← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 84

Sashe 79

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dije ta kara wayar a kunne tana share hawayenta ta ce

"Ba wani abu fa kaina ne yake ciyo"

Daga cen ɓangaren ya sauke ajiyar zuciya yace, "haba haba My luv to meyasa ba zaki sanar da ni ba kike wahalar man da kanki da Babyna? Yanzu ki shirya Aunty Ummi zata zo ta kaiki Asibiti sannu kin ji? ALLAH ya baki lafiya"

Ta ce "Ameen" cen cikin maƙoshi sannan ya sake cewa "ya kwananki da na Babyna?"

Ta ce "ƙalau"

Cike da mamakin yanda take ta ba shi amsa a taƙaice ya ce "Babyluv ko na yi maki wani abun ne ban sani ba?"

Ta ce "A'a" yace 'to wacece kike cewa da ni in gayar?"

Ta murguɗa baki kamar yana gabanta ta ce "wadda ka je wajenta ko ba'a buƙatar gaisuwar tawa ne?"

Ba shiri ya rufe bakinshi saboda fahimtar inda ta dosa, cikin dariyar da ta so kufce masa ne ya ce

"Ana buƙata kuma an karɓa hannu bibbiyu ALLAH ya saka da aljannah, amman fushin na minene? ko kin manta Umurninki na bi? To yanzu kuma tunda an yi maki abunda kike buƙata kuma ta dawo kamar yanda kika roƙar mata alfarma Ni kuma mi ye laifina a ciki?"

Ta ce "ba ko ɗaya hasali ma ka yi abunda ya dace" zai sake yin magana ne Zee ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da nufin sanar da shi komi ya yi ready, ganin yana waya ya sa ta yi saurin juyawa da nufin komawa, ya yi gyaran murya ta waigo ya yafitota ta ƙaraso wurinshi, ya miƙa mata wayar cikin jarumta ya ce "kHadija ce ku gaisa"

ZEE ta karɓi wayar cikin sanyin jiki tana shirin yin magana ta ji Dijen tana faɗin

"Dawo da itan ai abu ne wanda ya dace, kuma kai kanka zaka gano alfanun yafiya ga wanda ya yi maka laifi, saboda ladarka tana wurin Allah Kuma insha ALLAHu za ka ga sakamakon abun alkhairin da ka yi, fatana kawai ALLAH ya baka ikon yi muna adalci, kada don an sami ta ƙarfen a juyawa ƴar ƙauye baya"

Zee ta yi saurin faɗin

"Insha ALLAHu in dai ta ɓangarena ne matsala ta ƙare, da ni da ke yanzu mun zama abu ɗaya babu wani gorin asali ko wani fifiko, a zahirance ma kin sha gabana don kin riga da kin yi man fintinkau tunda har kike da zuciyar imani, kika ɗora Mijinki akan hanyar dawo da ni cikinku duk da abunda na aikata maku a baya, don ALLAH ki yafe mani kinji insha ALLAHu zan yi ko yi da kyakkyawar zuciya irin taki, saboda yanzu na gano cewa ko wane mutum da kalar baiwar da Allah ya yi masa, sau da yawa wanda ka ke renawa sai ya zo ya fi ka ta hanyoyin da kai ko da kuɗi ba zaka iya binsu ba, matuƙar sheɗan yana buga ganganunshi saman kanka, na gode sosai da taimakon da kika yi mani aka dawo da ni, kuma ki sa a ranki cewa kina da ƴar'uwa saboda yanzu Zee ta ɗaukeki tamkar ƴar'uwarta ta ciki ɗaya tunda har na gano ke ɗin alkhairi ce garemu ni da shi"

Tana ƙare faɗar maganar ta miƙa masa wayar ta fice da sauri tana kuka, ya bita da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya yace

"Babyluv sannu da namijin ƙoƙarinki, lalle ke alkhairi ce ga rayuwata, ina ta ya ƴaƴana farin cikin samun uwa ta gari irinki, fatana kawai a yanzu ALLAH ya sauke man ke lafiya ki bani Babyna a hannu in ɗauka"

Dije ta goge ƙwallarta ta saita natsuwarta ta ce "Insha ALLAHu ƴaƴa har sai ka ce in tsaya haka nan in huta , don in na Fara watso maku su sai ka rasa da hannun da zaka riƙe sauran"

Safwan ya fashe da dariya cikin dariyar ya ce "au watsosu ma zaki yi don salon mugunta?, To bari ki ji ko da jefosu zaki yi ta yi duk bayan minti biyar Habibynki ba zai taɓa rasa hannun da zai karɓesu ba, ke dai kawai ki natsu ki sako man su sannu a hankali ina karɓewa cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba ko ƙosawa"

Haka suka yi ta firarsu mai cike da barkwanci da raha har dukansu suka daina jin damuwar rashin ganin juna, sannan Dije ta daƙile firar dolenta don bata son ta shiga haƙƙin Zee, ba don ya so ba suka yi sallama cikin kewar juna tare da kwaɗayin ganin junansu, saboda mugun sabon da suka yi wa juna da kawunansu.

Har ga ALLAH Safwan ya ji daɗin yanda Zee ta dawo macen kirki, shiyasa cikin dauriya da kai zuciya nesa ya mu'amalanceta har lokacin barin garin ya yi ya tattara kayanshi ya koma Abuja, wurin Matarshi da ya ke jin a duniya kaf ba ya da matar da zata kamo ƙafarta ma bale ta kamota, ko da ko akwai ɗiyan lu'ulu'u da murjani a cikin.

****

Haka rayuwa ta yi ta shurawa sannu a hankali har cikin Surayya ya isa haifuwa ta haifo ƴarta mace masha ALLAH da ita.

Cikin zumuɗi Dijen ta yi ta murnar zuwa Yolar sai dai idan ta tuna da zata ga Zee sai jikinta ya yi sanyi, dole dai haka ta daure ta matsa masa ya barta ta biyo su Aunty Ummi suka nufo Yola, saboda a lokacin shi ana tsaka da aiki don during working hours ne, cike da jin daɗin yarinyar Dije ta fara santi tamkar ta sace yarinyar take ji saboda sonta da take yi, Hajiya Mama da su Surayya sai dariya suke yi mata ganin yanda ta maƙake yarinyar bata son kowa ya ɗauketa, don har goyeta take yi sai Hajiya ta yi faɗa take sauketa, Zee ma kullum tana zuwa da ita ake komi shiyasa Dijen ta rage kishinta da take ji aranta, saboda ganin yanda ta ke ta haba haba da ita tamkar cewa babu abunda ya taɓa shiga a tsakaninsu, haka ma da yanda take ta janta a jiki tana nuna mata cewa ai an zama ɗaya babu zancen wata kishiya shiyasa itama ta ajiye komi suka fara ɗasawa, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Hajiya Mama ba, ta ƙara godewa ALLAH da har ta jajirce Safwan ya dawo da aurenta, don tasan dole ne sai ya nemi wani auren tunda har ya saba da mace biyun, kuma da wacce ba'a san halinta ba gwara wadda daman cen an san halinta sai a ci maganin matsalar.

Aka yi taron suna lafiya cike da ƙayatarwa yarinya ta ci sunan uwar Mijin Surry ana yi mata laƙabi da ilham, bayan suna Safwan ɗin ya zo ya yi kwana biyu sannan ya kwashi Matarshi suka koma Abuja. kawosu ita da

Sannu a hankali itama Dijen cikinta yana ta miƙawa har ya kai watannin haifuwa, Hajiya Mama ta matsa masa akan dole ya dawo da ita wurinta ta haifu, amman ya nuna shi dai ya fi son idan ta haifu sai su dawo yolar, saboda cen ɗin tana samun kulawar manyan likitoci a Asibitin da take awo, sai da Hajiya Mama ta yi masa jan ido sannan ya kwasota da himilin uwar siyayarta da ta jaririn da za'a haifo masa, don daman cen shi rabuwa da ita ne ba ya so saboda ko da take da titsetsen cikinta idan jarabarshi ta motsa tasan ta yanda zata faranta masa har ta gamsar da Habibynta.

Shi yasa ko da suka zo Yolar ya kasa ya tsare gidan Hajiya Mamar ya ƙi barin garin har sai da korashi saboda yanda ake ta nemanshi a ma'aikatar ta su, saboda muhimmancin da yake da shi dole ne wani abun sai da shi.

Satinta ɗaya a Yola ta fara jin sign na naƙuda, Hajiya Mama tana bata kula sosai da sosai don itama ɗin har nurse's ta samo mata masu duba mata ita har gida ba sai anje Asibiti ba, Zee kanta kullum tana gidan ana renon cikin da dakon zuwan haifuwar, sai ko ga shi cikin ikon ALLAH wata ranar juma'a Asubar farin ta fara naƙuda, jikin Hajiya Mama yana rawa ta saka direba ya kwasheta da kayan da duk za'a buƙata suka nufi wata babbar Asibin da ke garin yolar, cikin nasara kwata kwata bata yi minti goma da shigarta labour room ba ta haifo santalelen yaronta Mai kama da Ubanshi sak, fari jajir har wani yalo yalo yake yi saboda tsabar farinshi, ga shi ƙatoto da shi masha ALLAH tamkar ba haifuwar Dijen Baffah ba.

Farin ciki wajensu Hajiya Mama da fiddo da ma Zee ɗin abun ba'a magana, saboda har rige rigen ɗauka ake yi tsakaninsu su biyu, Surayya ma rufe ido ta yi tace tunda da ita yaron yake kama itace zata riƙeshi, Hajiya Mama dai sai dariya take yi masu idonta akan ɗakin da Dijen take tana ta baccin sauke gajiyar naƙudar da ta sha.

Ango ƙarni kam daman yana kan hanyar zuwa Yolar sai ga kiran Fiddo ya shigo wayarshi cikin kuwwa da ihun murna take sanar da shi an samu Baby boy, ba shiri shi ma ya buga wata ƙatuwar kabbara ya ce

"ALLAHU Akbar? Alhmdllh! Shikenan na zama Baba, Little sis kina da tukuici mai tsoka a wurina, to ya ita Mamar boy ɗin lafiyarta ƙalau dai ko?"

Cikin murnar albishir ɗin da ya yi mata na tukuici ta ce "fine take big bros bacci ma ta ke yi yanzu haka"

Baki a washe ya ce

"Ok Ina Kan hanya daman ganin na kusa ƙarasowa garin ki shafa man kan babyna"

Cike da jin daɗi fiddo ta koma ɗakin tana dariya ta ce "Wayyo daɗi Ni ce na yiwa yayanmu albishir ya ce in tsumayi tukuicina"

Surayya da ke ta faman murnar ta sameshi a wayar da nufin ta riga kowa sanar da shi ba shiri ta kashe wayar tana harararta ta ce

"Ai WALLAHI kin ƙware da mugunta yanzu don salon yaudara shine kika fice waje kika rigani to ai dole mu raba koma minene"

Zee sai dariya take masu Hajiya Mama ta kira cen garinsu Dijen ta sanarwa da su Baffah, sannan ta dinga kiran mutane yan'uwa da abokan arziƙi tana ta sanarwar haifuwar, kafin ka ce me Asibitin ta cika da yan taya murna kowa baki har kunne.
Chapter 79 · 0% Book details