← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 84

Sashe 73

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zee ta daɗe durƙushe anan tana kuka har sai da Ruma ta zo ta ɗagata suka shiga ciki, inda suka taradda mahaifiyarta itama sai kukan take cisga gwanin ban tausayi, saboda takaicin abinda Zee ta aikata wanda tuntuni take nusar da Daddynta akan sangarcin da ya yi mata don ko kaɗan baya so a kyareta bale a nuna mata laifin da ta aikata ta gyara, to ga irinta nan yanzu ta janyo masu abun gori wurin mutane, Zee ta je ta rungume Mahaifiyarta tana wani irin kuka mai cike da ban tausayi, Mahaifiyar ta tureta har sai da ta faɗi ƙasa, sannan ta miƙe tsaye tare da nunata da yatsa ta ce

"Babban kuskuren da zaki aikata shine ki sake zuwa kusa da ni, don haka ki je tunda kin isa da kanki ki aikata duk abunda kike so, duniya ce wanda bai zo ba ma jiranshi take yi, kuma ta ishi kowa riga da wando har da zanen ɗaurawa"

Tana ƙare faɗar haka ta shige ɗaki abunta har da su dantse ƙofa, Zee ta sake fashewa da wani sabon kuka Ruma ta dinga bata haƙuri, amman ina yanayin da take ciki yafi ƙarfin ban haƙurinta, dole ta zura mata ido tana kallo zuciyarta cike da jimamin abun a ranta, tare da godewa ALLAH akan ƙoƙarin da ta yi wajen hana Zee cika burinta akansu Safwan da abunda zai faru ALLAH kaɗai yasan iyakacinshi akan matsalar.

****

Dijen Baffah kam ita da Malaminta sai cin amarcinsu suke yi hankali kwance, don ma masu zuwa jaje suna takurasu amman duk da hakan bai hanasu baiwa juna kulawa ba, cikin ɗan lokacin daga shi har ita sun sauya saboda natsuwar da suke samu da junansu, don shi Safwan ko tuno Zee baya son yi a ranshi, saboda ya riga da ya shafe babinta a rayuwarshi duka kuma yasa a ranshi duk runtsi ba zai sake zaman aure da ita ba, igiyar auren ce dai ta yi ta sha zamanta lafiya ko ita don ba ya iya saɓa umurnin Hajiyarshi ne da tuni ya cikasa mata ukunta ta huta.

Safwan kwance a falon Dije yana mayar da reply ga masu yi masa jaje ne ta fito ɗakinta cikin sanɗa ta zo bayanshi ta tsaya, sannan ta yi saurin duƙowa saitin kunnenshi cikin ɗaga murya ta ce

"Habiby!!!!!!"

Ba shiri ya zabura tare da jefar da wayar cikin firgicin da ta sakashi, Dije ta dafe ciki tana ƙyalƙyala dariya tana nunashi da hannu, cikin dariyar shi ma ya miƙe da nufin kamota ganin haka yasa ta fara gudu tana dariya, shi ma ya biyota yana faɗin

"Babyluv ki tsaya tun baki janyowa kanki aiki ba"

Dije ta dinga gudu sunata zagayen falon har ya ci nasarar cafketa suka faɗa kan kujera tare suna mayar da numfashi, Dije tana kyalƙyala dariya tace

"Don Allah Malam ka yi haƙuri ba zan sake ba"

Safwan ya cusa kanshi cikin wuyanta yana shinshino ƙamshinta idonshi a rufe ya ce

"Tunda baki tausayin kanki ai nima bana gajiya"

Dije ta yi sauri zaro ido tare da marairece fuska ta riƙe kunnuwanta duka biyu ta ce

"Am sorry my luv"

Idonshi a lumshe ya fara yamutsata tana zillewa tare da bashi haƙuri amman duk da hakan bai hanashi yin abunda yake so ba, bayan ya kammala ne ya koma faɗin

"Ke kika janyoni don haka dole ne ki yi haƙuri da halin Mijinki, faɗa man me kike so in yu maki ni ma wanda zan faranta maki tukuicin farin cikin da kike sakani?"

Dije ta zumɓuro baki wa je ta ce

"Baffah'na nike son in je in gano kwanan nan sai mafalkinshi nike yi"

Safwan ya zaro ido waje ya ce "canza wani don bazan lamunci doguwar tafiya da ke ba a yanzu, don ban sani ba ko na yi ajiya a jikinki ki zo ki jaza man jinya ba"

Dije ta ɓata fuska tace

"To Ni dai shi kaɗai nike so tunda na riga da na zana jarabawata da sai in ce ita, sai kuma in zaka kaini in fara karatun nursing ɗin tun yanzu"

Ya miƙe ya nufi ɗakinshi yana faɗin "in dai karatu ne har sai kin ce kin gaji amman tafiyar da kike so ce nake tantama, amman idan na yi shawara zan sanar da ke abunda na yanke"

Dije ta yi saurin miƙewa ta biyoshi tana faɗin "Don Allah ka barni inje WALLAhi na yi kewarsu Inna raboda da cen tun lokacin da Hansai ta haifu fa"

Ya yi saurin juyowa ya ce "to ke ma idan kin haifun ai sai ki je ba wani abu bane ba"

Dije ta fara kumbura fuska tare da rufe ido ta ce ",to Ni ina na isa yin cikin ma?"

Ba shiri ya fashe da dariya tare da dawowa inda take tsaye ya rungumota yana kallonta ya ce

"Baki isa ba ko?"

Ta ɗaga masa kai tana rufe ido, ya sake yin wani murmushi ya ce "Ok tom ya yi mu je in aunaki in gani in har da gsk baki isan ba"

Dije ta zare jikinta ta ce "A kaini Asibiti dai likita ya aunoni ai shi zai gano ban isa ba"

Ya ƙara janyota jikinshi ya sakar mata wani kiss a wuya ta zabura tare da kai masa wata kalar harara, ya yi dariya sannan ya ɗago fuskarta ido cikin ido ya ce

"A ganinki akwai wani likitanki bayan Ni Malaminki? To buɗe kunnuwanki ki ji, kinga waɗannan abubuwan sun ƙara cikowa"

Ya ƙare maganar tare da damƙo dukiyar fulaninta ta yi saurin lumshe ido, ya bita da kallo cike zallar ƙaunarta da sha'awarta da kullum take ɗibarsa, ya sake matso hips ɗinta ya ce

"Shi ma wannan ya ƙara buɗewa alamu sun nuna ni ɗin ba ƙaramin jarumi bane, don haka daga yanzu ki ɗauki kanki dai dai da matsayin mace mai ciki, saboda haka ba inda zaki je amman in har su ɗin kike son gani zasu zo har gidan nan ki gansu insha ALLAHu"

Dije ta yi saurin buɗe idonta tare da yin wani tsalle ta maƙalƙaleshi cike da tsantsar farin ciki ta ce

"Wayyo Habibyna shiyasa nike bala'in sonka"

Baki sake ya ce

"To bi a hankali kafin ki sanar da ni irin bala'in sona da kike yi don bazan lamunci a yi man asara ba"

Dije ta rufe idonta tace

"Wai da gaske cikin ne da Ni?"

Yana dariya ya ce "idan kina tantama ki bani nan da sati biyu zaki gasgatani"

Ta yi saurin barin wurin ta shige ɗakinta tana dariya wai ita kunya, ya bita da kallon ƙauna sannan ya shafo kanshi ya shige nashi shima saboda magriba ta kawo jiki kuma yana so ya sami jam'in SALLAH a Masallacin da ke manne da gidanshi, wanda bai wuce sati ɗaya da buɗashi ana sallah a ciki ba.

Tsuntsayen soyayya ayi a hankali kar ƙone wajen cinta da zafinta😝

Akafta👩🏻‍🦯

D/AUTA Ce ✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*

*Lamba 67*

Zancen Safwan ya tabbata don kuwa sati biyu bai cika ba Dije ta fara laulayi mai ɗan karen zafi, don kuwa ruwa ma idan ta sha sai ta amayesu, ga shi a lokacin Safwan ya fara zirga zirgar neman aikinshi, inda aka yi dace aka nemeshi Abuja interview, shiyasa ya mayar da ita wurin Hajiya amman ko da yaushe suna maƙale a waya har ALLAH ya dawo da shi, sannan ya kwashi Matarshi suka koma gida yana ci gaba da renon abarshi, don kuwa duk abunda take so baya jin nauyin dattijuwar da ke taya Dijen aiki yake zagewa kitchen ya yi mata, ko ba daɗi ta cinye tana santi daga baya kuma ta amaye tass!, Haka suke abu ƙaɗan ya ce sai sun je Asibiti an dubata don baya son ta zauna cikin gida da wata matsala a tattare jikinta, shiyasa duk wani abu sai ya nemi sani tare da shawarwarin ƴan Asibitin, duk da wani zubin yana biyewa son zuciyarta ya yi mata duk abunda ta ke so saboda kawai ta yi farin ciki, don ba ƙaramin jin jiki take yi ba, cikin haka ne Safwan ya tura direba ba tare da ta sani ba ya ɗauko su Baffah da Inna da Hansai da Usmanu don Gambo ta ce ita ta yi tsufa ba zata iya yin wannan doguwar tafiyar ba, duk da har a ranta ta so ace ta je ta dubo jikallenta, amman yanayin jikinta na tsufa yau lafiya gobe ciyo yasa ta haƙura ba don tana so ba.

Dije cike da mamakin ganin gidan wasu ƴan'uwansu Safwan da su Surayya a kitchen sai hidimar dafe dafe da soye soye suke yi, in sun sauke wannan su ɗora wancen gida ya runtume sai zuba ƙamshin garar da ake ta haɗawa su Inna ake yi, duk abunda aka yi sai an kawo mata ace ta ɗanɗana ta ji in ya yi, cike da mamaki take tambayarshi wai halan wasu baƙi ne zai yi masu muhimmanci shiyasa ake ta wannan hadahadar?, Yana dariya ya ce

"Ke dai ki ci ki ƙoshi ki sha maganin amanki ki je ki yi wanka ki tsalo kwalliyarki cikin sababbin ɗinkunanki"
Chapter 73 · 0% Book details