← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 84

Sashe 8

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dije ta dafe kirji Bakinta a bud'e ta ce,. "WALLAHI ALLAH ya sakawa su INNA don kinci da zalinsu Kuma akan mummunar fahimtar da kika yi masu idan Baki rokesu suka yafe maki ba da wuya in hakkinsu zai barki ki shiga aljanna"

Duduwa ta ce,. "Ki je ki sanar dasu idan suna da abun Kare kansu su Kare kansu in gani in har su d'in ba Yan iskan bane kamar yanda kike tunani, to ma wai ke tayaya aka sameki in ba ta hanyar abunda kike kira iskanci ba?, To bari kiji hanyar da aka sameki itace Bala yake so yabi shima ya yi auren ya samo nashi rabon 'ya'yan, shima in banda rashin hankali irin nashi me zai yi dake masifaffiya bak'ar mafadaciya dake, shiyasa ma in bandashi kaf garin nan babu wanda na tab'a jin yace yana sonki to me za'a tsinta jikinki in banda jidali"

Dije ta zumburo Baki tace,. "WALLAHI kinci sa'a Ina ganin kimarki a idona da tuni na shikka maki rashin mutunci akan wannan k'azafin da kika yi man Ni da su Baffah, to Ni ALLAH na tuba ma wani tsautsayi zai sa har in yarda wani yace yana sona? Ai duk Wanda kika ga yana soyayya WALLAHI mugun ma dan iska ne na fad'a na k'ara fad'a Duduwa Bala Dan iska ne tunda har baiji kunyar kallon tsabar idanuwana ba ya bud'a Bakinshi yace wai yana sona ba"

Ta kalli Balan ta murgud'a Baki ta buga masa wata jar harara tace,. " kuma Bari kaji narantse da ALLAH duk kasa nayi ciki da kai zan kuka tunda kai baka da imani"

Tana k'are maganar ta fashe da kuka saboda tuno labarin da Inna ta Bata akan cewa duk ta yarda wani ya tab'a hannunta ko kuma yace yana sonta ta amince ciki zai fito jikinta yayi katoto ta haifo macizai.

Tana k'are maganar ta fita rangai rangai ta bare Baki iya k'arfinta tana ta kuka tana fad'in wayyo ita yau ta shiga uku tsautsayi ya hau kanta, kowa ya ganta tana kukan sai dai ya bita da kallo yana tunanin yau me yasa Dije kuka haka, saboda kowa yasan takadirancinta don abunda duk zai sakata irin wannan kukan ba abune kad'an ba, wasu ko dad'i kawai suke ji don tunaninsu ko wani ta samu wanda yafi k'arfinta ya darza mata shegen kashi.

Dije kam ko gabanta bata gani saboda tashin hankalin da ta fad'a, don ita a ganinta tata ta k'are shikenan tunda bala yace yana sonta cikinta zai yi katoto ta haifo macizai.

Aiko tun daga nesa Inna ta fara jiyo sautin kukanta cike da mamakin abunda ya saka Dije kuka yasa ta yi kasake tana jiran shigowarta, sai ko gata buguzum buguzum ta fad'o Gidan sai da ta yi tsalle ta fad'i k'asa tana ta kururuwar wayyo ita cikinta macizai sun fara taruwa, Inna ta bita da kallo cike da mamaki tace da ita,

"Wai ke lafiyarki kike cikawa mutane kunnuwa da kuka haka?"

Dije ta tsagaita da kukanta tace,. "Ba Balan Duduwa bane yace wai yana sona ba, Kinga fa har macizan sun fara taruwa cikin cikina suna cizar mani hanjina"

Inna ta so ta yi dariya amman ta mazge tace,. "Ni dad'ina dake hauka to bari kiji idan dai kika yarda ya tab'a hannunki ne macizan zasu fara taruwa ko kin manta labarin da na baki?"

Dije ta yi girgiza Kai, Inna tace "ya tab'a maki hannun ne?" Tayi saurin girgiza Kai tace,

"A'a"

Inna tace, "to kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki ai tunda ke baki ce kina sonshi ba har hakan ya janyo ki bashi fuskar da zai tab'a maki hannu, amman da ace kin bari ya tab'a maki hannun kam to da yau macizan zasu fara taruwa a cikin naki, amman yanzu tunda har kin tabbata bai tab'aki ba to Alhmdllh tashi kije ki ajiye allonki ki zo kiji wani labarin"

Dije ta share hawayenta hankalinta ya dan kwanta ta je ta ajiye allon ta dawo Inna ta shimfida masu tabarma ta ci gaba da bata labarai masu sakata tsantseni da halayen maza marasa mutunci masu lalata yara, Aiko daram darasin Inna ya shige kwanyarta don daman cen ita rayuwar maza ba damunta ta yi ba, don in banda Bala ma kaf garin ba Wanda ya tab'a taronta da wannan mummunar maganar.

Suna cikin firar ne aka fara buga masu sallama a k'ofar Gida, Inna ta kalli Dije tace

"Je ki gani wa yake sallama idan Baffanku ake nema ki sanar bai dawo ba"

Dije ta tashi tana yar wakarta ta nufi k'ofar Gidan, aiko sai gashi taga wani yaron Maigari ta kalleshi da kyau ta yatsina fuska tace,. ,"Baya gida kaje ka sanar"

Yaron ya kalleta kamar ya shaketa yace, "ai tunda ke kina nan muje Maigari yana nemanki daman dake da Baffan aka ce ku zo to tunda shi baya nan ke ki zo ki wakilceshi"

Dije ta murgud'a masa Baki tace, ,"wani munafukin ne ya Kai karata kuma? Ni me ma nayi da za'a nemeni?"

Yaron ya juya ya fara tafiya yace, "Wannan kuma sai ki baiwa kanki amsa Ni Kinga tafiyata sai kin k'araso"

Dije ta bi bayanshi da harara aiko sai ga Kira Inna ta kwala mata, ta amsa da k'arfi ta koma cikin gidan tace

"Inna Maigari ne ya aiko yace inje in karb'o dussata da ciyawar da yayi alk'awali zai dinga baiwa Akuyata"

Inna ta yi mata wani kallo tace, "wace dusa bayan waccen wadda ya aiko maki?"

Dije ta Sosa kai tace,

"To ko dai ciyawarce yake nufi Dan sak'on ne bai ji sak'on dai dai ba? Bari inje in karb'o in dawo INNA kar yaga na dad'e"

Ta fice da sauri Inna ta bita da kallo tace, "ALLAH ya shirya"

Dije kam tana fita ta nufi gidansu Hansai da sauran kawayenta sannan suka rankaya Gidan Maigarin, don zuciyarta ta tabbatar mata cewa Tambari ne ya kaita k'ara wajen Maigarin.

Aikuwa sai ko gashi tana zuwa ta ga Tambari da Mahaifinshi, sai dai kuma bakin fuskokin da ta gani da bakuwar motar da ke ajiye k'ofar Gidan Maigarin, wadda ko Babu tambaya zaa gano tasu ce duba da yanda ta hangosu yan gayu da wasu tufafi da suke sanye dasu iri d'aya da hula wadda a tashi d'aya za'a banbancesu da wayayyun yan boko, saboda kayan bautar K'asar da ke sanye a jikinsu dukansu su biyun da d'aya ya kasance fari yayin da d'ayan kuma yake baki-baki don ba za'a kirashi da wulik ba.

Tofa ga wata sabuwar cakwakiya🤣

Akafta😅

D/Auta CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*

*Lamba ta 9*

Dije garin kallonsu har da su tuntub'e sannan ta sami gefe ta rakub'e kamar wata ta ALLAH tana yafito su Hansai da suka saki Baki suna kallon bak'in Yan bokon, Maigarin ya karb'i wata farar takarda daga hannun wannan farin mutumen, sannan ya bud'a takardar sai kace daman cen shi d'in wani jan wuya ne a bokon, gano ko harafi d'aya bai gano maanarshi ba yasa ya mik'awa Liman takardar, shima ya duba yaga bai san komi a ciki ba ya kalli Dije yayi wata dariya yace

"Karb'i takardar nan karanta muna ita Yar gidan Baffahnta"

Dije ta ji k'irjinta ya buga dam! da shiri cikin sanyin jiki ta karb'i takardar ta Kura mata Ido kurum!tana so ta gano abunda ke ciki, don ALLAH ya taimaka da harshen hausa aka yi rubutun sai dai kasancewar ba kullum ake zuwa Makaranta a garin ba yasa ba duka hausar ta sani ba, aiko kai tsaye wani tunani ya zo mata ta d'ago kanta ta kalli Yan bokon da suma ita suke kallo, sannan ta mayar da kanta tana k'ara tantance takardar ta mik'e cikin fara'a da wata jarumta ta kalli mai garin tace,

"Sak'o ne aka aiko daga birni akan a had'a duk wasu matasa na garin nan za'a daukesu aikin Soja a turasu Maiduguri domin a kwantar da tarzoma"

Maigarin da sauran masu ruwa da tsaki da ke garin har ma da su kansu bak'in suka zaro Ido, cikin firgici Tambari ya mike jikinshi yana rawa ya kalli Babanshi yace

"Muje Baba kasan bana jin k'arfin jikina idanuwana ma ko gani basuyi sosai, watakila ma shikenan Ni da lafiyar Ido haihata haihata"

Ba shiri dayan bakon wanda ba fari ba ya kumshe dariyarshi yayi saurin cewa,. "A'a ba haka bane mu an turo mu ne daga birnin akan zamu yiwa k'asa aiki mu zauna da ku anan Garin mu dinga koyawa yara karatu har na tsawon shekara d'aya, fatanmu kawai ku bamu had'in kai don ku sani tab'amu tamkar tab'a k'asa ne, don kuwa akanmu mutum zai iya k'are rayuwarshi gaba d'aya a prison in har ya kawowa hukuma ganganci"

Maigarin da sauran mutanen da ke garin suka zaro Ido alamun tsoro, Maigarin kam sai gyad'a kanshi yake yi alamun gamsuwa da zancenshi, Dije kam tana jin haka ta fara hararar dan farin saboda ganin yanda yake ta wani cin magani yana binsu da kallon kyama, Maigarin da kowa aka yi ta yi masu sannu da zuwa da fatar nasara akan aikinsu da suka baro gidajensu suka zo kauyen da nufin su tallafa masu.

Daga nan Maigarin yasa aka je aka gyara masu masaukin da zasu zauna sannan aka yi masu iso suka fito da jakunkunansu da suka zo da su aka shigar masu da su.

Dije ta bi dan farin da wata jar harara aranta tace,.

_"jishi don ALLAH sai kace baya tsugunnin Kashi, mu za'a nunawa fari?? farin banza da wani janbaki da ya gogawa lebenshi don kitifirin bala'i"_
Chapter 8 · 0% Book details