← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 73

Sashe 34

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wayar tace ta fara ringin cikin sauri ta d'auka ganin sunan Yah abduljabbar yake kira taji gabanta ya fad'i wata kunya ta kamata dakyar ta iya d'auka ta k'ara a kunnen ta shiru tayi batai magana ba shima a nashi b'angaren shirun yayi yana jin saukar numfashin dakyar ya iya bud'e baki yace
"shine kika gudu baki ban amsa ba?"
Cikin sanyin murya mai had'e da kunya tace "me xance Tohhh? "
D'an murmishi yayi Kafin yace "cewa xakiyi I luv you abduljabbar oya ina jiran ki fad'i ko sai naxo a fad'i a gaban Naji? "
Da sauri tace "a'a ni...ni wlh kunya nake ji"
Ta K'arasa fad'i cikin shagwa6a, hkan ba k'aramin k'ara birge shi tayi ba don yana masifar son mace er shagwa6a cikin muryar Idan xai musu fad'a yace "keee malama Idan xaki fad'a Ki fad'a don Wlh baxan kashe wayar nan ba sai kin fad'a min"
Wayyo Allah to ita ya xatayi wlh kunya take ji sai faman tutturo baki take tana yarfe hannu kamar a gaban shi take dakyar ta iya cewa cikin sanyin murya tare da rarraba kalamar kamar mai koyan magana "ina son ka Yah abduljabbar"
Tana gama fad'in hka ta yi hangin up d'in wayar tare da d'aukar pillow ta rufe fuskar ta dariya sosai ta bashi wannan kunyar ta ta ba k'aramin birge shi take ba kallo abdulkareem yayi wanda yake kunshe dariyar shi don shine ya matsa mishi sai ya kirawo ta awaya harara ya dalla mishi sannan yace "ai nasan ni ba irin maxan da xa'a kyale bane don hka dai nayi nasara "
"a hba abokina da gaske? "
"an fad'a ni na wasa ne " dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa sannan abdulkareem yace "sauran kayi ta nuna mata xafin kan nan naka ko wannan miskilancin naka wlh ka sake ka nuna mata so don ku more soyayyar ku kafin mu sha biki"
"tunda ni nake so ai angama komai don wlh sai umma ta gaji da rashin kunya ta ta aura min ita xan barsu su huta Don naji tana cewa sai sun gama skul wajen 2 years wlh bazan iya hak'ura ba "
Sakin baki abdulkareem yayi yana kallon shi duk ya canja ssai faman surutu yake kamar bashi ba cikin tsokana yace "Duk soyayyar nauwara ce ta canja hka sai xuba ka ke "?
Duka ya kawo mishi a kafad'a da sauri yayi tsalle ya kauce dukan bai same shi ba "kai captain matsala ta dakai saurin kawo hannu kace xaka daki mutum "
Dariya suka tuntsire da ita sannan suka cigaba da hirar su cikin jin dad'i da annushuwa

*Aishat A muh'd*😘

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd*😘

_jinjinar ban girma gare ki k'awata zaynab lawan ( *sarautah*) maman anwar da ikraam Allah ya raya mana su, Allah ya bar mu tare Ameen, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike wannan page d'in naki ne_❤😘

*~Pg 58~*

Duka fa'iza ta kai mata a baya firgigit ta mik'e a tsorace tana Sosa wajen harara ta watsa mata cikin xafin dukan tace "Haba fa'iza da xafi fah wlh Idan kika sake dukana xan fad'a wa Yah abduljabbar"
Sakin baki tayi tana kallon ta yayin da nauwara ta kashe mata ido d'aya cikin xakuwa fa'iza tace "ke kinsani a duhu bani labari sis? "
Nan nauwara ta bawa fa'iza labarin abin da ya faru tsakanin ta da Yah abduljabbar wani ihun murna fa'iza ta saki da sauri nauwara ta toshe mata baki tana cewa "Don Allah fa'iza ki nutsu wannan k'arar sai umma taji "
Dariya tayi tana rungume nauwara cikin tsananin murna tace "Allah nagode maka abin da nake jira kenan don Allah ki cire tsoron da kike yi mishi ki saki jiki kusha soyayya "
Lumshe ido tayi tare da bud'e su lokaci d'aya tana murmishi tace "ke ni kunyar shi nake wlh sannan Nifah ina d'an tsoron wannnan matar tashi? "
Harara fa'iza ta dalla mata tare da kai mata duka da sauri ta kauce tana cewa "ni matsala ta dake saurin duka daga magana"
"ai Kece kika ban haushi wlh ina ruwan ki da matar shi akan ta xaki xauna, kawai yarinya ki share ta"

Nan dai fa'iza ta dunga shawarwari masu kyau yanda xata samu kan Yah abduljabbar tare da fad'a mata irin abubuwan da yafi so basu tashi daga nan ba har sai da umma ta nemo su tukunna suka tashi

Tun daga lokacin sai suka fara wasan 6oya tana jin Shigowar shi xata gudu d'aki shi kuma kawai ya kyale tane ya xuba mata ido don yaga iya gudun ruwan ta har ranar da xai koma abuja basu had'u ba hka ya tattara ya tafi shi kanshi wani lokacin yana mamakin yanda son yarinyar nan yayi mishi kamun da har ya kasa 6oye shi ,toh ita nauwara taso sake sashi a idon ta Kafin ya tafi kunya ce ta hanata ya tafi ya barta da kewar shi don ma akwai album pictures d'in shi da fa'iza ta damk'a mata shi ko yaushe cikin kallon shi take yayin da son shi yake k'aruwa acikin xuciyar ta

Tun da xafin nan ya kama nauwara Idan ta tashi shan ruwa Bata sha mai rangwamen sanyi sai dai mai sanyi k'arara ko ta fasa k'ank'ara ta dunga sha gashi d'aki sai ta kure fanka da ac bata jurar yanayin xafi umma tayi fad'an ta daina sha sai ta koma sha a 6oye ai kuwa mura tayi mata mummunan kamu atishawa hanci ya dunga yoyo gashi murya ta dashe nan fah ido ya raina fata mura tak'i sauk'i gashi bata son shan magani

Kamar yau tana xaune a parlour tana sanye da black d'in siket da red d'in t shirt tayi tumfke kanta da ribbom red barimar kunnen ta red colour ce tayi kyau sosai tissue ne a gaban ta tari guda sai fyace hanci da atishawa take hancin nan yayi jawur dashi umma da aunty sadiya sun fita yinin bikin k'awar umma daga ita sai fa'iza da take bacci saleem kuma yana waje yana buga ball
Chapter 34 · 0% Book details