← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 73

Sashe 48

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty asma'u lokacin da taji labarin tayi kuka sosai ita ma a take ta k'arya ta hkan tuggu ne aka shirya don kawai a raba su ta kirawo abduljabbar a waya tana fara yi mishi xancen ya katse wayar ranta in yayi dubu ya 6aci akan abin da abduljabbar yayi nan ta shirya ta taho kano ba k'aramin firgita tayi ba lokacin da ta ga yanda nauwara ta koma sai katon ciki a gaba ta rungume nauwara suka dunga kuka sai da umma taxo tana mata fad'an ita da xata rarrashe ta xata xo ta sanya ta a gaba tana kuka haka tayi k'wanaki biyu ta tafi cike da tausayin nauwara a xuciyar ta daman ita tunda ta ganta jinin su ya had'u tana son nauwara, kausar ma bata ji dad'in abin da yayan ta ya aikata ba sai taja bakin ta tayi shiru fad'an da yafi k'arfin ka sai kaja bakin ka kayi shiru, fa'iza kuwa tayi bala'in tayi masifar duk a banxa tunda bata isa tayi a gaban shi ba sai dai ta rushe da kuka duk gidan ba wanda ya goyi da bayan abduljabbar, saleem ne bai nuna komai ba kawai da fa'iza ta gaya mishi sai cewa yayi "Allah ya kyauta" ya tashi xai fita daga d'akin duk da bai jin dad'in hkan ba a fusace fa'iza tace "toh sarkin hak'uri abin da xaka ce kawai "
D'an murmishin yak'e yayi yace "toh me xance aunty fa'iza hak'uri xata yi kawai rayuwar nawa take indai har bata aikata hkan ba na tabbatar wataran sai Allah ya tona asirin wanda ya kulla mata sharrin "
Yana gama fad'in hka ya fice daga d'akin yana goge hawaye afuskar shi sai jikin FA'iza yayi sanyi ita kuwa nauwara ko d'ago kanta Bata yi ba

Cikin nauwara ya shiga watan haihuwar shi xama dakyar tashi dakyar don ba k'aramin girma cikin yayi ba su umma ba k'aramin tausaya mata suke ba duk ta kumbura musamman ma kafafuwan ta kula wa sosai suke bata basa barin ta tana xama ita d'aya saboda idan ta ke6e ita d'aya tunani take ko kuma ta dunga kuka na tausayin kanta da abin da yake cikin ta umma ta sha kamata tana kuka nan xata xauna ta rarrashe ta tare da yi mata nasiha har sai taga hankalin ta ya kwanta tana dariya sannan umma xata ji dad'i, tun suna sa ran haihuwar kusa har ta shige lokacin nata su dai addu'a suke mata Allah ya sauke ta lafia

A firgice ta farka daga baccin da take sakamakon wani irin axabbaben ciwon mara da ya tashe ta ba shiri ta sauka daga kan gadon tuni har ta fara had'a uban gumi baya ma ya rik'e addu'a take duk wadda taxo bakin ta sai safa da marwa take a d'akin idan ciwon ya lafa sai ta xauna yana dawowa xatayi xumbur ta mik'e tsaye motsin ta shi ya tashi fa'iza daga bacci a rud'e ta K'arasa wajen ta tana cewa
"nauwara lafia? "
Ina ba bakin magana sai jikinta da yake rawa idanun nan sunyi jawur dasu da gudu fa'iza ta nufi d'akin umma ta fad'a kanta tana kuka a firgice umma ta tashi tana cewa
"ke fa'iza lafia me yafaru "
Cikin rawar murya tace "um umma nauwara ce ba ta da lafia sai wani irin abu..... "
bata K'arasa fad'in hka ba umma ta tashi da sauri ta dauki hijab ta saka sannan ta d'auko wayar ta tana neman abba har suka k'araso d'akin kallo d'aya umma tayi mata ta fuskan nakuda take da sauri ta kirawo abba a waya sannan ta K'arasa wajen nauwara da take a durkushe Tana faman xabga salati da addu'a tace
"Sannu nauwara Allah ya raba lafia sannu"
"fa'iza duba cikin bedroom d'ina ki d'auko wannan akwatin ki kai cikin mota da sauri fa'iza ta fita umma ta rik'o nauwara suka fito suna sauka k'asa abba da aunty sadiya suna k'araso wa mota suka nufa gaba d'ayan su suka shiga asibitin da umma take kai ta awo nan suka nufa da yake da file d'in ta kuma shine asibitin da gaba d'aya suke xuwa cikin en mintuna suka K'arasa aka shigar da ita labour room su umma suna tsaye a kofar d'akin kamar su shiga ciki fa'iza kuka kawai take umma tace
"fa'iza ba kuka xaki mata ba addu'a tafi buk'ata Allah ya raba su lafia "
Tun dare ake abu d'aya amman har safia nauwara bata haihu ba ba k'aramin jigata tayi ba duk ta fita hayyacin ta numfashi dakyar ta ke iya ja nurses biyu ne a kanta da doctor Aishat wadda ita ce on duty suna cikin tattaunawar gwara ayi mata CS ta huta a lokacin tayi wani nishi da k'arfi sai ga kan yaro ya fito da sauri doctor Aishat ta canja hand glove di'n hannun ta ta taimaka mata har yaron ya K'arasa fito wa

Mik'a wa nurse tayi yaron don su gyara shi cikin nauwara taga yana motsi ta6awa tayi sai taga da sauran wani d'an aciki don hka ta shiga taimaka wa nauwara don d'an ya k'arasa fito wa xuwa lokacin ta gama gala6aita jikin ta ba k'wari wani yunkuri tayi tare da nishi fit d'an ya fito yana gama fita ta xube ba numfashi cikin kad'uwa doctor ta mik'a wa nurse yaron ta dawo kan nauwara tana duba ta amman babu alamar numfashi

Cikin sauri ta fice daga d'akin don kiran wani doctor d'in ya taimaka mata, yayin da sauran nurses d'in har sun gama gyara babies duk maxa kyawawa dasu masu kamar uban su kamar yayi kaki ya tofar duk kamar su d'aya fito wa suka yi suka mik'a wa su umma su cikin murna da d'oki suka kar6e su fa'iza Mai kuka sai gashi ana dariya da tsallen murna umma ta Kalli nurse din cikin murmishi tace
"ina kuma nauwara dafatan tana nan lafia"
Lokaci d'aya nurses d'in nan fuskar su ta canja cikin tsoro umma tace
"Kuyi min bayanin halin da take ciki pls"
Dakyar d'aya ta bude baki tace
"I'm sorry madam Kuyi mata addu'a tana cikin wani hali saboda ko numfashin ta ya d'auke yanxu doctor Aishat ta tafi kirawo wani doctor don su had'u su yi......... "
Kasa K'arasa fad'i tayi ganin yanda suka xuba mata ido hankalin su yayi mugun tashi Kafin ta sake magana doctor Aishat da wani likitan sun shige d'akin da nauwara take sauran nurse din suka bisu da sauri suka rufe kofar

Tuni fa'iza mai dariyar ganin en babe's ta d'ora hannu akai xata xunduma ihu cikin sauri aunty sadiya ta toshe mata bakin ta

Aishat A muh'd
🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd

*~Pg 75~*

"Haba fa'iza ba ihu xaki yi ba addu'a tafi buk'ata fiye da komai Allah ya tashi kafad'un ta "
Aunty sadiya ta fad'i tana goge hawayen fuskar ta yayin da fa'iza ta rungume ta tana kuka mai ban tausayi, umma kuwa sai dai a shiru kawai abba ne ya kamata ya xaunar da ita kan kujera ganin ta k'ame a tsaye saboda tsabar tashin hankali da farga ba da take ciki gaba d'ayan su sunyi jugum jugum addu'a kawai suke a cikin xuciyar su

Bud'e kofar da akayi yasa su tashi da sauri doctor Aishat da doctor kabeer suka fito duk sai goge xufa suke da sauri abba ya K'arasa wajen su yace
"ta farfad'o doctor??? "
Cikin murmishi doctor tace
"Alhmdullilah yalla6ai mun samu nasarar hkan ta farfad'o numfashin ta normal sai dai munyi mata allurar bacci don ta huta saboda tasha wahala"
Ajiyar xuciya suka saki gaba d'aya tare da furta "Alhmdullilah " fuskar su tuni ta bayyana farin ciki nan Abba ya bi doctor don su rubuta mishi magungunan da xasu yi amfani dasu ita da yaran

Sai lokacin suka kar6i yaran suna kallon su tare da yi musu addu'a umma ta xuba musu ido har hawaye ya fito daga idonta xuciyar ta cike da k'aunar yaran kamar su d'aya da abduljabbar, a lokacin aka turo nauwara Xuwa rest room suka bisu da sauri har d'akin tana ta baccin ta hankali kwance sai dai ta rame sosai tayi wani irin fari sosai ta d'ashe aunty sadiya tace
"umma Bari na koma gida na dafa mata abincin da xata ci Idan ta tashi "
"okay auntyn yara sai kin dawo" ta juya ta tafi yayin da fa'iza ta jera yaran a gabanta tana kallon su xuciyar ta cike da k'aunar su dama natane kai gaskia dole nayi aure don na haifi yaran nan wayyo Allah baxan iya ba tabb wannan wahalar da nauwara tasha ta haife su ina xan iya nama fasa auren hka tayi ta xancen ta a xuciya ita kad'ai

A hankali ta fara bud'e idon ta har ta bud'e su gaba d'aya a nutse tace
"umma nahhh"
Da sauri umma ta kallo ta tare da k'arasa wa kusa da gadon cikin farinciki ta rik'e hannun ta tana cewa
"nauwara kin tashi Alhmdllh ya kike jin jikin naki"
"da sauk'i umma sai dai yunwa nake ji"
Ta fadi tana d'an Yatsina fuska
"me xaki ci??? "
"tea xan sha"
Da sauri ta K'arasa inda aunty sadiya ta kawo abincin ta fara had'a mata tea mai kauri sannan ta xuba mata ferfeson kaji sannan ta taimaka mata ta tashi xaune tayi brush tukunna ta dunga bata a baki har ta koshi tuni ta fara had'a gumi bayan umma ta gama bata ta d'an huta sannan ta kaita toilet ta taimaka ta tayi wanka da ruwa mai d'umi yanda xata ji dad'in jikin ta
Chapter 48 · 0% Book details