Sashe 17
Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaban ta ne yayi wata iriyar fad'uwa sakamakon ganin motar aminu agida alamar ya dawo kenan da sallama ta shiga falon turus tayi ta tsaya saboda ganin yanda yake ta safah da marwa a falon kallo d'aya tayi mishi ta d'auke kanta saboda yanda taga fuskar shi cike da tashin hankali yana ganin ta ya matso kusa da ita ya fara magana cike da tarin damuwa a cikin ta yace
"hindatu ina su nauwara? Na dawo gidan ba kyanan kuma ban gan su ba me yake faruwa ne?? "
Ita ma a rud'e tace "tabbb ka tambaye ni a gidan na barsu naje jifatu siyo mana drinks da fruit da gaske basa nan to ina suka tafi ko sun gudu ne???
"Keeeeeee dakata nafa san halin ki daman ba son xaman su kike ba a gidan, ina kika kai su iyee ki fad'a min Kafin na d'au mummunan mataki akan ki wlh"
Tuni cikin hindatu ya duri ruwa saboda bata ta6a ganin aminu a haka ba cikin dakiya tace "na..... nace.. ni na barsu a gidan na fita bansan inda suka tafi ba "
Bai san lokacin da ya fidda hannu ya wanka mata mari ba da sauri ta dafe kumatun ta tare da fashe wa da kuka a fusace yace "karya kike hindatu ki fad'a min gasky wlh "
Gaba d'aya ta gama tsorata dashi ganin yanda ya koma don hka cikin rawar murya da rud'e wa tace "suna tasha can na kaisu don na gaji da xama dasu a gidan nan"
"What!!! "
Ya fad'a da karfi ai wani tsalle ta daka sai gata a d'aki da sauri tayi wa kofa key sannan ta xame k'asa ta xauna tana mai nadamar abin da ta aikata dama ta barsu bata kore su ba don sai yanxu wani mugun tsoro ya kamata (Hmmm daman hausawa sunce dana sani k'eyace)
Da gudu ya fisgi motar shi ya bar gidan hka yayi ta bulayin neman su nauwara a tashoshi amman duk an tashi ba mutane saboda dare yayi sosai gaba d'aya aminu duk rud'e da tashin hankali hka yayi ta neman su amman ko me kama da su nauwara bai gani ba parking yayi a gefen hanya tare da d'ora kanshi a jikin steering d'in motar baisan lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba saboda tsabar tausayin su nauwara
Hindatu ta cuce shi ta gama dashi sai da yaci kuka ya koshi tukunna dakyar ya iya driving d'in motar ya tafi gida lokacin 1 am na dare hankalin hindatu yayi matuk'ar tashi sosai tayi da nasani yafi dubu ganin har yanxu aminu bai dawo ba ajiyar xuciya ta saki jin shigowar shi gidan amman ya dad'e sosai bai shigo cikin gidan ba kamar xata fita ta duba shi amman tsoro ya hanata tana nan mak'ale a jikin window ya shigo sai da gaban ta ya fad'i saboda ganin yanda fuskar shi ta koma idanun shi sunyi matuk'ar ja
D'akin shi ya shige tare da fadawa kan gado sai da ya huta tukunna ya shiga toilet ya d'aura alwala sannan ya fito nafilfilo ya farayi tare da addu'ar Allah ya kare su nauwara a duk inda suke k'wana yayi bai iya yin bacci (Allah sarki aminu bawan Allah gaskiya ba k'aramin so yake yiwa nauwara na)
????☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*??
*~Pg 30~*
Acikin k'wanaki 2 hindatu tayi nadama sau ba adadi akan abin da ta aikata ta axabtu iya axabtuwa ba duka ba xagi ko bakar magana kuma ba hana ta abinci yayi ba kawai tsabar abin da ta shuka take girba baya kulata sam ko gaida shi tayi baya amsa wa iya yaran shi kawai yake kulawa,baya cin abincin ta magana bata had'a su gaba d'aya tayi wani iri tana son bashi hak'uri amman babu fuskar hakan...
Shi kuwa aminu kullum acikin binciken inda su nauwara yake amman har yanxu bai gansu ba don hka ya hak'ura addu'a kawai yake musu Allah ya k'are su har ya d'an fara sakkowa daga fushin da yake da hindatu
Hakan da ta gani yasa ta durkusa har k'asa tana kuka tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi baxa ta k'ara kwatanta shi ba dakyar ya iya hak'ura tare da yi mata nasiha sosae mai ratsa jiki Shikenan suka shirya tsakanin su kun san ance tsakanin mata da miji sai Allah,suka cigaba da rayuwar su amman har yanxu bai mance da su nauwara ba yana d'an binciken su idan ya samu Lokaci ga addu'ar da yake musu...
*******
Abduljabbar kuwa aacikin satin nan suka shige cos d'in da aka tura su wajen su 5,ya tsallake ya tafi ko Jiddah bai gaya wa saboda haushin ta da yake ji don ko wayar ta baya amsa wa saboda lokacin da ya canja mata mota irin wadda take so ta dunga murna tun tafiyar shi bata kirawo shi ba sai a lokacin amman yayi biris ya k'i d'aukan wayar K'arshe ma da ta dame shi kawai sai yayi switch off d'in wayar don baya son jin komai daga gare ta tunda had'a shi da mahaifiyar shi take...
Ita kuwa jiddah da taji wayar a kashe sai bata damu ba tasan Kafin yaxo weekend ya huci don batasan da tafiyar ba sai bayan tafiyar shi da k'wana 3 taji labari ai kuwa ranta ya 6aci tana matsayin matar shi taya ya xai tafiya ta tsawon wannan lokacin amma ace bai yi mata sallama ba wannan ai ba adalci bane (hmm ashe jiddah tasan da hka ita take mishi ashe dai ba dad'i)
Ta d'an damu Kad'an amman cikin k'wana 2 ta watsar da damuwar ta cigaba da sha'anin ta ga xuwa aikin ta yana d'ebe mata kewa...
Ta dad'a mik'e kafa komai sai dai ayi mata aikin ta kawai tayi wanka sai sallah da xaman cin abinci sai fita office da yawan bin gidajen k'awaye...
********
Su nauwara da saleem kuwa sai da suka ci kukan su suka koshi sannan lokacin gaf da mangariba mutane har sun fara watse wa nan hankalin nauwara yayi mugun tashi don batasan inda xasu je su k'wana ba tsoro Duk yabi ya kamata
Suna cikin hka har duhu yayi basu ankara ba suka ga duk tarin mutanen duk sun kama gaban su wata er rumfa suka shiga tak'ure wa suka yi waje d'aya duk xuciyar su cike da tsoro ga duhu dulum ko'ina addu'o'i kawai nauwara take a cikin xuciyar ta da hka bacci ya d'auki saleem a jikin ta ita kuwa duk iya satar bacci ranar kasawa tayi
Da hka har asuba tayi musu awajen sai da gari ya waye sosai sannan a hankali saleem ya bud'e idon shi tare da cewa "Aunty nauwara har yanxu uncle aminu bai xo ya mayar damu gida ba? "
Kura mishi ido tayi don ta rasa mai xata ce mishi kafin a hankali tace "saleem ai mun bar musu gidan su ka amince abinda matar shi tace damu? "
Shiru yayi da alamar tunanin yanda sukayi da hindatu yake yi tukunna yace "yanxu to ya anan xamu xauna ya xamu yi idan xamuyi bacci ko wani abun sannan ina xamu samu kud'in da xamu dunga cin abinci kullum???"
Wad'annan tambayoyin na saleem ba k'aramin k'ara rud'ar da nauwara suka yi ta rasa amsar da xata bashi kawai sai tace "ina kud'in da aminu ya bamu Kafin yayi tafiya "
Hannu ya xura a cikin aljihun kayan su ya xaro yace "gasu aunty nauwara "
"nawa ne? "
"dubu 3 ne dai dai "
Saleem ya bata amsa ajiyar xuciya ta saki cikin jin dad'i Sannan tace "ka dauki duba d'aya ka siyo mana pure water muyi sallah Idan mun idar sai mu nemi wani abun mu ci"
"toh aunty "
Saleem yayi yanda nauwara tace mishi bayan sun idar da sallah anan saleem ya siyo musu wainar gero sukaci suka koshi suka d'ora da pure water ......
???☘☘????
*K'ARSHEN WAHALA*
????☘☘??
*Written by*
*Aishat A muh'd {Aunty}*??
*~Pg 31~*
Suna nan xaune har rana tayi zafi basa uhm basa uhm uhm sai dai idan saleem ya gaji yayi bacci ya tashi ba me kula su kowa harkar gaban shi yake
Wata mai siyar da abinci a tashar er dattijuwa bahaushiya ce tun da safe tagan su awurin sai dai su siye abinci suci kuma suyi sallah a wurin toh ko bara suke sai yamma suke tafiya abin da xuciyar er dattijuwar nan ta sanar da ita sai taji tausayin su sosai
6 na yamma wannan er dattijuwar nan ta tashi daga sai da abinci ta tattara kayan ta waje d'aya aka lode mata su a taxi sannan ta K'arasa wajen su nauwara tayi musu sallama nauwara ce ta amsa Kafin er dattijuwar nan ta cigaba da cewa
"ni suna na saude mai abinci don sana'a ta itace siyar da abinci awannan tashar, shine tun safe da naxo na ganku anan ku kad'ai gaku yara ina iyayen ku, koh bara kuke yi ne??? "
Wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun nauwara Bara!!! Nauwara ta mai maita hakan a xuciyar ta cikin wani irin yanayi tace "ba bara muke yi ba kawai bamu da wajen xama ne da ya shige nan"
Cikin mamaki take kallon ta kafin tace "ina iyayen ku,ina dangin ku? "
"iyayen mu sun rasu dangin mu kuma bamu san su ba"
Nan tausayin su ya k'ara kama ta don da ganin nauwara bata gani gashi kuma gurguwa ce "xaku iya bina gida na mu xauna tare ni kad'ai ce bani da yara ko d'aya sai dai mijina ya rasu tun jima wa ina xaune anan gaba Kad'an damu "
Shiru nauwara tayi alamun tunani take ganin hka saude ta cigaba da cewa "tsakani da Allah xan rik'e ku yarinya kada kiji tsoro na baxan cutar da kuba gidan da nake gidan haya ne mu 2 ne a gidan "
Nauwara Bata da yanda xasu yi kawai suka bita tun da basu da wajen xuwa d'aukan nauwara tayi cak ta shigar da ita mota da yake saude irin karfaffan nan ce saleem ma ya shiga tukunna mai taxi yaja su