← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 84

Sashe 36

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Soyayya da tasiri in har an saka tarbiyya,idan zaka yo komi farko ka fara yin niyya, duk mai ƙinka in ya biyo hanyarka za ya sha kunya, fasahar gwani matsayi nai ya fi inda zai zauna, hanci kan ji ƙamshi baki sa ƙashi ka ɗan tauna, ido kan ga haske linzami kace da ni suna ahaaa😉*

*Lamba ta 37*

Kafin ka ce me sai ga fiddo ta tada kwanon ɗan'waken tare da ɓalle murfin lemun da Baffah ya siyo masu, ta kafa kai ta kwankwaɗe tass ta jefar da gorar ta buga wata uwar gyatsa tare da shafa cikinta ta kalli Hajiya Mama da itama ɗin ita take kallo tana yi mata dariya, Fiddo ta wayancewa da faɗin

"WALLAHI ashe dai naji yunwa sosai Hajiyarmu"

Hajiya ta yi mata wani mere tace, "Naga alama kam tunda gashi har kin tada kwanon ɗan'waken duka, bayan ko daɗinshi ma baki ji ba"

Fiddo ta yi saurin ƙyalƙyalewa da dariya tace,. "yunwa ce naji ai"

Hajiya Mama tana dariya tace "Ga wani ki ƙara ko da ALLAH zai sa ki ji yunwar ta yi nesa da ke"

Fiddo ta yi saurin faɗin,. "A'a naƙoshi fa amman da ace wannan yarinyar zata iya irinshi idan mun koma gida ai da sai ta dinga yi man kawai"

Hajiya Mama ta yi saurin ɓata fuska tace,. "Eh kam tunda zamanki take yi me zai hana ta yi maki WALLAHI ki kiyayeni tun kafin ki janyo in barki garin nan tare da Khadijah har sai kinyi sati biyun da zata yi, kinga shikenan sai ki tayata ganin gidan"

Fiddo ta zaro ido waje tace,. ,"Don ALLAH kiyi haƙuri WALLAHI na daina"

Suna cikin firar ne Surry da Dije da su Lanti suka shigo Dije ta gabatar da su ga Hajiya Mama, cike da jin daɗi take amsa gaisuwarsu saboda ganin yanda suka durƙusa har ƙasa suna gaidata cikin ladabi cikin farin ciki ta yi masu kyautar kuɗi sunata godiya cike da murna.

Bayan komi ya lafa ne aka sake sabuwar gaisawa tsakanin Hajiya Mama da su Inna Hasiya, inda take sanar da su Safwan baya ƙasar ya je ƙaro karatu na tsawon shekara uku, amman ta sanar da su Dijen zata ci gaba da zama a hannunta har ALLAH ya dawo da shi lafiya, sannan ta sanar da su zancen makarantar da Dijen take yi, cikin jin daɗi su Baffahn suka yi masa fatar dawowa lafiya, tare da yiwa Hajiya Mama godiya da irin kayan arzukkan da ta cikasu da su, tsakanin kayan abinci da kayan masarufi, sannan ta kawo jimillar kuɗi har dubu ashirin ta basu tace su yi cefane, Baffah da Inna saboda tsabar jin daɗi har kukan murna suka yi sai zuba godiya suke yi.

Dije ta ja Surry suka yi gidan Inna Gambo domin su gayar da ita, suna cen ne su Hajiya Mama suka taraddasu aka sake aza sabuwar gaisuwa da Inna Gambon inda take ta yi wa Dije sharrin ta je birni tasha jar miya ta fara manyan kumatu, Hajiya Mama ta saki jiki ta dinga kare Dijen cike da barkwancin suka baro gidan bayan ta cikata da kyautar bajinta, sannan suka dawo gidansu Dije inda suka taradda Maigari ya aiko masu da kwano fam da naman kajin hausa da yasa aka yi masu dafuwar ruwa sun dafu lunguɓus sai ƙamshin daddawa da kayan yaji ke tashi, aiko cike da zumuɗi Surry ta fara ɗanɗanawa tana rawar kai ta zuzzuba masu har da Direbansu sannan ta ɗauki sauran ta kaiwa Inna Hasiya tace suma su ci, Inna cike da jin nauyi ta nuna mata ai ba komi su na gida ne su ci abunsu kawai, amman duk da haka atafau ta ce dole suma sai sun ci tunda suma ɗin ai ba baƙi bane.

Haka suka yi ta harƙallarsu cikin mutunta juna har zuwa marece, sannan suka shirya tsaf da nufin tafiya sai ga Usmanu ya dawo kan Babur ɗinshi da Baffah ya siya masa don zirga zirgar kasuwancinshi da ya fara cikin babban birnin, cike da jin daɗin ganinsu ya gayar da su a mutunce Dije sai farin ciki takeyi saboda ganin ɗan'uwanta.

Sun kimtsa tsaf da nufin tafiya saboda akwai inda zasu je su kwana da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola direct, sannan aka yi masu rakiya har gidan Maigarin suka je suka kai masa gaisuwa tare da godiya akan ɗawainiyar da aka yi da su, Mama Hajiya ta yi masa alkhairi tare da matanshi sannan ta fito aka rakosu har bakin motarsu ana yi masu ALLAH ya kiyaye.

Dijen ma sai wasar baki take yi tana yi masu bye bye sai dai suna haɗa ido da Fiddo ta galla mata ƙatuwar harara tare da murguɗa mata baki, Fiddo ta taɓe baki tare da yi mata wani mere tana yatsinar fuska, Hajiya Mama kam haka suka rabu cikin aminci tare da kewar juna, zuciyar Hajiyar fes saboda jin daɗin karamcin da aka yi masu, uwa uba sauƙin kan da Baffah'n Dije ya nuna akan rashin zaman Safwan gida tare da 'yarsu.

Bayan sun tafi ne Dije da su Baffah suka koma cikin gidan zuciyarsu cike da girmama irin mutuncinsu Safwan, Baffah sai jinjina lamarin Ubangiji yake yi tare godiya gareshi akan haɗasu da yayi da surkai nagari, waɗanda suka san mutunci tare da girmama ɗan'adam k ko da ko sun san cewa sun fisu nesa ba kusa.

Sauka lafiya su Hajiya Mama😆

Not edited😓

Akafta 😉

D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Alhmdllh Alhmdllh lalle dole ne in fara godiya ga Ubangiji kafin in ce komi, saboda jin daɗin yanda kuka nuna man ƙauna ta zahiri tare da ɗinbin karamcinku gareni ni D/AUTA, ku sani naji matuƙar daɗin ganin irin ruwan addu'o'inku gareni masu ɗauke da fatan alkhairi iri-iri, haƙiƙa duk wanda ALLAH ya baiwa masoya ya ji daɗi a rayuwarshi ta duniya, kamar yanda ni ma a yanzu naji mugun daɗi marar misaltuwa akan zallar ƙaunar da kuka nuna mani tare da littafina na DIJE ƘARANGIYA, naji daɗi na gode sosai wallahi ALLAH ya bar zumuncinmu da ku har aljannah, ni ma ina sonku all my FAN'S son so fisabilillah💋*

*Lamba ta 38*

Baffah saboda tsabar farin ciki nan take ya ce da inna, "idan ALLAH ya kaimu gobe ki ɗibi gero ki yi wainar sadaka a raba ko don mu nunawa Allah jin daɗin baiwar da ya yi muna, don WALLAHI sai yanzu nake jin nauyin abunda na aikata lokacin da na ke son hanawa Dije auren Malaminsu, musamman wancen yaron da shine tun farko ya fara yi wa Dije so na tsakani da ALLAH, ashe alkhairin nata wajensu yake ina ta ƙoƙarin hanata kaiwa wajenshi, Dije ki ci gaba da yi wa mutanen nan biyayya don ALLAH saboda ba ƙaramin mutunci ne da su ba, don ko a cikin masu kuɗin su nasu mutuncin daban ne, yanzu ki duba ki ga yanda suka saki jiki da mu tamkar cewa daman cen mun saba da su, Wallahi Ni dai kai bakina ba zai gaji da zunduma masu addu'ar fatan alkhairi tare da gamawa lafiya ba.

Dije tana wasa da gefen gyalenta tana ta wasar bakin jin daɗin yabonsu da yake yi, sai ko SAFWAN ya faɗo mata a rai ta saurin ɓata fuska tace

"To ai kai Baffah ita da surry ne masu mutuncin amman shi kanshi malamin namu fa ba halin kirki ne da shi ba, tare da wannan ƙanwar ta shi ƙarama WALLAHI in banda na ke tuna cewa kace kada in biyeta da tuni na aikata mata mara daɗi, don fa kusan kullum da sai ta tsokaneni da faɗa"

Baffah ya yi murmushinsu na manya ya ce,. "Ai shiyasa nake ta saka maki albarka saboda kawai biyayyar da kike mani ko da baki ganina kusa da ke, amman kada ki in sake jin kin faɗi cewa Mijinki ba shi da kirki tunda har ya nunawa duniya matsayinki ya aureki ai ya gama maki komi Dije"

Dije ta ɓata fuska tace

"Wallahi fa ba sona yake yi ba Baffah har kuɗi fa ya baiwa Balan Duduwa ya toshe masa baki akan ya bar masa ni, to mai sonka ne zai yi maka irin wannan kutunguilar?"

Baffah ya yi dariya mai sauti yace,. "Yaro man kaza to ai sonki ne da yake yi ma yasa ya bada kuɗin don kawai ya sami damar aurenki, don idan har da gaske baya sonki ai ba abunda zai sa ya damu don kawai wani zai aureki, amman kin ga yanzu sonki ne ya janyo ya yi amfani da damar da ALLAH ya bashi ya yi nasarar aureki, don haka ko da wani kika ji ya faɗi hakan to kada ki yi shayin ce wa da shi ni Baffahnki Ummaru Sanda nace ƙarya yake yi, ko da ko shi mijin naki ne kika ji ya faɗa to bance ki amince da zancen ba, don kuwa so mai suna so yake yi maki ko da ko bai faɗa ba"

Dije ta share guntayen hawayenta tace,. "To Baffah me yasa kullum yake ta yiman mugunta??, WALLAHI fa Hajiya kamar zata dake shi watarana idan taga yana cin zalina"

Baffah daɗi ya sa bakinshi yaƙi rufuwa yace,. "Ki godewa ALLAH Dijengalata saboda ya yi maki baiwar da ba kowa yake yi wa irinta ba, ki ce Alhmdllh kawai sai ya ƙaro maki wata ɗaukakar"

Dije ta washe baki tace,. "Alhmdllh na godewa ALLAH Baffahna WALLAHI na ji daɗin bokon da Hajiyar ta sakani, saboda na haɗu da mutane masu mutunci Baffah, WALLAHI baka ga yanda suke sona ba don ɗaya ma har karatu take ƙarani duk da su nasu karatun ba irin namu na nan garin bane, amman na fara ganeshi har ma na Kai hizif talatin wurinta Baffah, duk da fa cewa ta yi dole sai na dawo baya tun farko amman na yi nisa wallahi"

Baffah ya faɗaɗa fuskarshi da fara'a yace,. "Ai duk inda kike albarkar da muke saka maki tana tare da ke, ke dai ki ci gaba da haƙuri kawai da sannu zaki zamo abar kwatance a wannan garin namu, tashi ki je ki yi SALLAH idan na dawo masallaci mu ci gaba da firarmu kawai"
Chapter 36 · 0% Book details