← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 84

Sashe 16

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lawi ya yi shiru sannan yace, "To Baba a matsayinka na mahaifinmu anan garin na baka wuk'a da nama akan lamarin"

Maigarin kam sai faman girgiza Kai yake yi cikin damuwa yace,. "Kana da masaniyar itace ta yi wa Abokinka turaren mayu har ya yi kwanciya Asibiti a sanadin hakan?, To bari in sanar da kai gaskiya tun wuri ka canza neman aurenka zuwa wani Gida, don wannan yarinyar mai Ido a tsakiyar kai ta shiga birni to ba'a san iya abunda zata aikata ba don......"

Liman yayi saurin katseshi ta hanyar fad'in,. "Ayi mata fatan shiriya watak'ila ma sanadin shigarta birnin a samu matsalolinta su kau"

Hmmmm😕

Akafta😅

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA A KOWACE NAHIYA KUKE CIKIN DUNIYA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, HADIZA D/AUTA TANA GODIYA SOSAI👍🏻*

*Lamba ta 16*

Maigari ya yi wani mere ya mayar da kai gefe alamun rashin gamsuwa da zancen Liman, ganin haka yasa Liman d'in ya gyara zamanshi yace

"Ni a tawa shawara abunda naga yafi a kira MALAM Sanda a sanar dashi zancen, ka ga duk abunda ya fad'a shikenan da shi za muyi aiki"

Maigarin ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace,. "To za mu kirashin duk yanda muka yi zaka ji yarona, amman ina son ka yi nazarin maganata kafin ka yi nutso cikin abunda zaka zo daga baya kana cizon yatsa, Sabida a zahirin gaskiya yarinyar nan kirin jijiya ce, bata jin magana ko kad'an ina ji maka tsoron ka je da ita cikin danginka ta wargaza maka zumunci da Yan uwanka"

Lawi ya kara sunne kanshi cikin sanyi murya yace,. "Ai yanzu kurciya ce Baba jikina yana bani zata natsu matuk'ar ta ga bata gaban Iyayenta"

Maigarin ya d'age kanshi a sama yace,. "Uhm lalle kam akwai k'urciya to ALLAh ya baka k'arfin gwiwar tunkarar matsalolinta"

Lawi ya washe Baki fuska a sake yace,. "Ameen Baba na gode ALLAH ya rufa asiri kuma ya ja da nisan kwana"

Maigarin da Liman suka ce "Ameen" Lawi ya mike tsaye yace

"Ni zan dan fita babban birni in yo muna siyayya"

Maigarin yace "a dawo lafiya ALLAH ya tsare"

Suka yi sallama Lawi ya tafi zuciyarshi cike da farin cikin ganin cewa tamkar ma Dijen ta zamo Matarshi, bayan tafiyarshi ne Liman ya yi ta fahimtar da Maigarin akan fa'idar auren Dije birni, amman Maigarin kam sanin wacece Dijen yasa sam yak'i gano abunda Liman yake son nusar dashi, sai dai ya aika a Kira masa Baffahn Dijen don ya ji ta bakinshi saboda shi ya sa a ranshi ba zai tab'a yarda ya yi tsanin abunda za'a zo daga baya ayi kuka dashi ba.

Aiko dan sak'on yana sanar da Baffah'n Dije bai yi k'asa a gwiwa ba ya garzayo cikin fad'uwar gaba domin ya ji kiran me ne Maigarin ya ke masa kuma yanzu, duk da wani gefe na zuciyarshi yana sanar dashi cewa Dijen ce ta sake aikata wani abin bayan sakawa D'anbirni turaren mayu da ta yi, don duk iya b'oyon da yayi akan kada a gano Dijen ce sai da Maigarin ya gano itace, don kai tsaye ya kira Baffah'n ya yi masa Kamar daman cen ya san itace d'in, ta sigar bugun ciki yace da shi,

"Sanda mai yasa 'yarka bata bari a zauna lafiya ne wai? abun ya wuce kanmu ga shi yanzu har ta fara tab'a bak'inmu, to WALLAHI wannan karon za ta janyo maka zama gidan kaso matuk'ar baka tsawatar da ita ta ajiye shirmenta da rashin hankalin da take yi a garin nan ba"

Baffah jikinshi ya d'auki rawa ya fara cewa,. "Don ALLAH ayi hak'uri WALLAHI na yi mata fad'a sosai akan wannan abun da ta aikata, kuma yanzu haka ma an samu ta rage duk wani k'irin ji da take yi, insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba"

Maigarin ya yi shiru sannan yace, "au! Ashe dai da gaske itace d'in ce ta aikata? Um lalle rashin mutuncinta sai hauhawa yake yi, to WALLAHI bari kaji ta sake kwatanta wannan shirmen a gaban kowa zan saka Bafade ya yi mata d"an banzan duka a garin nan sai ya farfasa mata jikinta duka WALLAHI ka ji na rantse kuwa "

Cikin fushi ya mike ya shige cikin gida sai Liman ne ya dinga fahimtar da Baffah'n akan abun da Dijen ta yi bata kyauta ba, Baffah sai hak'uri kawai yake ta badawa cikin sanyin jiki ya baro k'ofar Gidan Maigarin.

To shiyasa yanzu ya ji tsoron wannan kiran kuma da Maigarin ya sake yi masa, a sukwane ya isa ya zauna cikin d'ar d'ar ya fara mik'a masu hannu suka gaisa, sannan cike fargaba ya ce

"Gani ranka ya dad'e ALLAH dai yasa lafiya??"

Maigarin ya gyara zamanshi ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace, "to Sanda wannan kiran daban ya ke da sauran kiran da aka sha yi maka a baya, saboda haka ka natsu ka fahimci abun da zai fishsheka ya sama maka zaman lafiya Kai da 'yarka da iyalan gidanka duka"

Baffah ya gyara zamanshi ya ce "Ina sauraronka ranka ya dad'e"

Maigarin ya fesar da iska a bakinshi kai tsaye ya ce

"D'aya daga cikin bak'in yan birnin nan to mai wankan darzar ne ya ga 'yarka Dije yana sonta da aure, kai me ka gani zaka iya surukuta da mutanen birni ko kuwa?don shi dai wannan yaron dan Gombe ne, abokin tafiyarshi ne dan YOLA"

Baffah kam dirim! dum! yaji a cikin zuciyarshi don kuwa maimakon ya ji dad'in maganar amman sai dakan lugude zuciyarshi take yi, ya yi shiru na yan mintuna Maigarin yana ta yi masa kallon gefe yana girgiza k'afafuwa, sai cen Baffah'n ya yi jarumtar fad'in

"ALLAH ya taimake ka ni dai gaskiya bazan tab'a yin nisa da Dije ba, nafi son ALLAh ya bata Mijinta a garin nan in auradda ita kusa da ni, don haka Ina mai baku hak'uri akan ya samu wata kawai su daidaita amman Ni kam ba zan yi wa Dije aure a birni ba"

Maigarin ya gyad'a Kai yace, "kayi kyaun kai Malam Sanda Ni ma dai abunda na hango kenan tun kafin ka zo da naji maganar, insha ALLAHu zan sanar dashi sakonka ALLAH ya zab'a musu abunda ya fi alkhairi dukansu da mu gaba d'aya"

Baffahn ya ce "Ameen" har zai mike Liman ya yi saurin dakatar da shi yace,. "Malam Sanda ka je dai ka yi shawara kafin akai karshen maganar saboda shi fa aure nufin ALLAH ne, Kuma duk inda ya nufa cen za'a Kai Yarinya to mutum bai isa ya canza tsarin ALLAH ba don lamarin ALLAH ba'a yi masa shishigi, don haka ka da ka yi jayayya da hukuncin Ubangiji a cikin lamarin aure, ka je ka nemi zabin ALLAH kafin ka yanke hukuncinka na k'arshe akan maganar"

Baffah ya dan yi Murmushin yak'e yace,. "Na gode liman amman Ni Kam iya gaskiyata ce na sanar da ku, don kam Ni bazan yi wa Dije aure a birni ba, musamman ma dai gari irin wannan na nesa ka ga tafiyata na barku lafiya"

Baffah sai fad'a yake yi cikin zuciyarshi har ya isa gida in da kai tsaye ya zayyanawa Inna duk abunda ke faruwa Inna ta zaro ido waje tace

"Oh ni d'iyar mutum biyu yanzu ita Dije me ya had'ata da wad'annan Yan gayu da har zasu ce suna sonta? Ko dai basu dube yanayinta da kyau bane?"

Baffah ya galla mata wata jar harara yace,. "Fad'a man aibin da ke jikinta da har wani ba zai ganta yace yana sonta ba??"

Inna ta mik'e cikin sanyin jiki tace,. "Na ga dai ko Yan garin nan namu har yanzu babu Wanda ya tab'a cewa yana son Dije sai Bala,ko shi kuma har yanzu bai tab'a zuwa Gidan nan yace ya zo zance wajenta ba"

Baffah cike da fushi yace,. "Eh kam da yake tafi kowa muni kaf! kafatanin mutanen garin ba ai ko dole a k'ita kam, to ke Hasiya in tone tone kike so ayi sai in ce mace nawa aka aurar a garin nan wadda ko kafar Dije bata kamo ba? Ke kanki kinsan cewa rashin jinta ne kawai ya janyo ake jin shakkun zuwa neman aurenta, kuma insha ALLAHu da ta mallaki hankalinta zata dena ai"

Inna ta yi saurin fad'in "Da zaka bi shawarata Ni dai Malam da ka yi bincike akan asalin yaron, idan ka gamsu dashi shikenan sai a auradda ita a huta kaga ita hankalinta a kwance namu a kwance"

Baffah yayi saurin fad'in " nasha aradun ALLAH in za'a mayar da gabana gabas a yankani ba zan bashi auren Dije ba, kiji ki k'ara fad'a in dai har nine nake da ikon auradda ita to bazan kaita nesa da mu ba, auren nesa ko auren jaraba haka kawai in bada 'yata ayi ta cin zalinta bata da kowa a gari bale taje ta Kai masa kuka taji dad'i, Ina ai bazata sabu ba wai bindiga a ruwa"

Ya mike ya fice fuuu sai zabgar fad'a yake ta yi, mintuna kad'an da fitarshi sai ga Dije ta shigo da Yan wak'e wak'enta tana tsalle, Inna ta yafitota ta ce

"Ke zo nan"

Dije ta k'araso ta zauna nesa da ita cikin tsoron kada Inna tace ta yi wani abin kuma, Inna ta maka mata harara tace

"Ki matso nace"

Dije ta gurguso ta zauna tare da zunb'uro baki ta kumbure fuska, cikin k'ara had'e fuska Inna tace

"Miye hadinki da Abokin wanda kika yiwa turaren mayu??"

Dije ta washe Baki tace,. "ALLAH sarki ai yana da kirki Inna kinsan na ce maki shine ya aramani Littafin nan na koyon turanci, kuma WALLAHI kullum sai yaba kokarina yake yi har litrafan rubutu ya bani Inna ai na nuna maki su ko?"

Inna ta maka mata wata hararar tace,. "Au ashe ya dad'e yana sonki shine baki fad'a man ba??"

Dije ta zabura tare da zaro Ido waje tace,. "Kambala'innan Ni yake so?? Inna wa ya fad'a maki wannan bak'in kazafin? Haka kawai Ina zaman zamana a janyo man jarfa"
Chapter 16 · 0% Book details