← Book details Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 73

Sashe 32

Karshen Wahala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba k'aramin tsorata jiddah tayi ba ganin abduljabbar ne ya rik'e mata hannu fuskar nan tashi a murtike ba alamar fara'a cillar da hannun nata yayi sannan cikin kakkausar murya yace "daga yau kada ki sake gigin d'aga hannu Kice xaki marin ta "
Yana gama fad'in hka yayi shige war shi yayin da jiddah ta rasa mai xata yi saboda tsabar takaici harara ta dalla wa nauwara da fa'iza da suke tsaye kusa da ita abin ya basu dariya don hka suka kyalkyale da dariya tare da tafawa haba ran jiddah idan yayi dubu ya 6aci gashi abdul ya mata warning di'n kada ta ta6a ta don hka a fusace ta koma d'akin umma
Suma su nauwara d'akin su suka tafi bayan sun xauna nauwara take kora mata bayanin yanda Yah abduljabbar ya tarfa ta tana xance hba mai fa'iza xata yi idan banda dariya sai da taci dariyar ta ta koshi har nauwara na tana taya ta kafin daga bisani ta nutsu Sannan ta magana "Nifah a yanda na lura Yah abduljabbar son ki yake "
Gaban nauwara sai da ya fad'i da taji abin da fa'iza tace cikin tsoro tace "na rok'e ki kada ki sake wannnan wasan pls, don Kinsan Yah abduljabbar ba ajina ne ba"
"keee dalla malama waya gaya miki baa ajin ki bane ai wlh Idan ya samu mata kamar ki ya more wlh ina nan ina addu'a Insha Allah sai hasashena ya xama gaskia "
"Hmmm kawai nauwara tace don bata da abin cewa kwanciya tayi tare da lumshe idon ta tana tunano abin da ya faru d'axu

Bayan ya shiga d'akin umma sun gaisa take bashi baki da yayi hak'uri akan laifin da jiddah tayi mishi tayi nadama sannan tasa jiddah ta bashi hak'uri har d'an kukan ta akan baxata k'ara ba, shi dai ya nuna ya hak'ura ba komai nan ta dunga murna kallon ta yayi a xuciyar shi yace yarinya baki da wayo kiyi min Wannan babban laifin ai da kishiya xan saka miki shine dai dai da abin da kika yi min yana gama wannan tunanin ya saki wani murmishin mugunta ita kuma ganin harda murmishi yasa ta dad'a tabbatar wa ya hak'ura sannan sukayi sallama da umma suna fitowa parlour yace "kije gida inanan xuwa yanxu "
Cikin marairaicewa tace "hba sojana baka hak'ura ba? "
D'an murmishi yayi Kafin yace "no ba hka bane kawai ina son ganin Abba ne"
"toh na jira ka mana? "
"kawai ki tafi nace "
To ganin lalla6a shi take yasa ta shige ta tafi shi kuma d'akin su fa'iza ya nufa cikin takun shi na kasaita kafa yasa ya tura kofar gaba d'ayan su a tsorace suka jiyo sake firgice wa suka yi ganin shi da sauri suka mik'e tsaye yayin da nauwara ta fara ja da baya cikin tsananin tsoro gabanta sai fad'uwa yake kallon fa'iza kawai yayi ta fahimci abin da yake nufi alamar ta fita daga d'akin ai kuwa a 360 ta fice abinta xuciyar ta cike da tausayin nauwara

Sai da ta tokare da bango tukunna ta dakata da ja da bayan da take k'araso wa yayi har inda take ganin ya d'aga hannu sama yasa ta da sauri ta runtse idon ta cikin tsoro gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin marin ta xai yi hawaye ne suka fara xuba a fuskar ta ido ya xuba mata hannun da ya d'aga tana tunanin marin ta xae yi ashe gashin kanta da ya barbaxu a fuskar ta ya hau janye wa yana mayar dashi baya a hankali ta bud'e idon ta suka had'a ido da sauri ta kawar da idanun ta don baxata jure kallon shi ba cikin wata irin voice kamar ba tashi ba yace "bana hana ki kula samari ba? "
"Don Allah Yah abduljabbar kayi hak'uri wlh banyi niyyar fita umma tace naje bakyau wulak'anta mutum amma baxan k'ara ba " Cewar nauwara cikin tsoro d'an murmishi yayi wanda yayi matuk'ar k'ara mishi kyau yace "good girl sauran na k'ara gani "
Sai faman kallon ta yake ita dai nauwara gaba d'aya a tsure take gashi yabi ya lallu6e ta da girman jikin shi da tsayin shi ba lalle a hange ta ba gashi duk k'amshin turaren shi ya gama cika mata hanci bakin shi yakai dai dai kunnen ta ya rad'a mata Cewar "nauwarahhh! an ta6a gaya miki Kina da kyau? "
Tambayar da ta kusan sumar da ita kafafun ta suka fara rawa K'arshe ma sai suke kok'arin yarda ita saboda ba k'wari hannun shi yasa ya rik'o kafad'un ta yace "relax! nauwarah answer me?"
Gaba d'aya ta gama rud'e wa shin mafarki take ko ido biyu Yah abduljabbar d'in da tasani shine yake mata magana hka tsawar da taji ya daka mata shi ya sake firgita ta sauran Kad'an fitsarin da take kok'arin rik'e shi ya kusa kubcewa kallon shi tayi ya dad'a hade fuska kamar bashi ba "Kina ji ina ina tambayar ki "
Sunkuyar da kanta tayi sannan a hankali ta bud'e baki tace "ehh aunty safah da en skul d'in mu suna fad'a min haka "
"Har da maxa koh? "
A tsorace ta d'aga kai alamar ehh nan wani kishi ya k'ara kama shi cikin d'aga murya yace "ki bud'e baki kiyi min magana kuma bana son k'arya "
Cikin rawar murya tace "ehh har dasu "
Idanun shi ne suka rufe da wani irin kishi baisan lokacin da ya murd'e hannun ta ba saboda axaba batasan lokacin da ta k'walla k'ara ba cikin jin xafi

K'arar da tayi shi ya shigo da umma d'akin a rud'e turus tayi ganin abduljabbar cikin mamaki tace "lafia abdul, Mai tayi maka? "
"umma kamata nayi tana xance a waje"
"tohh shine xaka dunga yi mata mugunta irin taku ta sojoji ai ni nace ta fita"
"toh umma kawai ba'a binciki halin mutum ba nagari ne ko d'an iska ne kawai sai a tura yara"
"ehhh to wannan da gaskiyar ka xa'a gyara amman bana son wannan muguntar "
Ta fad'a tana kamo nauwara wadda take kukan axaba duk 'yan yatsun hannun ta sunyi ja d'ago kai tayi ta kalle shi suna had'a ido ya sakar mata harara da sauri ta sunkuyar da kanta ya fice daga d'akin nan umma ta rarrashe ta tayi shiru Sannan ta fita a d'akin

Toilet ta shiga tayi wanka tana fito wa ta Kalli fa'iza da ke xaune tana ganin ta ta kwashe da dariya sannan tace "hmm taku salon soyayyar kenan "
Hararar ta nauwara tayi taja tsaki xata saki magana wayar ta tayi ringin don hka ta kyale nauwara ta d'auki wayar ta nan da nan aka fara mak'ale murya alamar da saurayi ake wayar K'arshe ma sai ta fice daga d'akin tana yiwa nauwara alama da hannu tana xuwa

Kwanciya tayi tare da rungume pillow tana tunanin maganganun abduljabbar dafa kirjin ta tayi kada dai ace xancen fa'iza ya tabbata ai kuwa da taji dad'i samun miji kamar Captain abduljabbar ai da ta more ba Kad'an ba Shigowar message taji a wayar ta dauka tayi ta bud'e password d'in wayar gaban ta ne ya fad'i ganin number d'in abduljabbar ce Dama tana da ita a wayar fa'iza ce ta samata tun lokacin da Abba ya siya musu ga abin da tagani ya rubuta

_daga yau duk inda xaki Kina sanya nik'ab_

Tabbb baxan iya ba wlh Hka kawai xafi ma kad'ai ya ishe ni sannan bani ma dashi don hka sai ta rubuta mishi reply kamar hka

_Yah abduljabbar ni bani da nik'ab fa'iza ma hka_
Tana gama rubuta wa tayi sending ya tafi sannan tayi addu'ar bacci ta kwanta ganin har yanxu fa'iza bata dawo d'akin ba xuciyar ta cike da tunanin abduljabbar sam ta rasa sanin me yasa take yawan tunanin shi kodayaushe

*Aishat A muh'd*

🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
*Aishat A muh'd*😘

_Zama da masoyi mai son ka tsakani da Allah akwai dad'i, haka xama da mak'iyi bashi dad'i ko Kad'an toh da xarar mutum ya furta maka so duk halin shi yafi mak'iyan ka sau dubu_

_*Cewar nauwara*_

*~Pg 56~*

*WASHE GARI*

Nauwara sai wajen 9:30 ta tashi saboda lectures d'in karfe 11 take dasu don hka baccin ta tayi,bayan ta tashi wanka ta yi had'e da brush dama tun asubah tayi sallahr ta shirya wa tayi cikin wata simple gown kalar milk da touch d'in blue ajikin rigar don hka veil d'in da tayi rolling sai ya kasance blue tayi kyau sannan ta sauko k'asa ta tarar da umma, aunty sadiya da fa'iza nan ta tsugunna har k'asa ta gaida umma da aunty sadiya ta Kalli fa'iza da tun fitowar ta take mata dariya k'asa k'asa harara ta dalla mata kafin cikin shagwa6a tace "umma kinga fa'iza tana yi min dariya kohhh"
Da sauri fa'iza ta danne dariyar ta ta kallon ta umma tayi sannan tace "rabu da ita nauwara ai naganta tun d'axu hka kawai mutum ya dunga dariya kamar wani sabon kamu "(ta nufin mahaukaci), gwalo nauwara tayi mata tare da wuce wa dinning table don yin breakfast itama fa'iza ta dawo wajen ta suna er hira tana kur6ar tea tace "fa'iza kinji wai Yah abduljabbar yace na dunga sa nik'ab Idan xan fita "
Xaro ido fa'iza tayi tana cewa "tabbb wlh kada ki yarda shi duk kishin ne hka? "
"ke wai waya ce miki sona yak'e??? "
"fad'a wa wanda bai sani ba, yarinya ai ni suna nake ya aure ki wlh jiddah ta raina kanta"
"Allah k'awata !"
"ah tsaya wasa yarinya"
Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa har su umma da aunty sadiya suna kallon su
Chapter 32 · 0% Book details