← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 84

Sashe 59

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gobe idan ALLAH ya kaimu Ummi zata je da ke Abuja, zaki zauna a cen ki ci gaba da karatunki a cen, insha ALLAHu zata riƙeki kamar yanda na yi maki a nan, fatana kawai ke ma ki ɗauke ta tamkar yanda kika ɗaukeni, don duk da kinsani amman dole in ƙara sanar da ke cewa itace gaba da Safwan shi yake bi mata, ki yi haƙuri da duk abunda ya yi maki da sannu zai hankalta har ya dawo ya baki matsayin da nike ta yi maki fata a wurinshi, sai dai ki iya mu'amala da kowa saboda yanzu da da cen inda aka fito ba ɗaya ba, kina da aure kuma Mijinki yana sonki ko da ko bai faɗa ba, saboda ki riƙe masa amanar kanki kuma ki riƙe mutuncin aurenki, ALLAH ya baku haƙurin zama ki dage ki yi karatunki don shine gatanki ko don ke ma ki tallafi iyayenki da hannunki"

Dije ta yi shiru tana sharar ƙwallah tace "ALLAH ya bamu haƙurin zama"

Ummi da Hajiya ta ce "Ameen"

Tun cikin daren ranar Hajiya ta haɗa mata kayanta tsaf! Asubar farin Garba ya zo ya ɗaukesu suka kama hanya sai fatan sauka lafiya ake ta yi masu, bayan tafiyarsu ne Hajiya Mama ta riƙo kunnen Fiddo ta ce

"Ke kuma WALLAHi ko da wasa na ji kin sanar da shi cewa ga inda Matarshi ta ke, to ki sani daga ranar kin bar gidan nan, don kuwa ƙauyensu Baabah Kulu zan kai ki cen ki zauna har sai an tashi aurenki a dawo da ke nan"

Fiddo ta zaro ido waje tace "Haba Hajiya wannan mugun ƙauyen? Ai WALLAHi ni ko yini ɗaya ba zan iya yi a cen ba bale har in yi rayuwa a cen tab! Mutuwa, Hajiya garin da ko toilet ba bu daji ake kashi kike so in je inyi rayuwa a cen?"

Hajiyar ta sunne dariyarta tace, "to idan ba kya so ki ceci kanki kawai a wuce wurin, amman WALLAHi duk ranar da naji kin faɗa masa inda take to a ranar zaki bar garin nan ki je cen"

Fiddo ta yi saurin shigewa ɗakinsu tana zancen zucinta tana faɗin, "to ni me ma zai sa in faɗi inda take tunda har ma ba wani damuwa ya yi da ita ba, kuma ma ni daga ALLAH ya rabamu da ƙaya ai godiya yakamata inyi wa ALLAH ba wai faɗa masa ba, don ni har kuɗi ma zan iya badawa akan kada ya gano inda take"

Ta faɗa gadonsu cike da jin daɗi tace"ALLAH ya raka taki gona WALLAHi Ummu ta gayar da Aysha"

***

Safwan kam a kiɗime ya isa Gomben kai tsaye Asibitin ya nufa don ko Lawi bai nemi rakiyarshi ba, sai kuwa ga shi zuwan ya yi rana don kuwa ko da ya je numfashinta sama tana kiran sunanshi cikin dusashiyar muryar da ta sha ciyo na faraɗ ɗaya, mahaifiyarta da Daddynta da sauran Yan uwanta da Aminu da ƙawarta Ruma duk kuka suke yi, ganin Safwan ɗin da ta yi ne yasa ta yi saurin kiran sunanshi da ƙarfi ta some, ai kuwa ɗakin ya ɗauki kuka saboda tsammaninsu ko ta rasu, shi kanshi Safwan ɗin kwatanta tashin hankalin da ya shiga abu ne babba, saboda ganin yanda ta rame lokaci ɗaya sai karen hanci da ya fito idanuwanta duk sun zurma, hankalinshi bai kwanta ba har sai da likitoci suka rufu a kanta tare da yin nasarar zuƙo numfashinta, cikin dawowar numfashin ne ta fara nishi sama sama tare da sauke numfashin da sauri da sauri, Mahaifin Zee ya zo gabanshi ya duƙa hawaye suna kwaranya akan fuskarshi ya ce

"Ka taimaki ƴata ta dawo cikin natsuwarta"

Aminu da ke tsaye ranshi a ɓace ya fice ɗakin, Safwan ya ɗago Mahaifin Zee ɗin ya miƙe cikin kwantar da murya yace

"Ka yi haƙuri Alhaji Insha ALLAHu ALLAH zai bata lafiya"

Muryarshi da ta ji yo yasa ta yi saurin faɗin sunanshi, Likitan ya ce ya matso kusa da ita ya bashi wuri ya matsa jikin gadon, Zee ta yi saurin riƙe hannunshi ƙam ƙam tana zubar da wasu hawayen takaicin kanta ta ce

"Me yasa ka yi man ƙarya? Me yasa ka amince da ni bayan kasan kana da matarka wadda ka fi so fiye da ko wace mace?, a hakan ka so in aureka in je inyi auren boranci? Ina sonka my man amman ka sani ko da zan mutu ba zan aureka ba, na yafe maka abunda duk ka yi mani ALLAH ya haɗa fuskokinmu a al..ja..n...n...ah"

Sarƙewar da numfashinta ya yi ne yasa ta sake somewa, Mahaifiyarta ta fashe da wani uban kuka, Ruma da ƙawarta da sauran matan da ke ɗakin suma suka kwantsama kukan, da ƙyar likitoci shawo kansu wajen fitar da su ɗakin suka dawo kan Zee ɗin suna ta aikin neman ceton rayuwarta.

Wayyo Zee Baby😢

Akafta🥰

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Addu'o'inku da kullum kuke bina da su ba ƙaramin faranta man zuciya suke yi ba🥰, na gode 🙏🏻sosai Mutanena Alkhairin ALLAH ya kai maku a ko ina kuke👍🏻 muna kyawon tare🤝🏻*

*Lamba ta 56*

Likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu amman numfashinta sai sama da ƙasa yake yi, wani likita ya ce da Safwan ɗin ya yi mata magana cikin daɗaɗan kalamai, ko da ALLAH zai sa ayi nasarar ceto ranta cikin mawuyacin halin da take ciki, saboda tana sonshi idan ta ji muryarshi kuma ALLAH ya shiga cikin lamarinta aka yi dace za'a yi nasara.

Safwan riƙe da hannun Zee ɗin da har lokacin take riƙe da shi jabau!, yana hawayen tausayinta ya ce

"Plss my precious ki tashi gani a kusa da ke, ke ma kinsan ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu ke ba, plss and plss for give me i apologies for you and everything else, ki tashi ki kalleni ido cikin ido in sanar da ke a shirye nike da aurenki a kowane lokaci, kinsan na yi maki alk'awali kuma insha ALLAHu bazan saɓa ba, ki tashi ki kalli Man ɗinki ki ido cikin ido ki ce kin yafe masa plss my dream"

Ya ƙare maganar cikin wata muryar kuka saboda yanda yaga har lokacin numfashinta ya ƙi daidaita, saboda yana jin tsoron ace ƴar mutane ta mutu ta sanadinshi, ganin anƙi samun abinda ake buƙata ne yace da likitocin su bashi minti biyu, saboda sun san kan aikinsu yasa suka bashi haɗin kai wajen ficewa dukansu, Safwan ya miƙe ya yi sunkuyo saiti da fuskarta ya buɗa bakinta ya saka nashi ciki, cikin wani salo ya fara zuƙo numfashinta a hankali tare da yi mata kalamai masu sanyi tare da kiran sunayen da suke faɗawa junansu cikin wata murya mai tsada, cikin nasara Zee ta dawo hayyacinta tare da fara zubar da hawaye gefe da gefen fuskarta, sannan ta ƙura masa ido ko ƙiftawa bata yi saboda ganin take yi abun kamar almara ko a mafalki, Safwan ɗin da ko hannunta bai son taɓawa ko acen ƙasar Turai wai shine yau da tsotsar bakinta, cikin mayen sonshi da ke fisgarta ta riƙe hannunshi gam ta ce

"My man me yasa ka yaudareni?"

Ya yi saurin ɗora hannunshi akan lebenta yace, "ki bar zancen plss a shirye nike da aurenki a duk lokacin da kika tashi"

Zee ta washe baki cikin farin furucinshi ta ce, "duk da ka yaudareni amman still har yanzu ban daina sonka ba, me yasa so yake makaho ne? me yasa zuciyata ta ƙi karɓar ƙiyayyarka da na yi ta cusa mata?, Haƙiƙa ka yi nasarar samun sarautar zuciyata You are my prince chrmn and my everything shonah"

Safwan cike da tausayinta yace "na yi kuskure ki yafe mani albarkacin son da kike mani ko don ceto lafiyarki, saboda ko da ina son a yi muna auren yanzu kin ga sai an jira kinji sauƙi tukunna, don kin san ba za'a yi aure kina cikin ciwo ba"

Zee ta yi saurin share hawayenta ta yunƙura da nufin ta shi zaune amman ta kasa, dole ya riƙata ta tashi zaunen tare da taimaka mata ta jingina jikinta da filo tana binshi da kallon ƙauna, cike da jin daɗin ganin nasarar da aka samu ne Safwan ɗin ya leƙa ya kira likitocin, abun mamaki sai ga Zee sun taradda ita zaune tana share hawayenta jefi jefi.

Cikin sauri wani likita ya kira Iyayenta suka shigo cike da jin daɗin albishirin ɗin da ya yi masu, mamaki fal zuciyoyinsu saboda ganin yanda ta ke zaune har da su dariyar ƙarfin hali, dukansu har likitocin sun gasgata ba ƙaramin so Zee take yi wa Safwan ba, Aminu kanshi da ya dawo ya taradda ita zaune ana bata tea tana sha ya jinjina lamarin, take yanke ya sallamawa kanshi barin Zee ko don ta samu abinda take so, saboda a yanzu ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya yi abunda ALLAH bai tsara a cikin rayuwarshi ba, haka wani bai isa ya auri matar da ba ta shi ba, don da tuni ya aureta saboda dakon sonta da ya yi ta yi a zuciyarshi tun tana ƙarama.

Kowa sai murna yake yi kan haka ne ma mahaifin Zee ya ja hannun Safwan ɗin suka fita, cike da jin daɗin ganin ƴarshi ta fara dawowa hayyacinshi yace

"Duk da bansan me ya haɗaka da Zainab ba amman jikina ya bani cewa kai ka janyo mata shiga halin da take ciki, a matsayina na Mahaifinta ina roƙonka da ka taimaki rayuwar ƴata ka aureta, tunda har kai take so ni ba zan takura rayuwarta ba saboda haka ba zan taɓa aura mata wanda bata yi na'am da shi ba, idan ka shirya ka turo iyayenka ni zan aura maka ita da hannuna ko da kowa baya so, tunda tana sonka ni ma kai nake so na aurawa ƴata"

Safwan ya yi shiru yana nazarin mafita saboda ya rasa ta wace hanya zai nunawa Baban Zee shi ba zai aureta ba, amman cikin zuwan wata dubara ya buɗa baki zai yi magana Baban Zee ya dafa kafaɗarshi ya ce
Chapter 59 · 0% Book details