba da cewa
" kamar bai san halin nauwara ba daga ganin abu ba bincike ba komai ya fara dukan ta da tsohon ciki "
Shiru duk suka yi aka rasa mai magana a cikin su dakyar abba ya iya cewa "Alhamdullilah tun da tana nan lafia sannan cikin bai xube ba shi kuma yaje rayuwa ce nauwara 'ya na dauke ta ba Inda xata je muna tare da ita Allah ya bata lafia "
"Ameeen '
Suka amsa gaba d'aya sannan ya tashi yana cewa "abdulkareem muje ayi test d'in jinin mu idan yayi dai dai sai a diba "
Abdulkareem wanda gaba d'aya baya cikin nutsuwar shi ya mik'e tsaye a sanyaye suka fice daga office d'in

Lokacin da nauwara ta tashi daga baccin duk abin da ya faru ya dawo mata tayi kuka tayi kuka Har taji ba dad'i dakyar umma ta rarrashe ta tayi shiru wanka ta taimaka mata tayi ta fito sannan ta gyara jikin ta sai ga fa'iza nan tana kuka wiwi ta shigo d'akin ta rungume nauwara umma da aunty sadiya suna gefe suna kallon su cike da tausayin su

Ba k'aramin dauriya nauwara tayi ba da tawwakali ta kauda duk wani abu acikin xuciyar ta amman ta rame sosai tayi fari sai katon ciki kamar xai rinjaye ta Sati d'aya tayi a asibiti suka sallame ta bayan sun tabbatar ba wata matsala haka suka tarkato suka dawo gida xuciyar kowa ba dad'i

6angaren abduljabbar ma baxan iya kwatanta muku halin da yake ciki ba ya bi duk ya rame saboda tsabar tashin hankali umma bata amsa gaisuwar shi abba ma baya sakar mishi fuska kamar da ana cikin hka aka tura shi wani course na tsayin shekara 2 wanda Indai yayi ya samu nasara xa'a k'ara mishi matsayi ba k'aramin jin dad'in hkan yayi ba saboda xai yi nesa da nauwara

Hka ya tarkata ya tafi bayan ya lalla6a iyayen shi sun d'an sakko daga fushin da suke dashi suka bishi da addu'ar fatan alkhairi har ya tafi bai k'ara ganin nauwara ba

Jiddah kuwa hankali ya kwanta tayi nasarar raba abduljabbar da nauwara masoyan da suke masifar k'aunar junan su yanxu bata da damu ko Kad'an

_kuyi hak'uri da wannan wlh na fita unguwa ne sai kuma gobe xaku ji ni_

Aishat A muh'd
☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 74~*
Chapter 47 · 0% Book details