Sashe 38
Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dije tace,. "Ke baki ga idonshi bane yanda suka koma jajjaye??"
Jummala ta yi saurin faɗin,. "WALLAHI Garbati baya shaye shaye don ko taba ma ban taɓa ganin yana busawa ba, wani lokaci dai ne nake ganin idanuwan suna komawa hakan ɗin, amman kuma daga baya sai su koma dai dai"
Dije tace "to ki yi haƙuri ni dai don ALLAH Jummala tunda dai ke ma fa kina son Garbati"
Jummala ta ce "in don so kam ina sonshi Dije amman abunda yake yi man ne bana so, sai inga kamar da mun mutu wuta ALLAH zai jefamu"
Dije ta miƙe tsaye tace,. "Ni dai haƙuri nike baki kuma ina baki shawarar ki daina ihu da kuwwar da kike yi ki barshi da ALLAH shi zai saka maki, don WALLAHI har an fara gulmarki a garin nan namu akan gudun da kike yi kina iface iface"
Jummala ta zaro ido waje tace,. "Na shiga uku Dije da gaske kike yi? Ashe ana jina wai ni ALLAH, gaske naga watarana yara suna zuwa gidan nan da sun kalleni suyi ta dariya"
Dije tace,. "Kaɗan ma kenan idan baki daina ba har sai kin fita kinji ana faɗin ga Jummala mai ihu cikin dare"
Jummala ta rufe baki tace,. "Aiko idan zai kasheni a gidan nan ba zan sake ihu har ajiyoni ba"
Dije tana saka talkaminta tace,. "Yafi maki dai ko don gudun gori watarana, tare da ƙananan gulmar masu yawan surutu"
Su Lanti da Mune suka taso ran Mune a jagule saboda ranta ya bata cewa da ita Dijen take, shiyasa ta yi saurin nufar hanyar fita tana faɗin
"Ni dai kunga tafiyata daman aikena aka yi na biyeku"
Dije tace,. "ALLAH ya kiyaye Mune sai mun haɗu gidanmu ko? ko shikenan daga nan munyi sallamar har in bar garin"
Mune ta washe baki tace,. "Rufani ki saya anjima kaɗan ma zan sameki gidan Gambon, bari dai in je inda aka aikeni in dawo"
Ta fice Jummala da Lanti suka ƙyalƙyale da dariya, Dije ma tana dariyar tace
"Mune mutunniyata ALLAH ya nuna mani ta daina halinta da naji daɗi"
Sannan Jummala ta rakosu har bakin gidan tana ƙarewa Dije kallo tace,. "Ashe gani duhu na yi maki ƙawallita, kinga yanda kika yi kyawonki masha ALLAH har da wasu kumatu kika fara yi, lalle birni ta karɓeki WALLAHi watarana ma ko ganeki nasan ba zamu yi ba"
Ke kika ce haka Jummala balle ni Dijen😝😂
Akafta🤣
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*AM BACK MY FAN'S albishirinku Littafina na BAƘON YANAYI na sakeshi free ga kowa, duk mai buƙata ya nemeni insha ALLAHu zan bashi kyauta ba sai ka biya ƙwandala ba, fatana kawai ku bini da ruwan addu'oinku kamar yanda kuka saba, ina yinku sosai alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke masoyana👍🏻*
*Lamba ta 39*
Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Haba Jummala ai duk inda na shiga ba zaki ce ki kasa ganeni ba, ballantana ma ai fuskata ba canzawa zata yi ba, ita ɗin dai ce wadda kika sani don haka ki ma daina wannan zancen, insha ALLAHu ni da ku mutu ka raba ƙawayena don kar ku ga wai don na je birni ku zaci watarana zan manta da ku, saboda komi na zama ai bazan taɓa mance Asalina ba, kuma muddin na tuno gida dole ne ku ma in tuno da ku, ni dai yanzu fatana kawai ki riƙe abunda na faɗa maki duk runtsi kada ki bari wani ya ji sirrin Mijinki, ALLAH ya baku zaman lafiya"
Jummala da Lanti suka ce "Ameen" ta rakosu har ƙofar gida tana ɗagawa Dije hannu tace
"Amman dai zaki dawo kafin ki koma ko?"
Dije tana shirin yin magana kenan suka jiyo muryar Garbati yana faɗin,. "Ta dawo ina? Ai ko wannan don kawai na so ne da WALLAHi ba zatan bata damar yin magana da ke ba, wannan ziyarar ma da aka kawo mun gode da ita, ina fatar ALLAH ya sa ba'a jangwalo man abunda zai fi ƙarfina ba"
Dije ta kalleshi sama da ƙasa tace,,,, "ka ma godewa ALLAH da har na zo na gyara abunda ka kasa gyarawa da kanka, idan ka ji tsoron Allah ka rage cin zalinta shikenan ka taimaki kanka, ni ka ga tafiyata don nasan darajar aurena bazan biyeka muna sa'insa ba"
Tana ƙare faɗar haka ta buga masa tsaki ta wuce abinta,Jummala ta ɗaga murya tace,
"Na gode Dije ALLAH ya biya sai kin dawo ai mun yi sallama ko?"
Dije ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta juyo ba ta ɗago mata hannu tace,
"Eh" Lanti ce kawai ta ce,, "to ya yi sai mun dawo jummala"
Suna tafe Lanti tana bata haƙuri akan abinda Garbatin ya yi mata, Dije saboda haushinshi ƙanzil ma kasa cewa ta yi har suka isa gidan Inna Gambo.
Yanayin yanda Gambon ta ganta yasa ta yi saurin faɗin,. "Wa ya taɓo mani Dijengalata ne? Daga zuwanta za'a fara ɗaga mata hankali"
Dije ta janyo tabarma ta zauna ta ce da Lanti itama ta zauna, bayan sun gaisa ne tace
"Wai ni kam Gambo yaushe Garbati ya koma haka ne??"
Gambo ta ce "tooh! Ke kuma Dije me ya haɗaki da Garbati ne?, Ko kin manta cewa da da yanzu ba ɗaya bane?"
Dije ta taɓe baki tace,
"Ai ni Gambo ba ruwana da sabgarshi shine dai yake son shige mani hanci, don Ni WALLAHI in Banda Jummala da ba abunda zai sa ma in ganshi in yi masa magana, saboda baƙar muguntar da yake yi wa Jummala don ya ga ita ba zata iya ramawa ba, don WALLAHI ALLAH in nice a dare ɗaya zan ji masa rauni"
Ta ƙare maganar tare da bubbuga hannunta tana dukan tabarma alamun da gaske take zancenta, Gambo ta yi mata wani kallo tana mere Baki tace
" To ko ke ɗin ce me zaki iya yi? Ballantana ma ni ina maki addu'ar ALLAH ya rabaki da wannan mugun hali irin na Jummala, Ai babu sakaryar yarinya irin wannan yarinya da bata da aiki sai tonawa kai asiri, saboda a garin nan ma mu yaushe rabonmu da wannan abun kunyar da haukar da take yi ne?, Ai ni WALLAHi ya biyani ma da ya ke koya mata hankali tunda har ita ta zama mara rufin asiri"
Dije ta bi Gambo da kallon baki san dawan garin ba ne, duk da wani gefe na zuciyarta kuma tana son ƙarin bayani akan zancen nata, ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Ke dai Gambo don baki san irin cutar da yake yi mata bane, don ke kanki kinsan Jummala ba ruwanta abun ne ya yi mata yawa shiyasa ta kasa haƙuri"
Gambo ta yi mata wani kallo tace, "To karkaɗe kunnuwanki da kyau kiji Jummala sam bata kyautawa kanta ba, saboda halinta na rashin haƙuri ne ya janyo komi, ina laifin Garbati don ya nemi yin kwanan aure da ita?, Mitssss! Ni bari inje in kawo maku fura ku sha ya fi man wannan magana mai cike da abun haushi"
Dije ta yi tagumi tanata nanata kalmar kwanan Aure a ranta don kawai ta gano ma'anarshi, amman ta kasa cikin zuciyarta tace
_"To ni kam wane kwanan Aure ne haka wanda har ake cin zalin mutum a kanshi?, wai ko dai Gambo bata gano abinda nake nufi ba ne shiyasa....."_
Hushin numfashin Gambon ne da taji a kusa da ita yasa ta yi saurin cire tagumin da tayi tana faɗin,. "Ni fa Gambo bana shan furar nan a ƙoshe nake"
Gambo ta maka mata harara tace,. "Ita furar ce yau bazaki sha ba Dije? Tab! Lalle birni ya sa kin fara canzawa, yanzu furar da har kokawa muke yi da ke akan sai kinsha ina ba zaki sha ba itace yau na baki a arha kike gwasaleni? To ai in ke ba zaki sha ba ke Lanti karɓi ki sha tunda dai nasan ba zaki ƙi cimarmu ba ke"
Gambo tana ƙoƙarin miƙawa Lanti furar Dije ta yi saurin riƙe kwanon tana turo baki tace,. "Ni dai bani in sha don naga kina ƙoƙarin ki canza man manufata"
Gambo ta buge hannunta Dije ta sake riƙe kwanon tana dariya tace,. "Sai fa na sha Gambo kafin ki bata tunda har ni kika fara yi wa tayi tun farko"
Gambo ta sakar mata tana faɗin,. "In banda ina tsoron ki janyo man asarar furar da ko lasata ba zaki yi ba, wai ma me ya janyo shi mijin naki da zai tafi ƙasar wajen bai je da ke ba??"
Dije ta kai ludayin fura bakinta tana faɗin, "sha kuruminki ko yanzu idan ya dawo tare zamu koma sai kinyi shekara biyar baki ganni ba, balle har ki yi man kora da hali, don haka ki rubuta ki ajiye sai kin nemi ganina da kuɗinki baki ganni ba, don ma ko da zan dawo na koma baturiya bazaki gane ni ba"
Gambo da Lanti suka fashe da dariya, cikin dariyar Gambo tace,. "sannu turawa masu jajayen kunnuwa sai dai kuma ke gashi naki baƙaƙe ne, to ko ya za'a zamo baturiyar da kunne baƙi Oho!?"
Haka suka ci gaba da firarsu mai cike da barkwanci suna dariya har aka aiko kiran Lanti daga gidansu, bayan tafiyarta ne Dije tana wasa da kare tana zane a ƙasa tace da Gambo,. "Wai ni kam Gambo in tambayeki? minene kwanan Aure da naji ɗazu kin faɗa?"
Gambo ta yi shiru na ɗan lokaci sannan tace,. "Yanzu ke baki san kwanan auren ba??"
Dije ta na dariya tace,. "Da na sani Gambo me zai sa in tambayeki? Ko yanzu abunda yasa na tambaya don bana son ya fito a jarabawarmu ta hausa ne ko wata rana wani ya tambayeni ya gano ban sani ba??"
Gambo tace,. "Hu'umm yanzu ke baki taɓa yin kwanan auren ba kike nufi ko yaya?"
Dije ta yi shiru sannan tace, "To ba bama sai in na sanshi ba sannan zanyi"
Gambo ta yi saurin cewa,. "Baki taɓa kwana ɗaki ɗaya da Mijinki ba?" Ta yi shiru tana nazari sannan tace "eh to na taɓa sau ɗaya lokacin da Hajiya ta matsa naje ɗakin Malaminmu na kwana, amman ni bansan me hakan yake nufi ba"