← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 73

Sashe 24

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yau ranar sunday da yammaci jiddah lokacin en rashin mutuncin ne akan ta fiye da ko yaushe tasa larai ta fito dasu nauwara xuwa falo sai da ta k'are musu kallo up nd down sannan ta shek'e da dariyar mugunta ganin yanda duk suka yi wujiga wujiga dasu Kafin ta bud'e baki tace
"matsiya ta yau xaku bar gidan nan don na gaji da ganin ku wallahi na tsane ku, don hka larai oya fitar min su daga cikin gidan nan yanxu yanxu "

Cikin matuk'ar kad'uwa larai tace "kiyi hak'uri hajia don Allah ki barsu ina tsoron fushin yalla6ai "
Wata muguwar harara ta watsa mata cikin tsawa tace "keee larai wlh ki shiga taitayin Ki ina magana Kina musa min toh wlh xan iya korar ki kema Idan baki aikata abin da na saki ba"

A tsorace ta kamo sandar nauwara ta fara yi mata jagora saleem yana binsu a baya ita nauwara ko a jikin ta saboda gwara lokacin da suke bara sunfi jin dad'in rayuwar su fiye da nan Wannan wahalar ta isa hka ko ina suka je sai tsana da tsangwama Allah ya isa tsakanin mu dake uncle sai Allah ya saka mana duk rashin Imaninka ne da kwadayin dukiyar da ba taka ba ya janyo mana shiga wahalar rayuwar nan....

Da hka larai ta fitar dasu da gidan sun d'an yi tafiya Kad'an sannan taja ta tsaya cikin tsananin tausayin su tace "Kuyi hak'uri nauwara hka halin ta yake sam bata girmama *D'AN ADAM* (littafin rufaida Omar) musamman talaka nima hak'uri nake da ita Allah ya taimaka muku a duk inda kuka shiga "
Ta xira hannu ta kunce xanin ta tare da d'auko wata 200 ta bawa saleem sannan ta cigaba da cewa "ga Wannan kud'in ko ruwa kwasha kiyi hak'uri "
Murmishin yak'e tayi tace "ba komai larai Mun gode matuk'a da yanda kika rik'e amanar shi wajen kula damu tsakani da Allah,nasan kema abin ne yafi k'arfin Ki shi yasa sai wata rana ki sani baxan ta6a manta wa da ke ba "

Da hka saleem yaja sandar ta sukayi gaba tun tana hango su har suka fita a layin sosai taji tausayin su hawayen da suka xubo a fuskar ta ta goge sannan ta juya ta koma gidan

A parlou ta tarar da jiddah sai waya take tana faman kyalkyala dariya tana bawa farida labari ta jefar da kwallon mangoro ta huta da k'uda ranar yini tayi wasai da ita sai farinciki take hankalin ta kwance

????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘????
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*??

*~Pg 42~*

Tafiya kawai suke duk inda suka samu jefa kafar su suke,har suka k'araso kan wani babban titi saleem yaja ta xasu tsallaka Ko tsaya wa duba wa bai yi ba yasa kai

Sun xo dai dai tsakiyar titin wata mota ta taho da gudu sai da taxo daf dasu aka ja wani uban birki wanda ya tsorata saleem da nauwara suka xube a k'asa cikin matuk'ar tsoro

A nutse ya fito daga motar yana sanye da army uniform d'in kallon su kawai ya tsaya yi cike da tsantsar 6acin rai tun daga nesa ya shaidasu kuma yasan ba wanda xai kore su sai jiddah, dakyar ya iya bud'e baki yayi magana saboda 6acin rai

"saleem taimaka mata ku shigo motar "
Abin da ya iya cewa kenan gaban nauwara ne ya fad'i tabbb yanxu gidan nan xamu koma matar shi tana axabtar damu ai har gwara hindatu akan jiddah

Cikin dakiya tace "no ba sai mun koma gidan ka ba hakan ma mungode "
Da ace tana gani da Idanunta da taga irin hararar da abduljabbar ya watsa mata cikin tsawa yace "keee wace da xaki hanani yin abin da nayi niyya"
Ita dai nauwarah shiru tayi tana jin shi ganin bata da niyyar tashi yasa shi K'arasa wa inda take hannun shi yasa ya d'ago ta cak ya nufi motar shi yayin da nauwara tsoro ya kamata baya xaunar da ita sannan ya shiga motar bayan saleem shima ya shiga ba wanda ya k'ara magana a cikin su har ya k'araso gidan umma
Bai k'ara yi mata magana ba ya sake d'aukar ta bai dire ta ba sai a parlourn umma kan kujera ya xaunar da ita sannan ya kirawo umma cikin mamaki take kallon su don ta shaidasu

"lafia abdul? "
Shiru yayi mata don shi bai ma san me xai ce mata ba ana hka Abba ya shigo falon shima tambayar abduljabbar d'in yake cikin 6acin rai yace
"Abba, umma ina neman alfarma a wajen ku don Allah ku rik'e min wad'annan amana, gasu nan a hanya na gansu kuma na tabbatar jiddah ce ta kore su daga gidan"
Murmishi abba yayi yace "Ah Haba my boy kada ka damu Insha Allah xamu rik'e maka su tsakani da Allah "
Umma ta sauke nannauyar ajiyar xuciya tace"Allah ya taya mu rik'o "
"Ameeen " abba ya amsa tashi yayi suka fita da Abba yana tausar shi kan Yayi hak'uri ganin ranshi ya 6aci sosai Sha'anin wasu matan sai hak'uri kada ya kula ta, shi dai abduljabbar jin shi kawai yake don Allah Allah yake ya je gida

Ai kuwa yana shiga gidan tun daga falo yake k'walla wa jiddah Kira, dummmm gaban ta ya fad'i jin muryar wanda bata ta6a xaton dawowar shi kusa ba tuni jikin ta ya hau 6ari na tsoro ta da d'a lafewa a d'aki taki amsa kiran hakan ba k'aramin sake tunxura shi yayi ba cikin sassarfa ya hau upstairs ya nufi ⌐part d'in ta

Duka d'aya Yayi wa kofar ta bud'e hakan ba k'aramin k'ara kid'ima jiddah yayi ba bai yi wata wata ba ya fisgo ta da karfi har ta buge kanta da faffad'en kirjin shi tace washhh tare da dafe kan nata hannu yasa murd'e hannun ta da karfi ta k'walla k'ara cikin kuka ta fara rokan
"abduljabbar don Allah ka bari da xafi fah, toh wai menayi maka daga dawowar ka?? "
Xuba mata idon shi yayi wanda suka yi matuk'ar ja saboda 6acin rai "ohhh bakisan me kika yi ba,bari na gani ko xaki tuna da kanki "

Nan ya cigaba da murd'e mata hannu da jan gashin kanta axaba tayi axaba jiddah batasan lokacin da fad'a mishi ita ta Kori su nauwara ba cikin kuka ta cigaba da cewa
"don Allah abdul kayi hak'uri baxan sake ba I'm so sorry pls"
Cika ta yayi tare da tura ta k'um ta bige da katakon gado wani wahalalen ihu ta saki da muryar ta dashashshiya wanda kuka yasa ta dashe ficewa yayi daga d'akin ya bar jiddah cike da tsantsar tsanar su nauwara a xuciyar sai dai kuma taji dad'i tun da ta kore su daga gidan ta,dakyar ta iya tashi ta shiga toilet wanka tayi sannan ta fito ta shirya ko make up bata tsaya yi ba ta xari key d'in mota da wayar ta fice wa tayi daga gidan idanun ta sun kumbura saboda kuka........

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*😘

_Sadaukar wa ce gare ki auntyn mu (Aunty mamy ) nagode da yanda kike k'aunar littafin nan, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike_😘

*~Pg 43~*

Yana fita daga falon umma, cikin tausayin su umma ta K'arasa wajen nauwara ta dafa mata kafad'a sannan tace "kada ki damu nauwara Insha Allah Kunxo inda xa'a rik'e ku tsakani da Allah, amman xan so naji takaitaccen tarihinki? "

Tun da ta fara magana nauwara taji k'aunar wannan matar ya kamata tana addu'a a xuciyar ta Allah yasa *K'ARSHEN WAHALAr* su ne yaxo K'arshe wata sassayan ajiyar xuciya ta saki batai k'asa a gwiwa ba nan ta ladafta wa umma labarin su Kaf, don ji tayi baxa ta iya yi mata k'arya ba kamar yanda tayi wa aminu da saude...

Umma batasan lokacin da hawayen tausayin su ya xubo mata ba Lallai Wannan k'anin baban nasu ya cika axxalimi, macuci, mayaudari labarin ba k'aramin ta6a mata xuciya yayi ba

"kiyi hak'uri nauwara komai lokaci ne akwai ranar sakamako, tun anan duniya Kafin aje gaban Allah, da ixinin Allah Kunxo inda xa'a share muku hawaye ni na d'auke ki a matsayin diyata ke da saleem "
Wani dad'i ne ya kama nauwara har hawayen farinciki ya xubo mata tama kasa cewa umma komai don murna, hannu umma tasa ta goge mata hawaye tace "mene na kuka kuma ?"
"umma ba dole nayi kukan farinciki na samu mahaifiya bayan ammi na, ngde sosai umma Allah ya saka miki da mafificin alkhairi "
"shiii ya isa hka godiyar nauwara "
Murmishi tayi wanda rabon ta da tayi shi tun xamanin suna rayuwa tare da iyayen ta da en uwan ta, "toh umma yi hak'uri na dai na, sai dai xan tayi miki addu'a yanda kika taimake mu ke ma Allah ya taimaka miki akan komai na go........... "
Da sauri ta dafe bakin ta bata K'arasa fad'i ba tace "ohhh umma yi hak'uri na mance "
Dariya sosai ta bawa umma hannun ta tasa ta rik'e kumatun ta duk biyun tace "ba komai 'yata sai ki kiyaye gaba"
Gaba d'aya suka sa dariya kamar wad'anda suka dad'e da haduwa sosai umma take jin k'aunar yaran a xuciyar ta

Nan ta taimaka wa nauwara ta tashi tayi mata jagora xuwa d'akin FA'iza sai da shigar da ita toilet sannan ta fito xuwa down stairs anan ta kai saleem shima nashi bedroom d'in tace "kayi wanka d'ana saleem sannan idan ka gama sai ka fito falo, nan ka d'auke shi tamkar gidan Kune ka saki jikin ka"
Rungume ta yayi yana cewa "toh umma ina ganin ki kamar ammi na? "
Murmishi tayi ta dafa mishi kanshi tace "Yawwa my boy ina son ka dunga ganina kamar ammin ka ,duk abin da kake so ka tambaye ni kamar yanda kake tambayar ammi da "
"toh umma thank u so much "
Daga hka ya cikata ya shiga toilet umma ta bishi da kallo fuskar ta d'auke da Murmishin jin dad'i
Chapter 24 · 0% Book details