← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 73

Sashe 23

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parking yayi a harabar asibitin ya bud'e kofar motar ya fito da kafar shi d'aya kamar ance ya juya gefen shi ya hango su nauwara a wajen ta dafa talatuwa tana yin tafiya a hankali saleem yana bayan su, yayi mamakin yanda yaran suka koma sunyi kyau sosai koma wa yayi da kallon shi kan nauwara wadda take sanye da riga da siket english wears kayan sun kar6e ta sosai a hankali yaji xuciyar shi tana ayyana mishi wasu batutuwa sai kawai ya kawar da wannan tunanin a cikin xuciyar shi ta hanyar fita daga motar ya nufi office d'in doctor cikin tafiyar shi ta kasaita

Bayan sun gama magana da doctor yake fad'in nan da 5 days xai sallame su don aikin yayi kyau sosai daga nan ya tashi ya fice daga office d'in lokacin da ya duba wajen dasu nauwara suke xaune yaga basa nan mybe don ganin mangarib ta gabato ne cikin nutsuwa yake driving d'in shi har ya k'araso gidan shi xuciyar cike da wasu irin yanayi wanda yake kok'arin karyata hakan...

*BAYAN K'WANAKI 5*

Acikin wad'annan kwanakin nauwara ta mik'e ras tana tafiyar ta kamar da amman sai dai da taimakon sanda take dogara wa tun da bata gani da idanun ta

Ranar da doctor ya sallame su abduljabbar ya baro tarin ayyukan shi a office ya taho kano, yana xaune shi da abdulkareem a gaba mota su talatuwa suka fito tana rik'e da tarkacen kayan su yayin da saleem yake rik'e da sandar nauwara yana yi mata jagora xuba mata ido abduljabbar yayi yana kallon ta yayin da abdulkareem yake kallon shi cikin tsokana yace

"Hmm captain ko da ita xa'a k'ara a ta 2 irin Wannan kallo hka?"

Harara ya watsa mishi yana cewa "kai Wlh abdul ka fiye sa ido ni just tausayi take bani "
"alright Idan tayi tsami maji don daga tausayi yake rikid'ewa ya xama sooo"

Har ya bud'e baki xai yi magana suka k'araso wajen don hka yayi shiru yayin da abdulkareem yake yi mishi dariya k'asa k'asa tuni ya cika yayi fam sai hararar shi yake dakyar ya iya danne dariyar yace wa nauwara wad'anda suka shiga motar

"Sannu nauwara Allah ya k'ara lafia "

Cikin d'an jin kunyar shi don ta d'au muryar shi tace "Yawwa uncle abdulkareem Ameeen ngde, ina su aunty maryam? "

Cikin mamaki abduljabbar ya juyo yana kallon abdulkareem cike da neman Karin bayanin yanda akai ta shaida muryar shi, gira ya d'aga mishi yana er dariya girgixa kai kawai yayi ya mayar da hankalin shi kan danna waya

Gidan shi kai tsaye suka nufa abdulkareem yayi parking sannan yace "captain ni baxan shiga ba fah bcoz ina sauri akwai inda xan je"
Baice komai ba ya bud'e motar ya fito sannan yace "ka tafi da talatuwa ka mayar wa da aunty sadiya ita "
Ya juyo da kallon shi kan talatuwa yace "Mun fah gode "

"Ah ba komai yalla6ai "
Talatuwa tace tana kok'arin fito da nauwara wadda tayi suman xaune jin hadaddiyar muryar abduljabbar gaban ta ya hau fad'uwa kamar ta ta6a jin Wannan muryar

Kallon saleem yayi yace "Yah boy taimaka mata mu shiga gidan "
"toh uncle "

Saleem ya fad'i hakan yana kok'arin kama sandar nauwara da hka yayi gaba suna binshi a baya har cikin gidan, tana xaune kan kujera da laptop a gaban ta tana aiki a cikin ta taji sallamar shi kamar a mafarki da sauri ta mik'e tsaye cikin mamaki tace
"my darling lafia? "
Ta tambaye shi ganin sai weekend ya saba xuwa waje ya samu ya xauna sai lokacin hankalin ta yayi kan su nauwara nan take annurin fuskar ta ya dauke

"su waye wad'annan ?"
"ai Kya basu wurin xama Kafin nayi miki bayani?"
Bata ce komae ba ta samu waje ta xauna tana karkad'a kafa ganin hka yasa abduljabbar yace
"oya saleem ku xauna "

Saleem ya kama nauwara xai xaunar da ita kan kujera da sauri jiddah tace "keee baka da hankali xaka xauna min kan kujera "

Tuni nauwara da saleem sun tsorata jikin su ya fara 6ari na tsoro, ran abduljabbar ya 6aci da abin da jiddah tayi musu ya kallo ta cikin tsananin 6acin rai yace
"Hey wlh kada na k'ara jin Kinyi musu tsawa i swear xan miki abin da xaki yi nadama"

Mtswww ta buga uban tsaki tare da fisgar laptop d'in ta xata bar parlourn ai kuwa yasa hannu ya fusgo ta tare da bata wani kyakkyawan mari cikin tsananin jin takaice yace

"ni sa'an kine xaki yi min tsaki, Kinsan kuwa yanda na tsani ayi min tsaki Idan kika k'ara yi min sai na fasa Wannan bakin stupid gal"

Ya K'arasa fad'i yana tunkude ta xaman en bori jiddah tayi a k'asa tana kuka sosai na takaicin abin da abduljabbar yayi mata gaban wad'annan yaran, tuni su nauwara da saleem sun tsure ganin yanda yake masifa

Zama yayi yana dafe kanshi sai huci yake, jikin nauwara na 6ari murya tana rawa tace "am... am don Allah ka... kayi hak'uri abin da kayi mana mungode Allah ya saka da alkhairi but ka barmu mu tafi Don........ "
Bata K'arasa fad'in abin da take so ta fad'a ba abduljabbar ya katse ta ta hanyar buga mata wata uwar tsawa da ba k'aramin firgita nauwara da saleem tayi ba balle jiddah da sauran kiris ta runtuma d'aki da gudu tsabar tsorata............

????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘??
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty }*??

*~Pg 41~*

Cikin tsananin fusata ya fara magana "Idan na k'ara jin Kinyi magana sai na 6a66arar da ke,bana so ina magana ana tsoma min baki "

Tsit kake jin parlourn yayi can ya bud'e baki ya kirawo larai er aikin jiddah da sauri ta k'araso wajen tana tsugunna wa sai da ya share kusan 5mint sannan ya bud'e baki yace
"na baki 20 mint kije ki gyara bedroom d'in cikin parlourn nan "
Da sauri larai tace "angama yalla6ai "
Ta mik'e ta shiga cikin bedroom d'in tana aiki da sauri don cika umarnin uban gidan nata

Har larai ta gama ta dawo suna xaune babu mai cewa komai, da ta gaya mishi ta gyara sai da yaje ya duba ya tabbatar komai yayi sannan ya fito ya ce
"Ki kai su cikin bedroom d'in sannan ki had'a mata ruwan wanka tayi sai ki basu abinci ina son ki dunga kula da ita saboda bata gani "
Jiki na rawa larai tace "toh" saboda yanda fuskar nan tashi take a tur6e ne ta taimaka wa nauwara ta mik'e sannan ta rik'e ta har sun juya ya dakatar da su ta hanyar sake wa larai gargad'i
"ina son ki kula dasu sosai wlh Idan na same ki da bakya mai da hankali wajen abin da na saki xan kore ki "
"toh yalla6ai Insha Allah xan kiyaye"
D'aga kafad'a yayi alamar ko a jikin shi bai dameshi ba taja su nauwara xuwa cikin d'akin

Mai da hankalin shi yayi kan jiddah wadda ta saki baki tana binshi da kallo kamar ba abduljabbar d'in ta ba ji yanda yake bada umarnin kula dasu kamar wasu en uwan shi na jini maganar da yayi ita ta dawo da ita hayyacin ta ya fara da cewa
"gasu nan basai nace ki kula dasu ba ko ki k'untata musu ba kin san ni dai bana iya d'aukan rainin hankali "
Yana gama fad'in hka ya tashi ya nufi upstairs ya bar jiddah cike da tunanin maganar don ta kasa gane abin da yake nufi can jimawa kamar wadda aka tsunkula da xaburo tana cewa kuttt wlh baxan yarda na xauna da wad'annan talakawan yaran ba agidan nan (hmm da dai bamu san asalin balbela ba sai muce...... readers sai ku K'arasa lol)
Tabbb Hka kawai ya jajibo mana mutane gida cikin sauri ta suri wayar ta number umma ta kirawo tana jin ta d'aga ta fashe da kuka tuni umma ta rikice tana tambayar ta lafia, cikin shashshak'ar kuka tace "ba abduljabbar bane ya kawo mana wasu yara gida ba, ni dai Gaskia umma kiyi mishi magana wlh baxan xauna dasu a gidan nan ba "

Shiru umma tayi ita kanta ta fara jin haushin jiddah amman da tayi wani tunani yasa tace "kiyi hak'uri jiddah wad'annan yaran da kika gani taimakon su xai yi tsintar su............ nan umma ta bata labarin da abduljabbar ya basu game dasu Sannan ta d'ora da cewa ni naga yaran wlh abin a tausaya musu ne Idan kuka rik'e su Allah ne kad'ai yasan ladan da xaku samu"
Tun da umma ta fara magana jin Bata goyi bayan ta ba a wannan time d'in yasa ta cika tayi fam da ita kamar ta fashe bata k'ara jin Mai xata ce ba ta yanke kiran xube wa tayi akan bed sai masifa take nan ta kirawo farida k'awar ta ta ladafta mata abin da yake faruwa nan kuwa tayi mata hud'ubar kan kada ta yadda ta tada masifa kawai ita ba ta yarda ba...

Ranar yini tayi tana bala'i ita kad'ai don ba wanda ya kula ta Washe gari da safe abduljabbar ya wuce abuja saboda tarin aikin da yake gaban shi ko takan jiddah bai bi ba

Tun da ya tsallake ya tafi jiddah ta shiga yiwa su nauwara rashin mutunci ta ko'ina don ko larai sai tayi k'wana wajen 3 bata shiga d'akin da suke ba saboda tsabar rashin mutuncin Jidda da bala'in ta sai dai idan ta samu lokacin ta tafi aiki sai ta shiga ta kula dasu

Ganin hka larai tana satar jiki ta shiga yasa ta koma sanya wa d'akin key ta sanya a jaka tatafi dashi aiki sai ta dawo xata bud'e su

wahala Kala Kala take d'and'ana musu ba k'arami ba kuwa don hka kawai take jin tsanar nauwara kamar ta shak'e ta ta mutu, gaba d'aya sai suka koma kamar da sun bi sun rame sosai saboda wahalar da take gana musu

Hka rayuwa ta cigaba da tafiya don abduljabbar sai da yayi 3 month Kafin ya waiwayi gida saboda ayyukan dake gaban shi, hkan ba k'aramin yiwa jiddah dad'i yayi ba saboda ta samu damar axabtar dasu son ranta
Chapter 23 · 0% Book details