← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 84

Sashe 62

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki yi haƙuri nasan zaki ga abokiyar zamanki bata sami halarta bikin ba, to hakan ya faru ne a sanadin hidimar karatun da ya sha kanta, amman ina fatar a duk lokacin da zama ya haɗaku ki yi ƙoƙari ki baiwa Mijinki haɗin kai wajen yi maku adalci a tsakaninku, ALLAH ya baku zaman lafiya a tsakaninku duka ya kawar da sheɗan cikin gidanku gaba ɗaya"

Kowa sai "Ameen Ameen" yake faɗa sannan ta kawo dunƙulalliyar kyauta ta bata, aka fito da Zee mutane da yawa sai yaba kirkin Hajiyar yake yi, inda kai tsaye aka wuce da Zee katafaren gidan Safwan wanda ya laƙume maƙudan kuɗi wajen haɗashi ta ko'ina, inda itama kanta Zee iyayenta suka zuba ta su bajintar wajen ƙawatashi da kayan ƙarau lungu da saƙo, abun dai masha ALLAH sai wanda ya gani don tsayawa misalta haɗuwarshi ma ɓata baki ne, saboda haka masu karatu na baku wannan aikin wajen misalta gidan da kanku.

Har ɗakinta aka kaita iyaye da ƴan uwa da ƙawayenta sai addu'ar zaman lafiya su ke yi mata, saboda ganin yanda ta haye wajen samun kyakkyawan Miji da kyakkyawan muhallinta gwani burgewa, uwa uba itama gata kyakkyawar farar mace kuma ga su da hannu da shuni ta ko'ina suka motsa nera kukan wahala ta ke yi, saboda akwai kuma an tara babu abunda zai gagaresu nema matuƙar da kuɗi ake sakawa a nemi abun.

Abokan Safwan sun shirya dinner wadda za'a yi a wani katafaren hall, sai dai shi ango ya ce sam shi kam ba wata dinner da zai je, shagugulan da aka yi ma sun wadatar ALLAH ya sawa aure albarka, ba magiyar da Zee ba ta yi masa ba akan ya yi haƙuri su je ko da rage lokacin da aka ɗiba ne za'a yi sai ayi komi cikin lokuta ƙalilan, amman ya buga kanshi a ƙasa ya ce shi bai san da wannan zance ba, cike da jin haushi Zee ta fashe masa da kuka dole ya koma aikin lallashinta, ganin yanda ta dami kanta akan son zuwan ne ya shirya suka je, amman har cikin zuciyarshi ba ya wani murna da duk wani shagali, aure dai ne anyi to tsirfin na mi ne kuma?.

Har aka yi dinner aka watse Safwan fuskarshi ba yabo ba fallasa sai dariyar yaƙe da yake yi wa mutane, Amarya da ango sun fito sun yi rawa sun sha liƙi ta ko'ina kuɗi ne ake zuba masu, bayan sun ƙare ne suka yanka cake tare da ciyar da junansu mutane sai ɗaukarsu photuna da videos ake yi, saboda shagalin ya ƙayatar da rai sosai ba tare da jan lokaci ba aka watse koma ya kama gabanshi, inda Ango ya ɗauko Amaryarshi zuwa gida tare da rakiyar abokai da ƙawayen Zee ɗin da za su kwana da safe su kama gabansu.

Kasancewar part ɗinshi daban shiyasa kai tsaye ya nufi sashenshi ya barta tare da zugar ƙawayenta suka nufi sashenta, cike da tsananin gajiya ya faɗa kan gadonshi tare da dafe kanshi idonshi a sama yana kallon seilling yana hasko Dijen Baffah cikin idanuwanshi, musamman lokacin da ya sami sa'ar rabata da abunda har lokacin idan ya tuna sai ya ji shi cikin wani yanayin buƙatuwa da son komawa cikin tafkinta mai ɓulɓulo da ruwan kogin ni'ima, waɗanda ko a misali ba zai taɓa kwatanta irin abunda ya ji a jikinta ba, don duk abunda zai faɗa ganin yake yi kamar ya fi hakan, saboda shi kanshi ya yi matuƙar mamakin yarinya kamarta ace itace da wannan tarin albarkatun ni'imar a jikinta, sai dai idan ya yi nazarin cewa ance ko wace mace da kalar ni'imarta sai ya ajiye mamakin don yasan ALLAHn da ya raba ya baiwa kowa ce mace haka itama ya raba ya bata tata, don ikon ALLAH ya fi gaban a yi mamakinshi illah kawai mu ce Alhmdllh a kowane hali a kuma kowane yanayi.

ZEE kam kasancewar abokan nata su ma kansu a fashe yake, shiyasa suka sakata ta sheƙo wanka tare da tsara mata dress cikin wata arniyar night gown fara ta yi kyau iya kyau sai dai komi na jikinta babu wanda ya ɓuya don har pant ɗin da ke jikinta ana hangowa, bra ma cewa suka yi kada ta saka kasancewarta daman cen breasts ɗin nata ba wani yawa ne da su ba, don bafulatana ce ta usuli mai ƙananan nonuwa, amman a hakan ma ba laifi sun ɗan fito a cikin rigar kuma shigar ta karɓe ta sosai, sannan suka fesheta da tsadaddun turaruka masu ɗan karen ƙamshi, suka zaunar da ita suna yi mata bitar abubuwan da ta yi, tana daɗe tana zaman jiran shigowar angon domin ya tafi da ita, sai dai shiru shirun da suka ji ya yi yawa ne suka bata shawarar kawai ta je ta sameshi da kanta, cikin zumuɗi ta miƙe don daman cen kawaici ne kawai take yi saboda kar aga zalamarta, aikuwa ta zumbula dogon hijabi wata ƙawarta ta rakata har sashenshi sannan ta dawo, Zee ta daɗe a ƙofar tana wassafa irin kallon da zata yi masa wanda zai sa ta sace zuciyarshi a lokaci ɗaya ya faɗa tarkonta.

Da guntuwar sallama ta shiga inda sallamar ta katse ba shiri saboda ganinshi da ta yi kwance takalman da ke ƙafarshi ma bai samu cirewa ba, suna nan sanye a ƙafar ta shi har lokacin, hular kanshi kawai ya cire saboda damuwar rashin sanin takamaiman inda Dijen take, damuwar hakan ne ta cika masa ziciya, Zee ta tako a hankali cikin faɗuwar gaba ta zauna gefen gadon tare da ɗora hannunta akan jikinshi ta ce

"My Man wai meke damunka ne? Na fahimci akwai damuwa a tattare da kai musamman yau ɗin nan, me yasa zaka taryi wannan daren na mu mai tarihi a garemu da wannan sabon yanayin??"

Safwan ya yi saurin riƙo hannunta daga kwancen tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya ce

"Sorry ni ma ban san me ke damuna ba, haka kawai na tsinci kaina cikin wannan yanayin, ki yi haƙuri kinji?"

Zee ta sauko ƙasa ta fara cire masa takalmin da Safar duka sannan ta haɗasu ta kai muhallinsu ta ajiye, ta dawo ta kwanta gefenshi ta shafo fuskarshi tana yi masa wani kallo ta ce

"Plss Honeybee ka daina wannan damuwar ka tattara sabon yanayin nan ka a jiyeshi a gefe ka kalli sabuwar Amaryarka gata a kusa da kai tana buƙatar kulawarka"

Safwan ya saka hannunshi ya janyota kusa da shi sosai ido cikin ido suke kallon juna, yana yi mata wani kallon tausayi saboda yasan ba ƙaramin so take yi masa ba, cikin mairairece fuska da alamun son yin kuka ta ce

"Plsss! my man!"

Safwan ya janyota jikinshi all kasancewar ba wani kumari ne da ita ba ya sakar mata kiss a goshi sannan ya miƙe zaune ya ce

"Bari in je in yi wanka ko da zan ɗan ji ƙarfin jikina, sannan mu zo mu yi sallahr godiyar ALLAH ga Ubangijinmu"

Cike da jin daɗin maganarshi ta lumshe ido daga kwancen ba tare da ta ce ƙanzil ba, ya miƙe yana cire kayanshi ta bishi da kallon ƙauna har ya shige toilet sannan ta sauke ajiyar zuciya a ranta ta ce

_"ALLAH ka bani ƴa ko ɗa mai kama da kai sak! my Bunny"_

Har ya fito bata san ya fito ba saboda ta lula sosai wajen tunanin zazzafar soyayyar da take yi masa, sai da ya saka ƙafa ya soso sililin ƙafarta sannan ta yi saurin ta shi zaune tana murmushi, ya ce ta je ta yi arwallah ta zo su yi sallar, ta miƙe tsaye ta yi wata miƙa ta cire hijabin da ke jikinta ta nufi toilet ɗin cikin wani takun jan hankali, ya bi bayanta da kallo ya yi wani gajeren murmushi sannan ya saka doguwar jallabiya fara ya shimfiɗa ƙatuwar carpet yana jiran fitowarta.

Bayan sun ƙare sallahr ne ya yi ta jera masu addu'o'in neman zaman lafiya sannan ya fara latsa amaryarshi tun a nan, don ko kazar amarcin da ake ci su ba su sami damar ci ba, saboda angon ba wani sukunin zuciya ne da shi ba shiyasa komi ma ya fita a ranshi, ita kuma murnar ganin yanda ya fara nuna mata zallar ƙaunarshi ne yasa ta ƙi cin komi, a hakan suka baje suna ta farantawa junansu ta hanyar musayar abubuwa da yawa, saɓanin Dije da shi ya yi kiɗan kuma ya yi rawar har ma ya sami guzurin kukan da ta rufeshi da shi wanda ya zama tamkar taki wajen haukace mata, Zee kam jiki ta saki itama ta nuna masa ba fa shi kaɗai ya iya tarairayar ba, cikin salon ƙaunar da ta baibayeshi da ita ne ta ci galabar samunshi yanda take buƙata, don kuwa ya baje sosai ya karɓi budurcin Amaryarshi, ba tare da ya sha wata wahala ba, duk ko da yanda take jin azaba amman hakan bai sa ta nuna masa gajiyarta ba, sai dai sunan Khadija da bakinshi ya ƙi daina ambata ya sa ta shiga tunanin wace khadija ce yake faɗa a yayin kwanciyar aurensu na farko?, amman ta bar abun aranta don bata son ta ɓata masa rai cikin wannan yanayin da suke ciki, sai da ya tabbatar da ya jigatar da ita sannan ya saurara mata don kanshi, ya koma saka mata albarka tare da jinjina mata akan budurcinta da ta adana masa.

Haka suka kwana cikin damuwa dukansu kowa da tunanin da yake yi cikin zuciyarshi, inda shi ya kwana yana tunanin ƙira da cikar ƙirjin Dijen Baffah, yayin da ita kuma ta kwana tana tambayar kanta wacece khadijar da ya yi ta kira lokacin da suke faranta junansu?.

Bayan sun yi SALLAHr asuba ne Zee ta kasa haƙuri ta ce da shi

"My man Ina son inyi maka wata tambaya da fatar baza ka ga laifina ba?"

Ya shafo fuskarta tare da riƙo hannunta ya sakar mata kiss a bayan hannun sannan ya ce

"Idan har kin san tambayar ba mai laifin ba ce ki yi kawai a shirye nike da in baki amsarta"

Zee ta yi saurin riƙo hannunshi ta saka nata sama da ƙasa ta riƙe gam gam wasu hawaye suka fara zarya cikin idonta ta ce
Chapter 62 · 0% Book details