← Book details Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 84

Sashe 78

Dije Ƙarangiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zee ta share hawayenta ta ce "Ai Ni tuni na gano cewa zafin nema baya kawo samu, don da banda ke da yanzu Ni kaina bana duniyar an riga da an kasheni, wanda ta sanadin haka ina da tabbacin Daddyna ma zai mutu itama kanta Mummy zata shiga muwuyacin hali, saboda gorin mutane ƙarshe itama ta bimu, Nagode sosai Ƙawata lalle ke ƙawar amana ce ALLAH ya bar zumunci kuma ya baki miji nagari ke ma ki je ki yi aurenki ki huta"

Ruma ta ce "Ameen"

Tare suka je suka samarwa Baabaah Asaben abunda ke faruwa cike da jin daɗi ta nufi gidamsu Zee ta sanarwa Mahaifin Zee saboda murna sai gashi da tashi zaune ba shiri zuciyarshi cike da jin daɗin jin wannan abun farin ciki, Mahaifiyarta ma ba ƙaramin daɗi ta ji ba da jin maganar, shiyasa ta nemi alfarmar ganinta ba ɓata lokaci Baabaah Asaben ta kira wani yaronta ta ce ya ɗauko Zee ya kawota.

Satinta ɗaya gidansu Mahaifiyarta tana nusar da ita tare da nasihohi kala kala da misalan abubuwa da yawa wadañda suka faru a duniya masu daɗi da akasinsu, sannan aka fara gyarata na tsawon kwana uku sannan Mahaifinta ya yi mata huɗuba sosai da kanshi ya ɗauketa ya kaita gidansu Safwan wurin Hajiya Mama ya bada haƙuri sosai sannan ya ɗauketa ya kaita gidan Safwan da hannunshi tare da yi masu addu'ar zaman lafiya.

Satinta biyu a gidanshi ba tare da ya waiwayota ba, har sai da Hajiya Mama ta nuna masa rashin kyautawarshi sannan ya baro Abuja ya nufo Yola ranshi ba daɗi, don in ta shi ake bi abarshi da Dijenshi ta isheshi rayuwa a duniya.

Ko da ya shigo garin sai da ya je wajen Hajiyarshi suka gaisa ya bata tsarabarsu sannan ya ɗan taɓa fira da fiddo da Surayya da aka dawo da ita haifuwa saboda Mijinta da baya nan, bayan sun gama tambayar juna bayan rabuwa ne ya miƙe zai tafi Hajiyarmu ta ce

"Ka kula da matarka don na hango shiriya a idanuwanta, kuma ka yi haƙuri da ni don nasan ba da son ranka ba biyayya ce kawai kake yi man, to ka sani duk lokacin da wani ya sami shiriya ta sanadinka ba ƙaramar lada zaka samu a wurin Ubangiji ba, shiyasa duk da nasan ta aikata mummunan laifi amman hakan bai sa na barka ka yi abunda ka so ba, don ina jin tsoron ka sake auro wadda zata aikata abinda yafi wanda ya yi muni, don gara ita da kishinta yake a fili yake kowa zai gani, saɓanin wasu da suke ɓoyewa a fili su nuna ba komi kuma su bi ta ƙarƙashin ƙasa su wargazaka daga kai har matar taka, to ko a hakan ma ka godewa ALLAH da baiwar da ya yi maka tunda bai haɗaka da mace mashurika ba mai biyar bokaye, wadda ba matarka ba har Ni da na haifeka da ƴan'uwanka duka zata iya rabaka gaba ɗaya"

Cikin sanyin jiki ya ce

"Na gode Hajiyarmu ai nasan daman ke baki ɗora wani ma a hanyar da bata dace ba bale ɗanki da kika haifa, Ubangiji ya ƙara bar muna ke ya karo lafiya da nisan kwana Hajiyarmu, na gode sosai kinga na manta da tsarabar da ɗiyarki ta bada in kawo maki"

Ya kalli fiddo ya ce "ke zo mu je ki karɓo na tafi Hajiyarmu sai na dawo"

Fiddo ta biyoshi zuciyarta cike shakkun abinda zata faɗa cen dai ta danne ta ce "big bros yaushe zaka je da Ni Abuja wurin Khadija?"

Ya waigo Yana yi mata wani kallo ya ce "Ba ma maraba da gulma idan har itace zata kaiki don nasan Zee ce taki don haka ki tattara kayanki ki je ki tayata zama idan na koma, ko ko karatu na ki ya zaki yi da shi idan kin je cen?"

Ranta a ɓace ta ce "Ni dai yayanmu cen nike son zuwa don ALLAH ka je da Ni in zaka koma yanzu, sai ka sakani makarantar a cen don nafi son inyi karatuna a cen"

Ya miƙo mata ledar saƙon da Dijen ta aikowa Hajiyar yana faɗin "lalle baki da hankali kina year 2 ki nemi barin makaranta saboda daɗin da ya yi maki yawa ko? To ki jira idan kin fara aiki sai ki koma cen da karatun kina biyawa kanki, Ni matsa ki bani gu tun ban hanɓarar da ke ba"

Fiddo ta yi cikin gidan tana gunguni don ita zaman garin ne ya gundureta, saboda in suna chatt da Husnah tana turo mata pictures ɗinsu in suna shaguna ko wuraren shaƙatawar da suke yawan zuwa, abun yana burgeta sosai shiyasa tasawa ranta itama zata koma cen a fantama da ita, amman dai ga shi ya gwasaleta a tashin farko.

Ya fisgi Motarshi ya nufi gidanshi, haka kawai yake jin baya son shiga gidan don ya daɗe zaune a parking space yana firarshi da ma'aikatan gidan, don ko jakarshi tuni aka shige da ita ciki sannan ya fito ya nufi sashen Zee ɗin zuciyarshi a cunkushe, sai dai yanayin da ga Zee ɗin yasa ya yi saurin sakin fuskarshi saboda ba ƙaramin bugawa zuciyarshi ta yi ba, ganin yanda ta yi baƙi ta rame sosai amman a hakan har da fara'a kwance a fuskarta da ta rame sosai tana yi masa sannu da zuwa.

Ya zauna tare da bin falon da kallo kamar mai neman wani abu sannan ya dawo da kallonshi gareta ya ce

"Ke fa? me ya sameki kika rame irin haka??"

Ta duƙe hawaye suna zuba ta fara wasa da yan yatsunta, cike da tausayinta ya ce

"Zo zo inji me ke faruwa ne?"

Zee ta durƙushe ƙasa tare da riƙo ƙafafuwanshi tana wani irin kuka take faɗin

"Plss ka yafe mani don ALLAH nasan ban yiwa kaina adalci ba, don ALLAH ka ce ka yafe mani ko da zuciyata zata yi sanyi"

Safwan ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujerar da yake yana share mata hawayen ya ce "komi ya wuce ki daina wannan kukan yanzu ba gamu tare ba?"

Zee ta sake fashewa da kuka tana faɗin "na cutar da kaina da hannuna don ALLAH ka yi haƙuri"

Dole Safwan ya ajiye komi ya fara lallashinta, sannan ta kaishi ya yi wanka ta rakoshi diny inda ta shirya masa abinci mai kyau, yana ci yana janta da fira saboda ganin har lokacin bata daina hawaye ba.

Cikin dauriya ya bata kulawa ba yabo ba fallasa haka suka kwana kowa da tunanin da ke cike cikin zuciyoyinsu, ita tana ganin kamar yana riƙe da ita shi kuma yana tunanin irin lalacewar da ta yi.

To mu dai sai dai muyi maku fatar ALLAH ya bada zaman lafiya da hkr😝

Akafta😊

D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*

*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Aski ya zo gaban gashi Mutanena💃🏻*

*Lamba 70 *

Haka dai suka kwana ba natsuwar zuciyoyi, bayan SALLAHr Asuba Safwan ko da ya dawo masallaci ya taradda Zee tana ta karatun Qur'ani, abun ya buregeshi kuma haka ya ba shi mamaki sosai, saboda sanin da ya yi mata ada da ƙyar ma take tashi yin SALLAHr a lokacin, sannan idan ma ya matsa mata ta yi tana kammalawa take yin kwanciyarta ko addu'ar kirki bata tsayawa yi, amman yanzu ita ce har da su karatun Qur'ani, cike da jin daɗin sauyin da aka samu ne ya zauna kan gadon yana ƙarasa addu'o'inshi na azkar, har bacci ya fara janshi ya kwanta ba shiri saboda baccin da ya fiegeshi ba tare da ya shiryawa hakan ba.

Misalin ƙarfe takwas ya falka saboda ƙamshij abun break ɗin da take haɗa masu, mamaki ya sake kamashi ya fito ɗakin ya nufi kitchen yana kallon yanda take ta hadadarta, cikin shigar wata doguwar riga ƴar kanti, tana ganinshi ta diririce tana gayar da shi cikin ladabi, bayan ya amsa ne zuciyarshi cike da jin daɗin sauyin da ta samu, ya fice kitchen ɗin zuwa sashenshi saboda zuciyarshi da ke ta kwaɗayin son jin muryar Uwargidanshi, don tun yana kan hanyar shigowa garin da suka yi waya ta ji ya sauka lafiya ta kashe wayarta, saboda kishin da ke cin zuciyarta game da zuwanshi wurin Zee, da abun ya kwana a ranshi saboda ya yi ta kiran wayoyinta a kashe ta Husnah ma a kashe, cikin takaici ya kira Aunty Ummi ya ce ta haɗashi da ɗaya daga cikinsu yana son yin magana da Dijenshi, Aunty Ummi ta nuna masa dare ya yi sosai ya dai haƙura sai da safe, saboda a lokacin ƙarfe sha biyu da mintuna dole ba don ya so ba ya haƙura amman zuciyarshi cike fal da son jin dalilin da Dijen ta aikata hakan.

Shiyasa ko da ya shiga sashenshi ko wanka bai yi ba ya fara nemanta a waya, aka yi da ce ta shiga itama caraf ta ɗaga sai dai shirun da ya ji ta yi masa ne yasa shi saurin faɗin

"Me na yi maki kika horani da rashin jin muryarki?"

Sheshshekar kukan da ya ji ne a kunnenshi yasa ya yi saurin sake wata maganar a rikice ya ce

"Subhanllah me ke faruwa ne? Me aka yi maki? Wa ya taɓa man ke don ya ga bana nan?"

Dije ta sake fashewa da kukan gaba ɗaya cike da ruɗewa ya ce

"Plss babyluv don ALLAH ki daina kukan nan ki sanar da ni abunda ya faru idan har kina son ganin natsuwata"

Cikin kukan Dije ta ce

"Ka gaisheta"

Tana ƙare faɗar hakan ta datse kiran, cikin wani sabon tashin hankali ya sake bi da wani kiran amman har ta tsinke bata ɗauka ba, ganin hakan ya sa ya dinga kiran Husnah kira bayan kira, tana bacci dole ta miƙe ta ɗauka ya ce da ita ta kaiwa Dijen, ta miƙe cike da jin haushin katse mata bacci da aka yi, sai dai kukan da ta tarar tana yi ne yasa jikinta ya yi sanyi, ta miƙa mata wayar ta fito zuciyarta cike da jin zafin kukan da ta ga Auntynta tana yi, don tun jiya take lallashinta akan ta yi haƙuri ta daina kukan da ta ke yi na rashin Auncle ɗinsu, ta yi kamar ta haƙura ashe bata haƙura da kukan ba.
Chapter 78 · 0% Book details