← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 73

Sashe 54

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da mummunan labarin 6atan yaran shi suka tashi don hka duk sun bi sun firgice saboda sune suka san sirrin gaba d'aya kuma Idan suka sha wahala xasu iya tona musu asiri Lallai Wannan karan shegiyar yarinyar nan (wato nauwara) da babban shiri ta xo Cewar Alhj salisu kenan nan suka fara binciken inda yaran shi suke da kuma Inda nauwara da saleem suke

6angaren su abba sun gama shirin su sai jiran ranar shiga kotu duk sun Duk'ufa da addu'a Allah ya basu nasara akan Alhj salisu sun samu barrister wanda yasan aikin shi sosai shima yana nashi binciken cikin K'warewa irin ta aikin shi

******
Ranar monday xa'a fara xaman kotu duk wani wanda ya kamata ya hallara a kotun an hallara waje ya cika yayi makil da jama'a don sauraran wannan k'ara mai cike da cin amana tsantsa da xalinci

A wannan rana Alhj salisu yayi nadamar abin da ya aikata sau ba adadi musamman lokacin da ya tsaya a gaban kotu gashi suka had'a ido da ammi nauwara saleem da kuma inna da baffah mahaifin shi duk jikin shi yayi matuk'ar yin sanyi bai ga alamar samun nasara ba sam

Toh dai a Wannan xaman da aka yi ba'a samu wasu kwararan hujjoji ba saboda su nauwara basu da wata karfaffiyar hujjar su akan Alhj salisu don hka kotu ta d'aga k'arar xuwa 2 weeks masu xuwa

Haka aka tashi daga kotun abin da ya ban mamaki shine me ya hana abduljabbar xuwa bayan shi yake da kwararan hujjojin a hannun shi ......

Aishat A muh'd

[4/12, 15:35] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 81~*

Acikin satin nan biyu da aka basu xasu koma kotu sun Duk'ufa da addu'a sosai tare da cigaba da bincike toh duk wasu binciken da suke basu samu wasu hujjoji ba don gaba d'aya Abduljabbar ya bi ya tattara su a wajen shi kuma bai sanar da kowa ba kuma yak'i xuwa har yanxu

Har aka sake shiga kotu xama na biyu babu wasu kwararan hujjoji kan dukiyar su ce tunda ga takardun duk dukiyar su nauwara but sunan Alhj salisu ne akai balle axo batun shi yasa aka k'ona gidan su har safah ta mutu da mai gadi don hka barrister di'n su nauwara shi ya nemi alfarmar a sake d'aga k'arar en jarida sosai sun taru a wajen suna d'aukan rahoton wannan Shari'ar mai matuk'ar d'aure kai da ban mamaki

Wani murmishin mugunta Alhj salisu yayi lokacin da suka had'a ido da nauwara wajen da take ya nufa duk da ta tsorata da ganin hakan amman hka ta dake ta tsaya wani d'an iskan kallo yake yi mata yace
"Wato ke ga shegiyar mara kunya koh, da ni xaki ja uban ki ma na cikin kabari yayi Kad'an balle ke "
Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa
"nasan xanyi nasara kuma ki shirya mutuwar ki ke da saleem kuma sai na auri uwar ki Kina kallo Kafin ki mutu shegiya ke ga mai taurin kai xanga uban da ya tsaya miki "
"Hahahaha loser "
Yatsine fuska tayi sannan ta dalla mishi harara tare da cewa
"wlh kayi Kad'an sai naga bayan ka mugu axxalimi kuma da kake cewa sai ka kashe ni *a rayuwa da mutuwa a hannun Allah take* sau nawa kake yunkurin kashe mu Allah bai yi ba daman ance *d'an hakin da ka raina shike tsone maka ido* kuma Insha Allah sai na tsone maka idanun ka gaba d'aya da ikon ubangiji ai xalinci baya dore wa maci amana butulu"
Sam bai yi mamakin abin da nauwara tayi mishi yasan xata fad'i abin da yafi hka ma ba K'aramar mara kunya ce ba maganganin ta sun 6ata mishi rai amman da yake d'an duniya ne sai ya maxe Ya nuna ta da hannu yace
"xaki gani? "
Murgud'a mishi baki tayi ita ma tace
"xa dai ka gani wlh "
Tana gama fad'in hka taja tsaki tare da juyawa ta tafi abin ta shima tsakin yaja tare da cewa
"yanda na kashe uban ki har lahira kema Hka xaki bishi "
Yana gama fad'in hka ya juya ya shiga mota suka tafi, kash! rashin sani yafi duhu inji malam bahaushe da yasani bai kula nauwara ba har sunyi magana haka ba saboda d'an leken asirin abduljabbar yana gefe yana d'aukan su video a waya ya tura wa abduljabbar ta what's app sannan ya tafi

Hka su nauwara suka koma gida cikin rashin k'warin gwiwa amman sun sake damarar sake bincike na sosai

Bari na waiwayi 6angaren abduljabbar naga ko me yasa yak'i xuwa

*******

Yana xaune kan kujera yana sanye da white d'in three quarter da maroon di'n riga mara hannu irin ta shan iska fuskar nan tashi d'auke da Murmishi laptop d'in shi tana kan kafar shi yana sarrafa ta cikin kwanciyar hankali yana kur6an xaxxafan coffee yana kallon duk yanda ta kasance a kotu yana d'an murmishi wani lokacin har d'an darawa yake Idan yaga yanda Alhj salisu yake hararar nauwara yana jifan ta da kallon tsana k'arara

Shigowar message yaji a cikin d'aya daga cikin wayoyin shi dake xube a gefen shi hannu yasa ya d'auka ya bud'e password d'in wayar sannan ya duba cikin what's app nashi yaga videon aka turo mishi bud'e wa yayi ya nutsu yana kallo murmishin mugunta ya saki tare da furxar da wani xaxxafan huci a hankali yace
"d'an iska xaka san baka da wayo wlh dole wannan Karon na uku na bayyana don na nuna maka kai k'aramin k'waro ne "
D'an turo ya saki tare da rufe laptop d'in shi ya d'an kwanta kan kujerar yana kallon wani film a mbc 2 wanda suke yanxu mai suna death race

Lokacin da suka xo da yaran Alhj salisu abuja da farko k'in fad'in komai suka yi sai da suka ji wahala kamar xasu mutu sannan suka fad'i komai sosai abduljabbar ya gigita da jin wannan rashin imanin irin na Alhj salisu kuma suka yi alk'awarin fad'in gaskia a kotu amman duk da hka sai da abduljabbar ya gwara musu kawunan su saboda tsabar 6acin rai tuni suka suma saboda tsabar axaba maimakon a k'wara musu ruwan sanyi su farfad'o amman ina ruwan xafi abduljabbar yasa aka xuba musu sai da yaga sun farfad'o sannan ya fita daga d'akin duk sunyi bak'i sun rame tsabar axabar da suka sha

Kuma yana sani yak'i halartar kotun don ya fison su d'an sha wahala sannan ya bayyana don a ganin shi yanke hukunci lokaci d'aya basu sha d'an wahala ba baxai yi mishi kyan gani ba kuma ya fison sai Alhj salisu ya sawa ranshi samun nasara daga K'arshe ayi mishi kwaf d'aya

Tun ana gobe xa'a yi xaman kotu na K'arshe abduljabbar ya shigo kano dashi da amintattun yaran shi joseph da mubaraq tare da yaran Alhj salisu a d'akin da yake punishment di'n yaran shi a d'akin aka xube yaran Alhj salisu sannan ya nufi part d'in su ya bar Joseph da mubaraq suna gadin su duk da wajen a rufe yake

Yana shiga jiddah ta taso da d'an gudu ta rungume shi tana murnar ganin shi don ya dad'e bai xo ba don hka yana wanka aka shiga biyan bashin k'wanakin da ba'a tare, ranar yini yayi a gida yana huta wa tare da xuba soyayya da jiddah yinin farin ciki yayi ba wanda yasan yaxo Kano saboda ya fison su had'u a kotu gobe.....
Washe gari misalin wajen karfe 10 na safe kotu ta cika da mutane ga en jaridu suma kallo d'aya xaka yiwa su Alhj salisu kasan suna cikin tsantsar farin ciki wannan Karon har da hajia binta matar Alhj salisu da baban ta Alhj salisu har da ladi (wadda Alhj salisu ya kai ta gidan su nauwara don ta dunga yi musu aiki a xahiri)

Su nauwara kuwa duk jikin su a sanyaye Har da barrister di'n don basu da wata shaida mai k'arfi sai kame kame amman duk da hka basu karaya ba sun dogara ga Allah sai addu'a suke a cikin xuciyar su

Karfe 10 dai dai aka fara Shari'ar su nauwara nan aka shiga tafka tambayoyi tsakanin barrister di'n su nauwara da nasu Alhj salisu har xuwa lokacin da aka tattara wa alkali bayanai aka bashi duk anyi tsit ana jiran hukuncin da xai yanke

Har alkalin ya bud'e baki xai yi magana kenan aka bud'e kofar aka shigo gaba d'aya kallo ya koma kan kofar don ganin wanda ya shigo, nauwara ma da kanta yake kallon k'asa ta d'ago kanta tare da kallon kofar ganin yanda gaba d'aya mutanen cikin kotun hankalin su yayi kan kofar shigo wa.....

Aishat A muh'd
[4/12, 15:35] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 82~*

Gaban ta ne yayi mugun fad'uwa ganin bayyanar Abduljabbar sanye yake cikin kakin shi yayi kyau kwarjinin shi ya cika wa mutane kai tafiya yake cikin kasaita har ya k'araso cikin kotun gaba d'aya mutanen cikin kotun binshi suke da kallo suna mamakin mai ya kawo wannan babban sojan mai muk'amin MG kotu xama yayi tare da had'a ido da barrister di'n su nauwara ya kashe mishi ido d'aya Jijjiga kai barrister yayi tare da sakin wani murmishin mugunta (na ce toh shi wannan abduljabbar d'in sai kace wani aljani yana abuja har yasan barrister di'n da xai tsaya wa su nauwara)

A karo na biyu alkali ya gyara xaman glass d'in shi a ido ya bud'e baki xai yi magana kenan barrister kabeer Ya nemi alfarmar xai gabatar da hujjar shi ta K'arshe nan barrister di'n su Alhj salisu yak'i yarda da hakan amman ina har alkalin ya bashi wannan favour di'n xama yayi cike da takaice ya kallo abduljabbar ai kuwa ya kashe shi da killer samiling sai da yaji d'an tsoron abduljabbar kuma yana kula da kashe idon da yayi wa barrister kabeer
Chapter 54 · 0% Book details